Sakonnin Masu Karatu (2011) (17)

A yau ma kamar sauran lokuta za mu duba sakonninku ne. A sha karatu lafiya.

64

Kamar makonnin baya, a yau ma wasikunku ne da na amsa.  Akwai saura da nake kyautata zaton nan da makonni biyu masu zuwa za su iso.  Sai dai zan cakuda su ne tare da wasu kasidun, don samun daman shiga wasu fannonin kuma.  Kafin nan, a kasidar da na gabatar kan tarihin Al-Imam Al-Khawaarizmi, na yi kuskure wajen rubuta shekarun da suka wuce bayan rasuwarsa.  Maimakon 1,200, sai na rubuta 200.  Wannan kuskure ne daga gare ni.  Na kuma gode wa wadanda suka bugo waya ko aiko sakonnin tes don nusar da ni.  Wannan ke nuna cewa lallai ana bin darasi yadda ya kamata.

Bayan haka, a halin yanzu masu karatu na iya ziyartar dukkan madawwanan da muka tanada don zuba dukkan kasidun da ke bayyana a wannan shafi.  Na loda dukkan kasidun da suka gabata inshallah.  Idan kasidun kimiyyar bayanai da intanet da wayar salula ko harkokin sadarwa ake nema, sai a je Makarantar Kimiyyar Fasahar Sadarwa da ke http://fasahar-intanet.blogspot.com.  Idan kuma ana bukatar zallar kasidu ne kan harkar sararin samaniya, da kimiyyar lissafi, da likitanci, da sinadarai, sai a je Zauren Kimiyya da ke http://kimiyyah.blogspot.com.  Na riga na sanar tuni a shafin Facebook, kuma da yawa cikin masu karatu da ke can sun ziyarci shafukan.  Duk wata shawarar da aka ga ta dace, sai a rubuto.  Baban Sadiq bai san komai ba, sai abin da Allah ya sanar da shi.  A sha karatu lafiya.


Assalamu alaikum Baban Sadik, a fasahar kere-kere kamar akwai dan tsafi wajen kera wani abu, ko dai zunzurutun ilmi ne?  Don wani malami ya ce mana duk inda fasaha tayi yawa, akwai sihiri. Ka huta lafiya, daga Kabiru Ahmad Gombe 08182374782 uribak.ahmad@yahoo.com

Malam Kabiru ai tun wajen Malaminku ka bar amsar tambayarka.  Domin ban san wani bangaren fasahar kere-kere bane ke kunshe da sihiri ko tsafi.  Sihiri dai shi ne juya hakikanin wani abu zuwa wani abu daban, ta hanyar da ta sha karfin tunanin dan adam a al’adance, tare da taimakon shedan ko kangararrun aljanu.  Da yace idan fasaha ta yi yawa akwai sihiri a ciki, abin da zan iya cewa kawai shi ne; sihiri nau’i biyu ne, kamar yadda wasu malamai ke bayani.  Akwai hakikanin sihiri da tsafi, wanda kowa ya sani, wanda kuma ke tasiri wajen warware imanin duk wani musulmi. Akwai kuma sihiri ta dabi’a, watau dan adam yayi wani abin da zai kama hankali da tunanin mutane (musamman dai zance), saboda kwarewa ko tasirin zancen, ba tare da taimakon wani aljani ko shedani ba.  

Irin wannan sihiri shi ne wanda Manzon Allah (SAW) ke magana a kansa a cikin wani hadisi da yake cewa, “Lallai a cikin zance hakika akwai sihiri…” duk malamai sun tafi a kan cewa ba hakikanin sihirin da ke warware imani ba yake nufi.  Domin sahabbai sun sha kulla baitukan wake a gabanshi, wasu lokuta ma waken shi ake yabo a ciki, kuma bai hana ba.  Kamar su Hassaan bn Thaabit, da Abdullahi bn Rawaaha, duk mawakansa ne masu yabonsa.  Abin da yake nufi shi ne, lallai wake na cikin abin da ke tasiri a zukatan mutane, irin tasirin da kusan sihiri ke yi wajen kama zuciya da dabi’a.  Wannan kuwa wani abu ne sananne ga duk wanda ya san rayuwar Larabawa musamman kafin zuwan Musulunci.  To, idan wannan malami na nufin irin wannan nau’in tasiri ne ko sihiri, sai mu ce eh, akwai.  Domin duk wanda ya ga inda ake abubuwa da dama na kere-kere, musamman inda ake kera jiragen sama, da yadda kwamfutoci ke sarrafa injina ko na’urorin da ke gudanar da wadannan ayyuka, zai ga kamar akwai sihiri a ciki, amma ina; tsantsar ilmi ne da kwarewa. 

