Yadda Kasashe Ke Sanya Wa Fasahar Intanet Takunkumi (1)

Saboda karfin gamewar fasahar Intanet a duniya, an samu kasashe da dama sun fara kayyade mu’amala da ita. Cikin ‘yan kwanakin nan aka samu korafe-korafe daga kasashen Turai dake zargin kasar Sin sanadiyyar wannan ta’ada. Kai kace ita ce kadai ta kebanta da wannan aiki. Daga wannan mako za mu fara bayani kan wannan tsari na kayyade Intanet, da kasashen dake wannan aiki da kuma irin hanyoyin da suke bi wajen aiwatar da hakan.

295

Mabudin Kunnuwa

Cikin watan Yunin da ya gabata ne sauran kasashen duniya, musamman ma turai da Amurka suka kafa wa kasar Sin kahon zuka da azalzala cewa ta taka dokar dan Adam, sanadiyyar sabuwar dokar da ta fitar a farkon watan, cewa daga yanzu duk wata kwamfuta da za ta shigo kasar a matsayin kayan sayarwa ko amfani, dole ne kamfanin ko dillalin da zai shigo da ita ya sanya mata wata masarrafar tacewa da ta tanada mai suna Green Dam Youth Escort.  Wannan masarrafa ta kwamfuta aikinta shine lura da gidajen yanar sadarwar da mai amfani da kwamfutar ke ziyarta, da kuma tabbatar da cewa ta hana shi shiga wasu gidajen yanar sadarwa na batsa, kamar yadda hukumar sadarwar kasar ta sanar.  Wannan, inji gwamnati, shine dalilin bullo da wannan sabuwar doka.  Kuma tuni hukuma ta fara aiki kafada-da-kafada da kamfanonin shigo da kwamfuta kasar, irin su Apple, da Microsoft Inc. da dai sauransu, don ganin sun fara shigar da wannan sabuwar manhaja ko masarrafa cikin dukkan kwamfutocin da zasu shigo dasu kasar don sayarwa ko aiki dasu nan gaba.

Yin wannan sanarwa ke da wuya sai kwararru kan harkar kwamfuta da Intanet a kasar, da kuma sauran hukumomin kasashen Turai suka fara surutun cewa ba komai kasar ke son yi ba illa dakushe fadin albarkacin baki, musamman ma ta hanyar siyasa.  Wannan suka kuwa ya samo asali ne daga irin zargin da ire-iren wadannan kasashe suka saba yi kan kasar Sin wajen alakarta da shugabannin al’ummar Tibet da na Taiwan masu neman ‘yan cin kai, wadanda kuma ke samun goyon baya daga kasashen Turai da sauransu.  Hukumar kasar Sin dai bata juya baya daga wannan ra’ayi ba ko kadan, sai ma kara kaimi da take yi wajen hadin kai da kamfanonin kasashen Turai da na Asiya masu shigowa da kwamfutoci cikin kasarta, don tabbatar da cewa sun bi doka.  Tace dole ne ta kare al’ummarta daga irin ashararancin da ke tattare da wannan fasaha ta Intanet, na abinda ya shafi batsa; kowane irin nau’i ne kuwa.

