Tsaunuka Masu Aman Wuta (4)

A kashi na hudu kuma na karshe, munyi bayani ne akan tokar dake bulbule mahallin da tsaunin da ya kama da wuta yake. Ba wai garuruwa ko kauyukan dake wurin kadai ba, hatta sararin samaniya duk abin yana shafa.

169

“Tokar Kunun Dutse” (Ash Plume)

To bayan wannan sinadari kuma, sai abu na gaba da ke fitowa daga cikin wannan tsauni, wato “Tokar Kunun Dutse”, ko kuma Ash Plume, ko Volcanic Ash a Kimiyyance.  Wannan shi ma yana dauke ne da sidanarai masu cutarwa da amfani.  Wannan toka na dauke ne da buraguzan duwatsu da gilasai masu fadin kasa da milimita biyu, da ke samuwa a yayin da wani tsauni yayi amai.  Babban abin da ke haifar da wannan toka mai dauke da hayaki kuwa ita ce masifaffiyar iskar da ke cillo wancan damammen kunun dutse mai fitowa daga karkashin tsaunin.  Wannan iskar ce ke dauko wannan toka, ta cilla shi sama har cikin sararin samaniya.  Wannan tokar kunun dutse na dauke ne da launin ruwan kasa, wato Brownish Ash.  Abu na biyu da ke taimakawa wajen samar da wannan tokar kunun dutse shi ne sinadaran haske masu kyastuwa daga wutar da ke kamawa daidai lokacin da wancan kunun dutse ke fitowa daga kasan tsaunin.  Sai abu na uku, wato buraguzan laka da ke samuwa yayin da kunun dutsen ke arangama da makogwaron tsaunin wajen fitowa a fusace, wato Volcanic Vent. 

Idan kuma Tsaunin Kankara ne da ke teku (wato Glacial Ice), da zarar kunun dutsen ya fito, ya hadu da narkakken ruwan kankarar da ke tekun, zai sandarar da shi ne nan take zuwa gari ko tokar gilasai, sannan kuma kurar da ke fitowa daga tsaunin ta tarkata wannan garin gilasai tayi sama da su, don toshe hazo da sararin samaniya.  Tirkashi!   Kafin mu kai ga amfani, zai dace mu yi bayanin munanan tasirin wannan toka na kunun dutse.  Hakan ne zai bamu damar fahimtar cancantarsa wajen haddasa irin hasarar da yayi wa kamfanonin jiragen sama a watan Afrilu.

Shi dai wannan toka da zarar yayi sama, ba ya narkewa.  Sabanin irin tokan da muka saba gani da mu’amala da shi.  Shawagi yake yi a sama.  Don yana dauke ne da sinadarai masu wahalar sha’ani.  Da zarar ya hadu da ruwa ko danshi, yakan zubo kasa ne, ya daskare, ya zama gundarin dutse shi ma, amma nau’in Tuff.  Yana dauke ne da hayaki mai dauke da sinadarai masu cutarwa.  A shekarar 1783, lokacin da tsaunin Leki da ke Tsibirin Iceland yayi amai, wannan tokan kunun dutse ya yi sanadiyyar mutuwar kashi daya bisa biyar na mutanen kasar nan take.

- Adv -

Da wannan toka ya garzaya Yammacin Turai, yayi ajalin mutane sama da dubu ashirin da uku a kasar Ingila.  Shakar wannan toka dai lalura ce babba, musamman ga masu cutar da ke da alaka da numfashi, irin Asma.  Yana sanya kaikayin idanu.  Idan kuma ka shake shi lokacin da yake tattare da danshi, to yana tara wasu sinadarai masu dauke da narkakken sinadarin siminti a cikin huhunka.  Idan kuwa ya zubo kasa, bayan ya gama shawagi a sama, yana iya rusa rufin gidajen jama’a; iya gwargwadon yawansa a saman rufin gida.  Wannan na faruwa ne sanadiyyar sinadaran da ke dauke cikinsa, masu nauyi.  Yana lalata amfanin gona, yana kashe dabbobin gida, da na ruwa (irin kifaye da makamantansu), yana lalata hanyoyi, sanadiyyar santsi da hazo da yake haddasawa.

