Sinadaran Da Ke Cikin Ruwa

Cikin kashi na hudu, mun dubi dabi’u da sinadaran dake cikin ruwa ne. A sha karatu lafiya.

377

Matashiya

Cikin kasida mai take: “Yadda Ruwa ke Samuwa da Nau’ukan Sinadaran dake CIkinsa,” mai karatu ya karanta bayanai kan yadda ruwa ke samu, da yadda ruwan sama ke samuwa, da yadda tsarin maimaituwansa yake, wato “Water Circle,” da kuma bayani kan mizanin ruwa a duniya, da wasu duniyoyin da ake tsammanin suna da ruwa a cikinsu.  Wadannan bayanai sun zo ne cikin shekarar 2011.  Abin da ya rage mai karatu ke binmu bashi shi ne bangaren bayanin da ya shafi sinadarai ko siffofi ko dabi’un ruwa.  Wanann, a kimiyyance, shi ake kira “The Properties of Water.” Ko kace: “The Chemical and Physical Properties of Water.”  Abin da ya dawo damu kan wannan maudu’i kenan a wannan mako.

Mai karatu yaji cewa a duniya babu wani sinadari na kimiyya irin ruwa.  Bayan ni’imar aiko Annabawa da Manzanni da Allah yayi wa duniya, babu wani ni’ima da Allah ya kara baiwa bayinsa (Aljanu da Mutane da Dabbobi da Tsirrai) irin ni’imar ruwa.  Wannan zance kuwa ba wai Malaman musulunci ne kadai suka tabbatar dashi ba, hatta wadanda basu da alaka da addini ma sun yarda cewa ruwa ya sha bamban da duk wani abin da dan adam ke mu’amala dashi a sararin wannan duniya tamu, wajen tasarrafi.  In kuwa haka ne, bayan duk abin da muka sani a al’adance na siffofi ko matsayin ruwa a gare mu, me ya kara tabbatar masa da wannan matsayi hatta a wajen Malaman kimiyya?  Kafin sanin wadannan abubuwa, ya kamata mu san wai shin, shi ruwa wasu sinadarai ne ke haduwa don samar dashi?


Ruwa, Waye Kai?

Malaman fannin kimiyya musamman masu bincike kan sinadaran da Allah ya hore mana su a sararin wannan duniya, bayan sun gama gwaje-gwajensu, sun tabbatar da cewa ruwa na samuwa ne ta sanadiyyar kawancen wasu sinadarai ko madda na kimiyya guda biyu; da maddar Hidirojin (Hydrogen) guda biyu, da kuma maddar Oksijin (Oxygen) guda daya.  A kimiyyance, ga yadda ake rubuta shi: H2O (Bangaren farko mai dauke da “H2” na nufin maddar Hidirojin guda biyu ne.  Bangaren “O” kuma na ishara ne ga maddar Oksijin, guda daya).  Wadannan maddoji ne guda biyu ke haduwa don samar da sinadarin ruwa kamar yadda muke ganinsa.  A hade suke, kamar yadda mai karatu ke gani a hoton dake shafin nan, shi yasa a kimiyyance ake kiran wannan gungu da suna: “Water Molecle.”  Duk wani sinadarin kimiyya mai iya mannewa a jikin dan uwansa, ana kiransa: “Molecle” ne.

Malaman kimiyya sun tabbatar da cewa, ruwa ne kadai sinadarin dake samuwa a yanayi ko dabi’ar yanayi (Form) iri uku.  Shi kadai ake iya samunsa a yanayi narkakke (Liquid Form), ko yanayi sandararre, a matsayin kankara (Solid Form), kuma a yanayin iska (Gaseous Form), a sararin wannan duniya tamu.  A wannan duniya tamu akwai ruwa a cikin iska (Water Vapour), akwai shi a cikin giragizai, akwai shi a cikin teku, akwai shi a yanayin kankarar kan tsauni (Glacier), akwai shi a yanayin kankarar teku (Iceberg), akwai shi cikin dandanon gishiri (Salt Water) a tekuna, akwai shi cikin dandanon gardi a rafuka, da koguna da kuma karkashin kasa.  Wannan yanayin dabi’ar samuwa da siffa, ruwa ne kadai ya kebanta da shi/su.

