Tsakanin Kwakwalwa da Zuciya: Wa Ke Samar Da Tunani? (6)

Ga kashi na shida hudu kan binciken da muke yi wajen kokarin fahimtar bangaren dake samar da tunani, tsakanin kwakwalwar dan adam da kuma zuciyarsa. A sha karatu lafiya.

749

Sabanin Ra’ayi kan Ma’anar Zuciya a Larabci

Kamar sauran ayoyin da suka zo kan wasu mas’alolin shari’a, Malaman tafsiri sun sha bamban wajen fahimtar ma’anar kalmomin da ke nuni zuwa ga zuciya a Kur’ani da Hadisai ingantattu.  Wasu sun dauki kalmar a zahirin ma’anarta kamar yadda Allah ya kawo ta, basu mata tawili ba.  Ma’ana, basu karkatar da ma’anarta zuwa ga wani abu daban ba.  Wasu kuma sun dauki kalmar zuciya (“Al-Qalbu”, ko “Al-Fu’aad”, ko kuma “As-Sadr”) a matsayin Majaaz ne.  Wato kalmar da ke wakiltar wani abu daban, amma ba ita ake nufi ba.  Suka ce abin da ake nufi shi ne “Hankali” ko kuma “Basira.”

Bayan haka, wadanda basu yi wa wadannan ayoyi ko kalmomi tawili ba wajen tafsiri, suna dogaro ne da cewa, daga cikin ayoyin da Allah ya ambaci zuciya, akwai inda ya ambace ta yana mai danganta ta ga tunani ko hankaltar abubuwa.  Har wa yau, akwai kuma ayoyin da Allah ya ambaci kalmar zuciya tare da mahallin da take, wato kirji kenan. In kuwa haka ne, a cewar masu wannan ra’ayi, lallai akwai alakar da ke  nuna dangantaka a tsakaninsu, dangantaka mai karfi kuwa.  Domin Allah ba zai ayyana abu, tare da muhallinsa, ya kuma danganta masa wani aiki na musamman ba, face akwai hakan tare da abin da Allah ya ambata.  Domin daga cikin sifofin Allah madaukakin sarki shi ne, Mai hikima ne shi, yana dora kowane abu ne a mahallinsa; ba ya yin wani zance wacce ba ta bayar da fa’ida.

Suka ce wuri na farko da Allah ya ambaci zuciya yana alakanta ta da tunani shi ne cikin Suratul A’araaf, aya ta 179, inda yake cewa: “Kuma lalle ne hakika, mun halitta, saboda Jahannama, masu yawa daga cikin aljannu da mutane; suna da zukata, ba su fahimta da su….”  Suka ce Allah ya ambaci zukata (na mutane da aljannu), sannan yace ba su fahimta da su.  Fahimta kuwa, a cewarsu, ba ta samuwa sai ta hanyar tunani.  Wuri na biyu na cikin Suratul Taubah aya ta 87, inda Allah ke cewa: “…Sun yarda da su kasance tare da mata masu zama (a cikin gidaje). Kuma aka rufe a kan zukatansu, saboda haka, su, ba su fahimta.”  A nan Allah na ishara ga munafukan madina da suke kin zuwa yaki, da sakamakon da ya biyo bayan wannan mummunar akida tasu, ga zuciyarsu.  Ma’anar da wannan aya ke bayarwa iri daya ne da wanda ta gabace ta.

Sai wuri na uku cikin Suratun Nahali aya ta 108, inda Allah ke cewa: “…wadancan ne wadanda Allah ya bice hasken zukatansu da jinsu da gannansu. Kuma wadancan su ne gafalallu.”  Suka ce wannan aya ma tana nuna cewa lallai zukata na yin tunani. Domin idan babu tunani, babu yadda za a yi gafala, ko shagala da wani abu mai muhimmanci, ya samu.  Sai wuri na hudu cikin Suratul Israa’i aya ta 36, inda Allah ke cewa: “Kuma kada ka bi abin da ba ka da ilimi game da shi.  Lalle ne ji da gani da zuciya, dukkan wadancan, (mutum) ya kasance daga gare shi wanda ake tambaya.”  Suka ce wannan ke nuna cewa lallai zuciya na tunani.  Domin an hana mutum yanke hukunci ne da jahilci.  Idan kuwa zuciya ta zama babu ilimi a cikinta, to, za a rasa yakini (wato karfin tabbaci da irada) a tare da ita.  Idan aka rasa yakini a cikinta, to babu abin da zai maye gurbin ilimi sai jahilci.  Shi kuma jahilci alamunsa su ne shakku da rashin tabbas, da dimuwa.  Su kuma wadannan dabi’u ko yanayin zuci suna samuwa ne ta hanyar tunani.  Idan babu tunani, babu yadda za a yi a samu shakka ko dimuwa irin ta zuci.