Idan kuma yana sama aka fara ruwa mai dauke da walkiya da cida, to yana haddasa daukewar wutar lantarki, da dukkan hanyoyin sadarwar tarho, ya kuma sanya firgici iya kusancinsa da mutane ko garin da ake ruwan.  Idan kuma ya riski direban jirgi a sama, lamari ya lalace kenan.  Yana iya toshe masa gabansa nan take, yana iya kara wa jirgin nauyi, sanadiyyar zubowar da zai rika yi a saman jirgin.  Wannan zai sa wani bangaren jirgin ya fi wani bangaren nauyi, musamman fukafukansa.  Idan kuwa haka ta faru, to akwai matsala. Domin jirgi na tafiya lafiya ne idan nauyinsa yayi daidai a dukkan bangarori.  Amma idan ya zama wani fiffiken ya fi wani fiffiken nauyi, to yana iya samun matsala nan take.  Bayan nan, yana tasiri wajen lalata fitilun da ke taimaka wa jirgin sauka.  Yana lalata farfelan jirgin idan ya shige ciki.  Dole kuwa haka ta faru, saboda sinadaran da ke dauke cikin wannan toka basu narkewa.  Idan jirgi ya ci gaba da tafiya a cikinsa, yana iya toshe masa bututun da yake gejin iska da shi, wanda kuma ke nuna masa iya tazarar tafiyarsa, wato Air Speed Indicator.

Kamar yadda bayanai suka gabata a baya, samuwar wannan toka a sama na iya hana direban jirgin sadarwa tsakaninsa da masu lura da shi a tashar da yake son sauka ko ya baro a baya.  Illa mafi muni da wannan toka ke yi wa jirigi shi ne ya sanya injin jirgin ya kama zafi, sanadiyyar toshe shi da yake yi.  Idan hakan ta faru, jirgin ba zai samu kuzari ba ko kadan, dole ya gangaro kasa-kasa, in kuwa ba haka ba dukkan injinansa na iya daukewa nan take.  Wannan shi ne abin da ya faru da wani jirgin British Airways F19, daidai lokacin da tsaunin Galunggung da ke kasar Indonesiya yayi amai, tare da watsa wannan toka a sararin samaniya cikin shekarar 1982.  Nan take dukkan injinan jirgin guda hudu suka daina aiki, sai da ya rage tafiya, ta hanyar gangarowa kasa daga tazara nisan kamu dubu talatin da shida (36,000ft) zuwa kamu dubu goma shabiyu (12,000ft). Irin wannan har wa yau ya faru da jirgin KLM Boeing 747 da ya taso daga birnin Amstadam na kasar Nedaland zuwa nahiyar Amurka.  Daidai lokacin ne tsaunin Redoubt da ke jihar Alaska ya fara amai.  Jirgin bai tsaya ba ya ci gaba da tafiya.  Saukarsa ke da wuya sai dukkan injinan jirgin suka yi dameji.  Sai da aka kashe dalar Amurka miliyan tamanin ($80M), aka fitar da tokar da mizaninta ya kai kilogiram tamanin (80kg) daga injin, sannan aka kwashe wajen watanni uku ana gyara.  Wadannan su ne kadan cikin illolin wannan toka na kunun dutse.  Ta bangaren amfani kuwa, yana da tasiri sosai wajen sanya kasar noma ta zama mai amfani da albarka, kamar dai yadda wancan kunun dutse nau’in Passive Lava ke yi.

Kammalawa

Daga bayanan da suka gabata, a bayyane yake cewa tsaunuka masu aman wuta na da matukar tasiri ga al’umma da kuma muhallin da suke ciki.  Duk da cewa munanan tasirinsu ya fi bayyana a fili, amma suna da wasu amfanoni da jama’a ke amfanuwa da su bayan lokaci mai tsawo da yin amansu.  Wani darasin da ya kamata mu koya daga rayuwa tare da wadannan tsaunuka shi ne, duk wani abin da Allah ya kaddara samuwarsa a doron kasa ko a cikin teku, to don amfanin dan Adam ne.  Ko da kuwa wannan abin na masa mummunar illa duk sadda ya bayyana, ko ya faru.  Kuma Allah na iya amfani da shi wajen halaka duk wanda ya ga dama cikin bayinsa.  Sannan samuwar wannan toka da ta bice sararin samaniya cikin watan Afrilu, wa’azi ne ga duniya baki daya, cewa idan za a yi hasara irin wannan cikin kasa da makonni biyu sanadiyyar aman da wani tsauni guda daya yayi a wata nahiya da ke can kurya, to me zai faru idan aka wayi gari dukkan tsaunuka masu aman wuta suka fara amai a lokaci guda?  Don haka mu fadaka, mu kuma shiga taitayinmu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.