Har wa yau, ruwa ne kadai daga cikin sinadarai, ke iya gudanuwa a duk inda aka kai shi ko aka ajiye shi, kuma shi ne kadai sinadarai kowane irin abu na da bukatuwa gare shi;  bukatuwa na kusa ko na nesa.  Babban misali shi ne jikin dan adam.  Ruwa a jikin dan adam yana daidaita yanayin jiki; idan zafi ne, ruwan sanyi zai daidaita shi.  Idan sanyi ne ruwan zafi zai daidaita shi.  Sannan ruwa a jikin dan adam na inganta masa mahadar kasusuwan jikinsa, wato “Joints,” su zama masu santsi, mai laudi, kada su bushe suyi kaushi.  Ruwa a bakin dan adam na jike dukkan tantanin dake mahallin ne; daga tantanin idanu (Eye Tissues), da tantanin baki (Mouth Tissues), zuwa tantanin hancinsa (Nose Tissues), duk ruwa na jike su, ya danyantar dasu don kada a samu matsala.  Ruwa ne ke raya dukkan bangarorin jiki dake cikin dan adam; irin su zuciya, da hanta, da koda, da sauransu.  Ruwa ne ke rage wa koda da hanta aikinsu, ta hanyar wanke su fyas, da kwashe dukkan sharar da ka iya toshe musu hanyoyin dake cikinsu don hana su aiki yadda ya kamata.   Sannan, yawan shan ruwa ga wanda ke gudawa yana rage gudawar, idan har an kamu.  Idan ba a kamu da ita ba kuma yawan shan ruwa na hana kamuwa da ita.  Ruwa ne kuma ke daukan sinadaran gina jiki na abinci, da sinadaran iska, don isar dasu zuwa cikin kwayoyin halitta (Cells) dake jikin dan adam.  A karshe, yawan shan ruwa iya gwargwadon bukata kan narkar da sinadaran abinci da na abin sha (“Minerals” da “Nutrients”) zuwa sauran sassan jiki, don a samu gamewar fa’idarsu.  Ruwa sarkin aiki!

Dabi’u da Sinadarai

“Dabi’un ruwa” na nufin siffofinsa na bayyane ne.  A yayin da kalmar “Sinadaran ruwa” kuma ke ishara ga irin abubuwan da suke boye a cikinsa na maddojin kimiyya da idanun dan adam basu iya gani.  Allah Buwayi Gagara-misali!!!  Ga wasu daga cikin dabi’u da sinadaran dake dauke a cikin ruwa ko tattare da ruwa:

Narkarwa

- Adv -

Ruwa wani irin sinadari ne mai iya narkar da duk wani abin da aka jefa a cikinsa, ma’abocin narkewa; duk wahalarsa wajen narkewa kuwa.  A cikin dukkan sinadaran dake wannan sarari da muke rayuwa, ruwa ne kadai ke iya narkar da duk wata madda ta kimiyya idan ya hadu da ita.  Wannan dabi’a ce tasa masana kimiyyar sinadarai a duniya ke kiran ruwa da cewa: “The Universal Solvent.”  Idan aka jefa su gishiri, da sukari, da sinadarin tsami (acid), da iskar da muke shaka, a cikin ruwa, duk yana iya narkar dasu, ya hadiye su, su zama a cikinsa don a iya amfanuwa da abin da ke cikinsu.  Shi yasa ake kiran wadannan sinadarai da suna: “Hydropholic” ko “Water-loving”, wato masoya ruwa kenan.  Muddin suka shiga cikinsa, to sun zama shi.  Iya gwargwadon yawansu a cikinsa iya gwargwadon tasirinsu da kamantuwar da ruwan zai yi dasu.    A daya bangaren kuma, idan aka jefa masa mai daskararre ko narkakke – irin su man ja, da man gyada, da man shanu, da bakin mai, da fetur da dukkan dangoginsu  – ba ya iya hadiye su; ba sa iya sajewa dashi, ba sa iya narkewa a cikinsa.  Saboda su ba masu narkewa bane.  Kuma shi yasa ake kiransu da suna: “Hydrophobic” ko “Water-fearing”, saboda kasa narkewa da suke yi a cikinsa.  Wannan kudura ce mai karfin gaske da Allah ya baiwa ruwa.

Launi, da Dandano, da Kamshi

Bayan haka, a karankanshi yana iya narkewa ne kadai (idan a sandare yake) a yanayi madaidaici.  Ma’ana, idan ruwa yana yanayin kankara ne, idan aka kawo shi cikin yanayin mahalli (Temperature) madaidaici, nan take zai kama narkewa.  Kamar yadda idan a yanayi mai zafi yake dabi’arsa na iya canzawa.  Idan zafin wuta ne, zai kara narkewa kuma nauyinsa (Density) ya karu saboda tasirin zafi.  Idan kuma a narke yake sai aka jefa shi cikin yanayi mai dan karen sanyi, nan take zai sandare, nauyinsa ya ragu.  Ba zai koma hakikanin nauyi da mizaninsa ba sai sadda ya sake narkewa.  Sannan ba shi da wari, ko kamshi.  Kuma dandanonsa bai yi iri daya da kowane irin abu ba.  Amma a Hausance akan ce yana da gardi.  Amma a kimiyyance Malaman kimiyya kan ce: “Water is tasteless,” ma’ana, ba shi da dandano.  Wajen launi fa?  Launinsa launin gilashi ne ko karau, wato “Crystal” kenan a turance.  Idan yana dan kadan kenan.  Amma idan mai yawa ne, launinsa kan karkata kadan zuwa launin shudi ko sirkin shudi, wato “Hue Blue” kenan.  Idan kuma yana yanayin iska ne, to idanun dan adam ba ya ganinsa, sai dai aji danshinsa a inda yake.  Ruwa kenan!

