Tsarin Amfani da Wayar Salula (3)

Kashi na 28 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

430

Mu’amala da Fasahar Intanet

Daga cikin hanyoyin aiwatar da sadarwa da samun bayanai a wayar salula musamman irin na zamani, akwai fasahar Intanet.  Wannan fasaha ce mai tasiri matuka a duniya yanzu.  Farkon bayyanar  fasahar Intanet ta ta’allaka ne kawai da kwamfuta.  Ma’ana, ta hanyar kwamfuta kadai ake iya mu’amala da fasahar.  To amma shekaru kasa da 15 da suka gabata zuwa yau, an samu hanyoyin ginawa da kuma bayyana shafukan Intanet ta wayar salula, cikin sauki, da kuma inganci.  Wannan hanya tana da matukar muhimmanci sosai.  Domin mai waya zai iya karanta labarai, da taskance su, da kuma ganinsu, duk ta wayarsa.  Sannan zai iya aika sakonnin Imel ta wannan hanya, da kuma karban sakonnin, duk ta wayar salalularsa.  Hakan na yiwuwa ne dangane da yanayin girma, da fadi, da kuma ingancin wayarsa.

Kafin a iya mu’amala da fasahar Intanet a wayar salula, dole ne ya zama tana da ka’idar sadarwar wayar iska ta Intanet, wato “Wireless Application Protocol,” ko “WAP” a gajarce.

Wannan ka’ida ce ke taimakawa wajen hada alaka tsakanin wayar salula da giza-gizan sadarwa na duniya, wato: “World Wide Web.”  Kana iya gane hakan idan ka je “Menu”, ka gangara kasa, ka ga “Web” ko “Internet” ko kuma “Browse.”  Ya danganci tsarin wayar da kamfanin da ya kera.  Da zarar ka ga tambari mai dauke da dayan wadancan tambari guda uku, to lallai wayar za ta iya shawagi a giza-gizan sadarwa na duniya.  Daga nan kuma sai abu na uku, wato kudin lilo da tsallake-tsallake.  Ma’ana, ya zama akwai kudi a cikin wayarka.  Domin da zarar ka shiga Intanet, nan take kamfanin waya zai fara diban nasa rabo daga abin da ke cikin taskar ajiyarka a waya.

Abu na karshe da ake bukata kafin iya mu’amala da fasahar Intanet a waya shi ne, tsare-tsaren kamfanin sadarwa, wato: “Network Configuration,” ko kuma “Configuration Settings.”  Wannan kuma daga kamfanin waya ne. Galibin lokuta wayar salula kan karbi wadannan tsare-tsare ne daga kamfanin waya kai tsaye, da zarar ka shigar da katin SIM cikin wayarka a karo na farko, ko a duk sadda ka cire ka sake mayarwa.  Musamman ma katin SIM din kamfanin Etisalat.  Haka ma na MTN ko Glo ko Airtel.  To amma idan wayarka ‘yar kasar Sin ce, wato: “China Phone,” wannan kam dole sai an sa wadannan tsare-tsare da hannu, wato: “Manual Configuration.”  Duk da cewa akwai wayoyi irin na kamfanin TECNO wadanda ke iya karbar wadannan tsare-tsaren kamfanin waya kai tsaye.  To, amma idan aka yi rashin sa’a ba ta karba kai tsaye ba, ta kuma iya sarrafa su ba, to dole sai an dangana da masu gyaran waya don su taimaka su shigar da hannu.

Sannan kana bukatar adireshin gidan yanar sadarwar da za ka shiga, muddin ta waya ne.  Wannan ya danganci bukatarka.  Illa dai, galibin gidajen yanar sadarwar da ake shigansu ta wayar salula adireshinsu kan canza.  Misali, idan kana son shiga shafin Dandalin Facebook ta waya, adireshin shi ne: www.facebook.com/mobile, ko kuma http://m.facebook.com.  Amma asalin adireshin shi ne: www.facebook.com.  To amma idan ka shigar da na asalin ma, nan take ka’idar da ke lura da aiwatar da sadarwa ta wayar salula za ta fahimci cewa ta waya kake kokarin shiga, nan take kuma za ta karkatar da kai zuwa shafin da ya dace da fuskar wayar salula idan har gidan yanar sadarwar da kake kokarin shiga ya tanadi shafi makamancin haka.