Wasu kan ce wai Turawan kanfani kan yi tsafi a yayin da suke kokarin gina gadoji a cikin teku, da wasu gidaje da ke wasu wuraren da ake tunanin akwai kwankwamai a ciki, wai shi yasa ma idan suna haka, sai leburori ma’aikata su ta fadawa cikin teku, ko su yi ta hadari, don aljanu na shan jininsu ne sanadiyyar tsafin. Duk wadannan wasu abubuwa ne ko zantuka da babu hakika a cikinsu.  Ban ce karya bane kai tsaye, ban kuma ce turawa ba su yin sihiri ko tsafi ba, a a, suna yi.  Amma abin da ya bayyana mana da shi muke hukunci. Wannan shi ne abin da zan iya cewa.  Idan malam yana kusa, sai ya taimaka maka da karin bayani.  Allah shi ne masanin hakikanin abubuwa. Da fatan an gamsu.


Salam, tambaya ta kan ATM ne. Kamar ina da kudi a Current yaya zan juya su su koma cikin Savings ga na’urar ATM?

- Adv -

Eh to, abin da na sani shi ne, bankuna na iya jona miki taskar ajiyarka guda biyu (Savings da Current) su rika amfani da katin ATM guda daya.  Ma’ana kina iya shiga kowanne daga cikinsu don cire kudi.  Dangane da juye adadin kudaden da kike da su daga Current zuwa Savings kuwa, wannan sai dai ki bi tsarin “Transfer” don yin hakan.  Wannan ne zai baki damar shiga da kudaden da kike da su a Current su koma Savings.  Idan kika sanya katin, za ki ga inda aka rubuta “Funds Transfer”, idan kika matsa akwai inda za ki shigar da adadin kudin da kike son fitarwa, da nau’in taskar da kike son mayar da kudin, da sauran bayanai.  Babu wahala tsarin inshallah.  Da fatan kin gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadiq, barka da warhaka. Ina fatan kana lafiya, Allah yasa haka, amin. Tambaya ta ita ce: Me yasa idan mutum yana kallon bidiyo a intanet sai ya rika tafiya lakakai-lakakai, sannan ya dan tsaya, sai kuma ya ci gaba? Ba kamar yadda muka saba kallo a bidiyo CD/DVD ba? Wassalam! Daga Uncle Bash, J/Yola 07037133338, unclebbash@yahoo.com

A gaida Uncle Bash namu.  Wannan tsari na kallon hoto mai motsi ta Intanet shi ake kira “Streaming.”  Idan kai tsaye (Live) kake kallo a lokacin da abin ke gudanuwa, ana kiransa “Live Streaming.”  Dalilin da yasa kake ganin abin ba ya tafiya da sauri kamar ya kamata, shi ne babu inganci cikin tsarin Intanet din da kake amfani da shi.  Da a ce muna amfani da tsarin “Broadband” ne, da garau za ka gani, babu wani saibi balle tangarda.  Wannan shi ne kokarin da ake ta yi wajen ganin an inganta tsarin sadarwar Intanet a Najeriya.  A wasu kasashe ba ka iya bambance tashar talabijin ta gama-gari, da tashar talabijin ta Intanet (Internet TV), saboda ingancin sadarwar Intanet a kasashen. Da fatan ka gamsu.


Salam, barka Baban Sadiq. Ga tambaya ta: wacce irin gudunmawa kake ganin fasahar ICT za ta iya bayarwa ga nazarin Hausa? Ga adireshin Imail dina nan. ismailaliyu@gmail.com Daga Waziri

Malam Ismaila sai ka duba akwatin Imel dinka, tuni na tura maka kasidar Farfesa Abdallah Uba Adamu.  Sai ka saukar ka buga.  Allah sa  mu dace.


Assalamu alaikum, shin akwai yadda za a yi mutum ya samu makalolinka na aminiya wadanda ka gabatar a baya ta hanyar Imail? Bissalam

Eh kana iya samu, sosai kuwa. Sai dai kuma ganin cewa suna da yawa, ba za ka ji dadin karbarsu a lokaci daya ba.  Domin sun kai wajen 28MB, ma’ana mizaninsu ya kai wajen miliyan ashirin da takwas. Sai dai a turo maka su kadan-kadan.  Ko kuma ka je shafinmu da ke http://fasahar-intanet.blogspot.com don daukansu daya bayan daya, a duk sadda kake so.  idan kuma ka fi sha’awansu samunsu ta Imel din, sai ka turo adireshinka a turo maka.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.