Tsarin Amfani da Wayar Salula (5)

Kashi na 30 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

194

Tsarin aikawa da sako ta hanyar Fasahar Bluetooth abu ne mai sauki. Idan kana son aikawa da sako ta Bluetooth, abu na farko shi ne “neman” wayar salular da kake son aika mata da sakon.  Wannan shi ake kira Searching, a turancin fasahar sadarwa.  Da zarar ka yi wannan, ka’idar da ke lura da wannan aiki zata nemo maka wadanda ta hararo maka su, kai tsaye.  Dole ya zama suna tazarar da bai wuce taku talatin ba (30 Feets) ko mita goma (10 Meters) daga inda kake.  In sun wuce wannan tazara, ba za ka taba hararo su ba.  Idan aka hararo maka su, za ka samu bayanan da suke dauke dasu, ko kuma sunayen da masu su suka basu.  Da zarar ka nemo wayar da kake son hulda da ita, sai ta sanar da mai wayar cewa ana neman sa, sai ya amince, ta hanyar matsa “Accept”.  Idan ya amince maka, sai wayarka ta nemo ka’idojin da suka dace ta bi wajen aika sakon, ta kuma lika wa wannan waya da ta barbaro, alamar da za ta sheda ta wajen aika mata sakon.

Daga nan, sai kuma ta kara binciko cikin wancan wayar, don tabbatar da dacewa da wannan alama da ta lika mata.  A ka’ida, dukkan wayar salula ko kayan fasahar sadarwar da take iya saduwa da wata ta wayar iska, na dauke ne da suna da ke cikin rukunin lambobi, wanda ta kebanta dasu; kamar yadda kwamfuta ke dauke da lambobin IP, wato Internet Protocol Address.  To idan wayarka ta nemo sunan wannan waya da take son saduwa da ita, ta tabbatar da sunanta, sai ta bata suna na musamman, sannan sai ta nemo kogo (Port) mafi sauki da za ta iya aikawa da sakon, ba tare da mishkila ba. Da zarar ta nemo, sai ta fara barbara, don sheida wa wancan wayar salula, cewa ‘gani nan tafe’.

Idan aka amsa mata, sai ta fara aikawa, kai tsaye.  Idan ta gama aikawa, sai ta rufe wannan hanya, tare da yanayin sadarwan. Ita kuma wacce ake barbara, da zarar sakon neman alfarma ya zo mata, sai ta taimaka wajen nemo ka’idar da za ta yi wannan aiki na karban sako. In ta nemo, sai kuma ta zabi kogon (Port) da zai karbi wannan sako, don shigar mata.  Gama wannan aiki ke da wuya, sai ta fara sauraron sakon.  Da zarar an turo, sai ta karba kai tsaye.  Idan sakon ya shigo kogon da aka tanada masa kafin zuwa, sai ita wannan waya da ta karba ta rufe kofofin da ta bude da farko, don cika sadarwa.

Duk wannan na faruwa ne cikin lokacin da bai wuce dakiku ashirin ba.  Illa kawai aikawa da sakon ne ya danganta da yawan mizanin sakon; idan mai yawa ne, zai dauki lokaci.  Idan kuma kadan ne, nan da nan sai a gama.  Wannan tsari na aikawa, a yayin da ake aikawa din, shi ake kira Pairing, ko kuma Point to Point Communication (ko P2P, a lafazin ilimin aikawa da sako ta zamani.

- Adv -

Daga cikin alfanun da ke tattare da fasahar sadarwa ta Bluetooth akwai saukin aikawa da sakonni ba tare da ka kashe ko sisi ba. Ko da babu taro a wayarka kana iya aikawa da sakonni.  Abu na biyu shi ne, kana iya aikawa da lambobin waya ga wani ta hanyar fasahar Bluetooth.  A daya bangaren kuma, fasahar Bluetooth na iya maye maka gurbin masarrafar MMS, wajen aikawa da lambobi, ko aikawa da hotuna, ba sai lalai ta hanyar MMS ba, wanda hakan zai iya ci maka kudi, musamman idan wanda za ka aika masa a kusa yake da kai. Har wa yau, fasahar Bluetooth na iya hada ka mu’amala wajen musayar bayanai da wasu kayayyaki ko na’urorin sadarwa masu dauke da fasahar, a iya tazarar da hakan zai iya faruwa.

Misali, idan kana da wayar salula mai dauke da wakoki ko karatuttuka ko wasu jakunkunan bayanai na sauti da kake son saurare alhali kana tuki ko kana wani abu daban da ba ya bukatar shagala, kana iya samun lasifikar mota mai dauke da fasahar Bluetooth sai kawai ka nemo lasifikar ta wayar, ka saurari duk abin da kake son saurare ba tare da matsala ba.  Haka idan kana son buga wasu hotuna da kake dasu a wayarka, kana iya amfani da na’urar dab’i mai fasahar Bluetooth (Bluetooth Printer), daga inda kake zaune, ka buga dukkan hotunan da kake son dabba’awa, ko bugawa ba tare da matsala ba.

A duk sadda ka nemi wayar wani ta wayarka don musayar bayanai da wayarsa, wajen karba ko aikawa, kuma ka kasa samunsa, ta yiwu bai kunna fasahar Bluetooth dinsa bane.  Idan har a kunne take, to, watakila tazarar da ke tsakaninku ta wuce mita 10, sai a lura.  Idan tazarar ba ta wuce mita 10 ko taki 30 ba, to ta yiwu akwai matsala da dayan wayoyin biyu.  Sai kowannenku ya kashe fasahar Bluetooth dinsa, ya sake kunnawa.  Idan abin ya ki, a kashe wayar a sake kunnawa.  Duk yadda aka yi sai an dace.  Idan aka gano wacce ke da matsala daga cikin wayoyin biyu; an kashe Bluetooth an sake kunnawa, bai yi ba.  An kashe wayar, an sake kunnawa, abu bai yi ba, to, akwai matsalar da ke da alaka da babbar manhajar wayar.  Don haka sai a goge tsare-tsaren wayar ta hanyar “Resetting.”  A je “Menu,” a gangara “Security,” sai a karaso “Factory Settings.”  Idan aka matsa eh, wayar za ta koma sabuwa kamar yadda aka siyo ta.

Duk tsare-tsaren da aka mata za su share, amma lambobi da bayanan  sauti da bidiyo suna nan lafiya lau.  Amma duk hoton da ka sa a fuskar wayar zai share.  Haka duk muryar da ka sa a matsayin sautin wayar (Ringing Tone), zai share.  Da haka in Allah Ya so fasahar Bluetooth din za ta dawo yadda take, kamar yadda aka siyo wayar a farkon lokaci. A gaskiya fasahar Bluetooth na cikin masarrafan da basu cika samun matsala ba a wayar salula, duk yadda aka kai da amfani da su kuwa.  Sai dai idan mutum ya cika tsokale-tsokale a wayarsa.  Bayan tsarin aika sakonni na SMS, fasahar Bluetooth na biye wajen inganta karbuwar wayar salula a hannun jama’a a duniya baki daya.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.