A nasu bangaren, marubuta kan fasahar Intanet da kwamfuta sun ci gaba da nuna munin wannan abu da kasar Sin ke kokarin yi, da cewa yana cikin himmar da kasar ke yi ne wajen ganin ta hana, ko kuma a kalla ta sanya wa wannan fasaha mai muhimmanci takunkumi, (ta hanyar lura da irin gidan yanar sadarwar da ake ziyarta, tare da irin bayanan da masu mu’amala da Intanet din ke zubawa kan abinda ya shafi hukuma) wanda kuma yin hakan laifi ne mai girma, a cewarsu, kuma take ‘yancin dan Adam ne wajen fadin albarkacin baki ko samun bayanai.  Sai dai kuma yana da muhimmanci mai karatu ya fahimci cewa, wannan laifi da ake ikirarin kasar Sin na kakarin kutsawa cikinsa, akwai kasashe sama da hamsin – ciki har da kasar Amurka da Ingila da Faransa da Jamus da Rasha da Isra’ila – da tuni sun yi kaurin suna a hukumance wajen kare irin nau’in bayanan da ke Intanet, ta hanyoyi dabam-daban.  In kuwa haka ne, wannan ke nuna lallai akwai wata matsala kenan gamammiya dangane da tasirin wannan fasaha.  Don me wadancan kasashe da ma kowace kasa ke kokarin sanya wa wannan fasaha takunkumi?  Wasu hanyoyi ake bi wajen yin wannan aiki?  Wai shin, zai ma yiwu a sanya wa wannan fasaha takunkumi har hakan yayi tasiri?  Wadannan, da ma wasu tambayoyi masu muhimmanci ne wannna kasida za ta yi kokarin amsawa cikin wannan silsila mai matukar muhimmanci.  Da farko za mu fara da dalilan da ke sa kasashe ke daukan wannan mataki.

Don Me Ake Sanya Wa Intanet Takunkumi?

A takaice, tsarin hana shigar da wasu bayanai na musamman cikin Intanet,  ko kayyade yanayin samunsu ga jama’ar wata kasa ko al’umma, ko kuma hana mu’amala da wannan fasaha ta Intanet yadda mai yin hakan ke so, ko toshe ka’idar da ke sadar dashi ko wani gidan yanar sadarwa na musamman, shi ake nufi da sanya wa fasahar Intanet takunkumi, wato Internet Censorship kenan, a Turancin kwamfuta.  Wannan aiki kuwa ba wani bane ke yi illa gwamnatocin kasashe ko hukumomin da ke wakiltarsu.  Amma takunkumin da wasu ke sanyawa a gidajen yanar sadarwarsu, ta yadda baka iya ganin wasu bayanai ko samunsu, musamman a gidajen yanar sadarwar kasuwanci ko wasu harkokin kudi, ba a kiran shi da Internet Censorship.  Amma wanda kasashe ke yi yana shafan hatta asalin fasahar ne, kamar yadda mai karatu zai karanta nan gaba.  Kasashen Turai da sauran dokokin da ke bayar da kariya ga bayanai na ilimi da samunsa a ko ina ne a duniya sun haramta sanya kowace irin kariya ce da ke iya taimakawa wajen kare al’ummar kowace kasa daga samunsu.  Suka ce bai kamata a haramta karatun kowane irin littafi ba, ko shafin yanar sadarwa, ko wani shiri na talabijin ko gidan rediyo, wai don yana dauke da abinda a al’adar mutanen ko addininsu ake ganin haramun ne ko canfi ne mummuna. A tunaninsu dole ne a baiwa kowa ‘yan cin fadin albarkacin bakinsa, muddin hakan bazai kawo tashin hankali a kasa ko al’umma ba.  To amma duk da haka, me yasa wadannan kasashe musamman, ke sanya wa wannan fasaha mai dauke da dimbin ilimi takunkumi su kansu?

- Adv -

Akwai dalilai da yawa.  Da farko dai yana da kyau mai karatu ya fahimci irin tasirin da wannan fasaha ke dauke dashi, wanda hakan tasa kusan kowace kasa ke ganin “dole” ne ta sanya mata takunkumi ta wasu hanyoyin, ko dukkan hanyoyi, kamar yadda wasu kasashen ke yi.  Akwai siffofi guda uku da suka bambanta wannan fasaha da sauran hanyoyin sadarwa irinsu talabijin da rediyo da kuma mujallu da jaridu.  Siffar farko ita ce “gamewa”; da zarar ka fara mu’amala da wannan fasaha, za ka ji ka ne cikin duniya tsundum.  Baka jin akwai wani kariya tsakaninka da kowace kasa ne a duniya. Kana iya ziyartar kowace kasa, ka samu bayanai kan al’ummarta, da irin abinda hukumomi ke yi na kyautatawa ko munanawa.  Kana iya mu’amala da mutanen kasar, kaji ra’ayinsu, su ma su ji naka.  Wannan ke nufin duk al’adunsu da akidunsu, da addininsu, da kuma yanayin rayuwarsu, kana iya gani ko sani nan take.  Duk wannan har wa yau, kana iya yinsa ne ba tare da ka samu fasfo da biza din zuwa kasar ba. A takaice dai cikin ‘yan mintina da dakiku kana iya zagaye kasashen duniya ta hanyar wannan fasaha.