A Najeriya kamfanonin waya na da gidajen yanar sadarwarsu, inda za ka iya shiga daga wayar salularka, don mika kokenka ko kuma amfanuwa da masarrafan da suka tanada wa masu mu’amala da katinsa.  Har wa yau, wasu kamfanonin (kamar Etisalat) sun tanadi masarrafar mu’amala da Dandalin Facebook na musamman, don masu amfani da katinsa.  Idan kana amfani da layin Etisalat ne, da zarar ka shiga shafin www.facebook.com/mobile ko http://m.facebook.com nan take za a ce maka, ka saukar da manhajar Facebook na musamman don mu’amala da fasahar Intanet ba tare da ka kashe ko sisin kwabo ba.  Suna yin haka ne don sawwake wa masu amfani da waya hanyoyin ta’ammali da fasahar Intanet.

- Adv -

Kamar sauran ayyukan waya masu bukatar yanayin sadarwar kamfanin waya, mu’amala da fasahar Intanet a jumlace, ba kyauta bane.  Idan ka sa kudi a cikin katin wayanka, ka fara shiga shafukan Intanet, za a fara cire kudi ba kakkautawa.  Iya yawan shafukan bayanan da ka budo a shafukan da ka ziyarta, iya yawan kudin da za a cire.  Idan shafukan da ka shiga akwai hotona da bidiyo, to, za a cire kudi mai dimbin yawa.  Domin hotuna da bidiyo suna wakiltar mizanin bayanai ne mai yawa, musamman ma dai bidiyo.  Haka ma sauti.  Idan ka shiga shafin BBC harshen Hausa ka fara sauraren shirye-shiryensu, za a cire maka kudi sosai.  Sai ka shirya.

Sai dai kuma ta la’akari da ganin cewa jama’a kan so mu’amala da fasahar Intanet amma suna tsoron yawan kudin da za a cire musu, kamfanonin waya a Najeriya sun bullo da tsare-tsare daban-daban.  Misali, kamfanin MTN kan bayar da kyautar mizanin bayanai miliyan goma (10MB) a duk sadda ka loda katin 400 misali.  Kamfanin Etisalat ya bullo da tsarin EasyMega, inda za ka sa naira dubu daya, ka shigar, sai a baka mizanin bayanai miliyan 500 cikin wata guda.  Ko ka sa naira 500, a baka mizanin bayanai miliyan 200 a wata guda. Haka akwai tsarin da idan ka sa katin 200 a duk mako, kamfanin zai baka kyautar mizanin bayanai miliyan 15 a mako guda.  Duk wadannan tsare-tsare ne da suka bullo da su don saukake mu’amala da fasahar Intanet ta wayar salula, kuma don su ma su samu yawaitan kwastomomi cikin sauki. Hanyar kasuwanci ce.

Sai dai ba kowace waya ce za ka iya mu’amala da fasahar Intanet don kawai kana da kudi a katin wayarka ba.  Wayar salula nau’in BlackBerry suna bukatar tsari ne na musamman; irin tsarin da ake kira BlackBerry Internet Service (BIS), kamar yadda bayanai suka gabata a baya.  Ma’ana, ko naira miliyan daya kake da shi a katin wayarka ba za ka iya mu’amala da Intanet ba sai ka nemi kamfanin waya ya dora ka kan tsarin BIS, sai ya zare kudin daga katin wayarka, sannan ya dora ka a kan tsarin.  Misali, kamfanin Etisalat na karban naira 3,000 ne a duk wata kan tsarin BIS.  Idan ka sa kudin a katin wayarka, sai ka matsa *499*1# sai hash.  Da zarar ka sa za su zare kudin, sai su mika lambar wayar BlackBerry dinka ga kamfanin Research In Motion (RIM), wato kamfanin da ke kera wayoyin kenan, don ya jona ka.