Alaka da Infra-red

Daga cikin launukan dake sararin wannan duniya tamu akwai nau’in hasken Infra-red, wanda haske ne kasa da launin ja; ko kace kasa da ganin duk wani mai gani.  Irin wannan haske idan ya shiga ruwa ko ya haskaka cikin ruwa, narkewa yake yi nan take.  Ma’ana, hasken Infra-red ba ya bayyana a cikin ruwa.  Wannan ne ma yasa shuke-shuke da tsirrai dake cikin kogi, ko rafi, ko teku suke iya rayuwa.  Domin hasken rana na iya riskarsu nan take, duk zurfinsu a cikin teku.  Kuma idan bamu mance ba, su ciyayi da itatuwa da shuke-shuke, suna rayuwa ne ta hanyar makamashin hasken rana dake riskarsu a inda suke.

Makamashin Lantarki

Kamar yadda bayani ya gabata a sama, ruwa na dauke ne da sinadarai guda biyu da suka yi gungu don samar dashi; da maddar Hidirojin (Hydrogen) guda biyu, sai maddar Oksijin (Oxygen) guda daya.  Dukkansu a like suke da juna, kamar yadda yake a hoton dake shafin da mai karatu ke karatun wannan kasida.  Wadannan maddoji kowannensu na da kimarsa da nau’in karfinsa a kimiyyance.  Maddar Oksijin dai karfin mace take dauke dashi, wato “Negative Charge” (alamar – ), a ma’aunin karfin makamashin lantarki.  A daya bangaren kuma, maddar Hidirojin na dauke ne da karfin namiji, wato “Positive Charge” (alamar + ), a ma’unin makamashin lantarki.  Wannan nau’in na karfin lantarki dake cikin sinadaran ruwa ne ke sa duk wani abu mai holoko (kamar kwallo, ko balan-balan, ko wani abu rufaffe mai dauke da iska) ya rika yawo a saman ruwan, ba tare da ya nitse ba.  Wannan tasiri shi ne Malaman kimiyya ke kira “Capillary Force” ko “Capillary Action.”

Ruwa sinadari ne madaidaici.  Wannan na cikin manyan kudororin Allah madaukakin sarki.  Abin da wannan ke nufi shi ne, ya dace da yanayin dabi’ar mahallin duniya, domin ita kanta duniyar Allah ya halicce ta ne cikin yanayin madaidaici, kamar yadda mai karatu watakila ya taba karantawa a kasidar da na gabatar shekaru 4 da suka gabata mai take: “Makamashi da Dukkan Nau’ukansa.”  Wannan tsari na daidaito yana cikin ruwa.  Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, maddojin Hidirojin dake cikinsa, ita ce kadai maddar da ta dace da yanayinsa.  Malaman kimiyya suka ce da za a cire maddar Hidirojin a maye gurbinta da wasu maddoji irin su: Lithium, da Sodium, da Calcium, da Potassium, da Caesium, duk za su kore maddar Hidirojin.  Ba wannan kadai ba, nan take ruwan zai canza yanayi, daga ruwa zuwa yanayin maddar Hydroxide, wanda duk wani abu mai dauke da wuta yazo kusa dashi, nan take zai kama da wuta.  Ka ga ya tashi daga matsayinsa na ruwa ya koma wani makamashi mai dan karen hadari.

Alaka da Tubalin Halitta (Cells)

Jikin dan adam na dauke ne da miliyoyin kwayoyin halitta ko kace tubalin halitta, wato Cells kenan.  Su ne ke tafiyar da rayuwarsa, domin duk wani bangare na jikinsa; ciki da waje, yana dauke da wadannan kwayoyin halitta.  Su ne rayuwar ma dai gaba daya.  To, duk da wannan matsayi nasu, asalinsu ruwa ne.  yanayinsu ruwa ne.  A cikin ruwa suke rayuwa.  Idan babu ruwa, ba za su taba iya aiwatar da komai ba.  Samuwar ruwa a mahallinsu ne ke taimakawa wajen narkar dasu, da mayar dasu cikin yanayin da zasu gudanar da ayyukansu cikin sauki.  Rayuwar wadannan kwayoyin halitta kacokam ya dogara ga ruwa ne.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.