Siffa ta biyu ita ce siffar “jakar magori”; ma’ana duk hanyoyin sadarwar da suka rigayi fasahar Intanet bayyana, a halin yanzu ta lakume su. Don haka idan kana son karanta jarida, kafin mai saye a kan titi ya gani ya saya, zaka iya karantawa.  Idan kana son kallon shirye-shiryen talabijin, duk kana iya kallo.  Idan kana son sauraron shirye-shiryen gidajen rediyo, su ma duk akwai su kyauta.  Idan kana son buga waya daga kasarka zuwa kowane kasa ce a duniya, kana iya cikin sauki ko ma a kyauta.  Duk wannan, da fasahar Intanet a kwamfuta kana iya mu’amala dasu nan take, ba tare da ka biya kudi ba.  Hatta gidajen talabijin na kudi (irinsu CNN, da BBC da sauransu) masu amfani da tauraron dan Adam, kana iya samunsu kyauta, ka kalli shirye-shiryen, ko karanta duk abinda ke gidajen yanar sadarwarsu.  Siffa ta karshe ita ce siffar samar da hanyoyin kirkire-kirkire.  Abinda wannan ke nufi kuwa shine, sanadiyyar bayyana da yaduwar wannan hanyar sadarwa ta Intanet, da dama cikin mutane sun samu aikin yi a ciki, ta hanyar gina gidajen yanar sadarwa, ta hanyar saye-da-sayarwa, ta hanyar rubuce-rubuce, ta bayyanar kusan dukkan fannonin rayuwa da sabuwar hanyar aiwatar dasu cikin sauki, duk ta hanyar wannan fasaha.

Wannan yasa fasahar Intanet ta sha bamban wajen tasiri ga jama’a ko al’umma, idan ka hada tasirin sauran hanyoyin sadarwar da bayaninsu ya gabata.  Don haka akwai al’adu kala-kala a ciki.  Akwai addinai kala-kala a ciki.  Akwai rayuwa iri-iri a ciki. Akwai nau’ukan siyasa iri-iri a ciki.  Akwai hanyoyin koyo da sarrafa abubuwa kala-kala a ciki.  Wasu su yi daidai da abinda wata kasar ke so, wasu kuma su saba wa yanayin al’ada ko addini ko siyasarta.  Sannan ba a nan wannan tasiri ta tsaya ba kawai, wannan fasaha bata san iyakan da ke tsakanin kasa-da-kasa ba, balle ta nemi izni wajen shigar da bayanan da ke cikinta, ko kuma tantance irin bayanan da al’ummar kasar ke so.  Da zarar ka shiga kawai shikenan, duk abinda ke ciki kana iya mallaka ka sarrafa, ko yi mu’amala dashi kai tsaye, kuma nan take ba tare da bata lokaci ba.

Sanadiyyar wadannan siffofi da fasahar Intanet ta siffatu dasu da kuma tasirin da fasahar ke haifarwa, tasa kowace kasa ke da irin hanyar da take bi wajen ganin ta cin ma burinta na shugabancin siyasa ko addini ko kuma dora al’ummarta kan abinda take ganin shine daidai wajen mu’amala da wannan fasaha.  Wasu kasashe kan kayyade tsarin amfani da Intanet a kasarta ne don kautar da su daga miyagun al’adun wasu kasashe.  Wata kuma kan kayyade ne don wata manufa ta siyasa.  Ire-iren wadannan kasashe sun hada da manyan kasashen Turai da Amurka da kuma kasashen Asiya, irinsu Koriya ta Arewa, da Sin, da Biyetnam da Rasha da dai sauransu.  Masu kayyade fasahar Intanet don kaucewa gurbatuwar akida ko addini kuma galibi suna Gabas-ta-Tsakiya ne, irin su kasar Saudiyya da Yaman da Siriya da dai sauran kasashe.  Kasashe irinsu Iran kan kayyade sanadiyyar siyasa da kuma addini.  Haka kasashe irinsu Isra’ila da Turkiyya.  A takaice dai kowace kasa na da irin nata manufa da ke sa ta kayyade abubuwan da ke cikin fasaha na ilimi ko abin mu’amala.