Idan kayi rajista a wannan tsari, za ka iya mu’amala da fasahar Intanet a kowane lokaci, na tsawon lokacin da kake so, har na kwanaki 30, ba tare da tsangwama ba.  Babu iyaka kan mizanin bayanan da za ka yi ta’ammali da su.  Da hotuna, da bidiyo, da sauti, duk kana iya mu’amala da su, wajen gani, da saurare, da saukarwa a wayarka duk sadda ka so.  Haka idan wayarka irinsu iPhone ne, kana iya zuwa kamfanin wayarka, sai su dora ka kan wani tsari na musamman da zai sawwake maka kudin mizanin bayanai, don ka amfana da wayar sosai.

Idan ana ta’ammali da fasahar Intanet a wayar salula ya kamata a lura da wasu abubuwa masu muhimmanci.  Abu na farko shi ne, ba kowane shafin Intanet ya burgeka za ka kutsa ciki ba.  Akwai shafukan da ke dauke da kwayoyin cutar wayar salula, wato “Virus.”  Idan kayi rashin sa’a ka samu kanka a cikin shafi irin wannan, yana iya gurbata maka ma’adana da masarrafar wayar salularka; ta rikice, ka kasa sarrafa ta.  Sannan ba lale bane ka san dalili.  Haka za ka yi ta jele tsakanin masu gyaran waya da masu sayar da kayayyakinta, ba kowa zai iya gano abin da ke damunta ba.  Sai ka gama kashe kudi wajen masu gyara a karshe ace maka ai ga abin da ke damunta. Abu na biyu shi ne, ba kowane bidiyo, ko hoto, ko kuma shafi ya burgeka za ka saukar (Downloading) a wayarka ba.  Akwai hoton da shi kanshi kwayar cuta ce.  Saukar da shi a ma’adanar wayarka hadari ne ga rayuwarta baki daya.

Wasu cikin matasa kan saukar da hotunan taurarin fim na kasashen waje, irin su Angelina Jolie, ko Meena ko Solomon Khan ‘yan kasar Indiya, ko Rambo da dai sauransu, zuwa wayarsu, don kawata wayar, da nuna cewa lallai suna sonsu.  Abin da ke faruwa shi ne, galibin masu gina manhajar kwayar cutar kwamfuta don sharri a Intanet ko don leken asiri, sukan kirkiri masarrafa na musamman ne don yin hakan, amma kai za ga hoto ne, ba jakar bayanai irin wacce aka saba gani a matsayin masarrafa ba.  Idan ka dauki irin wannan hoto ka loda wa wayarka, sai Allah.  Sai a kiyaye.

Abu na uku, ga masu mu’amala da jama’a a Dandalin Abota musamman na Facebook, kun dai ji irin abin da ke faruwa, musamman lamarin wata matashiya ‘yar wani babban hafsan Soji da aka kashe kwanakin baya a Legas, duk ta Facebook aka fara alakar.  Ba kowane mutum za ka yi abota ta kut-da-kut da shi ba, ko kawance na kut-da-kut da ita ba. Ya kamata ka san waye shi ko ita tukun, kafin a kai ga matsayin aminantaka.  Matsalar matasanmu ita ce, muna da saurin amincewa mutane, musamman mata dai.  Irin wannan matsala ce mai girma.  Musamman ga mutumin da baka taba gani ba, baka taba sanin hakikaninsa ba, sannan baka gamsu da dabi’unsa ba.  Ba cewa ake ka zargi duk wanda ka gani ba, a a.

Abu na hudu shi ne, mu kiyayi bata lokacinmu wajen rubuta zantukan da ba su da amfani a shafinmu na Intanet ko na Facebook.  Wannan bai kamaci mai hankali ba.  Ace ka bata lokaci kana ta surutai marasa amfani gare ka da sauran jama’a.  Ka sani, a lokacin da kake hakan, kana bata lokacinka ne, wanda ba zai taba dawowa ba.  Kana bata batirin wayarka ne, wanda ba za ka kara dawo da shi ba.  Kana kuma bata ingancin rayuwarka ne, wajen salwantar da fahimtar da ta kamata a ce ka ciyar wajen ciyar da kanka ko al’umma gaba.  Sai mu kiyaye.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.