Don haka masu bincike kan tasirin fasahar Intanet suka kasu kashi biyu; wasu na ganin kuskure ne babba idan aka ce haramun ne kowace kasa ta hana al’ummarta amfanuwa da wani nau’i na bayanai da ke cikin Intanet.  Saboda al’adu sun sha bamban; addini ya sha bamban; akidu sun sha bamban; haka nau’in siyasa ya sha bamban.  Kuma tun da kowace kasa tsarinta daban, kuma bazai taba yiwuwa kowace al’umma ta zama daya ba, dole ne, a cewar masu wannan ra’ayi, kowace gwmanati ta kare al’ummarta daga abinda take ganin zai gurbata musu tunani ko akidu ko al’adu; komai dadinsa kuwa, kuma duk yadda al’ummar ke jin dadinsa kuwa.  Domin abincin wani, guban wani ne.  hagun wani, shine daman wani.  Gabas din wani, shine yamman wani.  Kuma a bayyane yake cewa abubuwan da ke cikin wannan fasaha shi ma a cakude yake.

Masu ra’ayi na biyu kuma suka ce a a, bai kamata kowace gwamnati ko hukuma ta kayyade wa al’umma abinda zasu gani ko karanta ko kuma yi mu’amala dashi ba. Wannan, a cewar masu wannan ra’ayi, shiga hakkinsu ne.  Abinda kawai za ta yi shine ta ilmantar dasu kan abinda zai amfane su ko kuma cutar dasu.  Suka ce idan gwamnati bata yi ba, to wajibi ne ga kowane uba ko maigida ko kuma duk wani mai dauke da alhakin wanda ke karkashinsa, da ya tarbiyyantar dasu da dora su kan abinda yake ganin shine daidai a garesu.  A takaice dai, ko ma wani ra’ayi ne daidai, a bayyane yake cewa kusan dukkan kasashe sun kasa hakuri wajen barin wannan fasaha sake waiwai.  Shi yasa, kamar yadda mai karatu zai karanta a gaba, kusan rabin kasashen duniya – talakawansu da masu kudinsu, musulmansu da wadanda ba musulmai ba – sun kirkiri hanyoyi dabam-daban wajen sanya kariya daga irin bayanai ko nau’ukan abubuwan mu’amala da ke cikin fasahar Intanet.  In kuwa haka ne, to don me za a kafa wa kasar Sin kahon zuka?

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    Masha Allah Allah ya saka da alkhairi

    Zan so malaman yafara bayani akan Blogger/Wordpress da abubuwan da ya kunsa domin wayar ma da al’umma kai.

    Domin kara fadada harshen Mu ako ina a fadin Duniya, da kuma kara fahimtar da al’umma cewa a halin yanzu zasu iya yin Bincike da Hausa ba dole sai da English ba

    A lokacin da wani yaga ina yin bincike da Hausa abin da ya fara tambaya shine:

    Shin dama ana iya bincike akan abinda ya shafi Kimiya da Fasaha da Hausa? Ko wani abu makamancin hakan??

    Eh

    Amsar dana basa yayi mamaki Saboda a tinanin sa bai taɓa tinanin hakan ba.

    Faɗaɗa wannan hanyar wajen wayar ma da al’umma kai akan yadda zasu mallaki Blog/Website cikib sauki, da kuma avubuwan da ya kamata su sani kafin su fara aiki da hakan.

    Fatan Alkhairi

Leave A Reply

Your email address will not be published.