Sai wuri na biyar, cikin Suratul Kahfi aya ta 28, inda Allah ke cewa: “…kuma kada ka bi wanda muka shagaltar da zuciyarsa daga hukuncinmu, kuma ya bi son zuciyarsa…”  Mun yi bayani a baya cewa babu yadda za a yi a samu shagala ba tare da tunani ba.  Sai wuri na shida cikin Suratul Hajji aya ta 46, inda Allah ke cewa: “Shin, to, basu yi tafiya ba a cikin kasa, domin ya zama suna da zukata wadanda za su yi hankali da su, da kunnuwa da za su saurare da su a tare da su?  Domin lalle ne idanun ba su makanta, amma zukata wadanda ke a cikin kiraza su ke makanta.”  Suka ce wannan aya na nuna abu biyu.  Na farko Allah ya kalubalanci kafirai da suyi tafiya a cikin kasa su ga yadda ya hallakar da wasu al’ummomin da suka gabace su, wannan zai sa su hankalta da zukatansu. Hankalta da abu kuma, kamar yadda muka sani, ba zai yiwu ba sai ta hanyar tunani.  Ba wai su kalli abin su san yana nan ake nufi ba, ba irin wannan hankaltar ake nufi ba.  Ana nufin su dauki darasi, su kokkoma da zukatansu kan abin da suka gani.  Wannan kuwa shi ake kira tunani.

Abu na biyu shi ne makantar zuci, wadda ke cikin kiraza. Ma’ana zuciyar da muka sani din nan dai, ita Allah ke nufi, a cewarsu.  Sai wuri na bakwai da ke cikin Suratu Muhammad, aya ta 24, inda Allah ke cewa: “Shin to, ba za su yi tunani bane kan Kur’ani, ko kuwa a kan zukatansu akwai makullansu ne?”  Wannan aya tana magana ne kan tunani dangane da ayoyin Kur’ani, da gaskiyar zantukan da ke cikinsa.  Allah ya ce ko akwai makullai ne da suka kulle zukatan kafirai, da har suka kasa yin tunani kan Kur’ani?  A nan Allah ya ambaci rashin tunani, ya alakanta shi da kullewar zuciya.  Wannan ke nuna da zuciyar a bude take, da tunani ya samu.

Sai wuri na karshe cikin Suratun Naas aya ta 5, inda Allah ke cewa: “…wanda ke sanya wasuwasi a cikin kirazan mutane.”  Wannan aya tana magana ne kan tasiri da gamewar wasuwasin shedan ga zuciyar dan adam.  Sai aka ambaci mahallin da zuciyar take, wato kirji kenan, don nuna cewa lallai wasuwasin shedan na da gamewa da kuma tasiri mai karfi wajen sabo.  Shi wasuwasi wani irin zancen zuci ne mai dauke da umarnin aikata sabo, wanda bawa ke ji a tare da shi.  Duk sadda ka ji kana son ka aikata wani aikin sabo, to ka san cewa lallai wannan jin da kake ji a zuciyarka, wasuwasi ne na shedan.  Wannan, a cewarsu, alama ce da ke nunawa a fili karara, lallai zuciya na tunani.  Domin da ba ta tunani babu yadda za a yi dan adam ya bijire wa dukkan wasuwasin shedan, wanda kuma a halin yanzu ba haka lamarin yake ba.  Ma’ana ba dukkan wasuwasin shedan bane yake tasiri wajen sa dan adam ya aikata sabo, in kuwa haka ne, kenan ashe zuciyar dan adam na tunani, wajen tantance irin umarnin da take samu a cikinta, kafin ta baiwa gabobin jiki umarnin aikatawa.  Bayan haka, akwai hadisin Nu’umanu dan Bashir wanda a karshensa Manzon Allah ke cewa: “…kuma lallai a cikin jiki akwai wani gudan tsoka; idan ya gyaru, jiki gaba dayansa ya gyaru.  Kuma idan ya baci, to, jiki gaba dayansa ya baci.  Ku saurara, ita ce zuciya.” 

Dukkan wadannan nassoshi na ishara ne zuwa ga wannan zuciyar da ke cikin kirjinmu, kamar yadda yazo karara a cikin wannan hadisi.

- Adv -

Tantance Hakikanin Lamarin

Daga bayanan da suka gabata, za mu fahimci cewa lallai akwai wani lamari tattare da wannan bangaren jiki da ake kira zuciya; shin, da ra’ayin masu cewa “hankali” ake nufi da kalmar “Al-Qalbu”, ko na masu cewa hakikanin “Zuciyar” ake nufi.  Domin a cikin Kur’ani an danganta “hankali” ga zuciya.  An danganta “tunani” ga zuciya.  An danganta “rai” ko “ruhi” ga zuciya.  An danganta “An-Nafs” (wato “zati” ko “hakikanin mutum”) ga zuciya.  An kuma danganta “fahimta” ga zuciya.   Dukkan wadannan kalmomi an kawo su a wurare daban-daban, a sigogi daban-daban, inda kalmar “Al-Qalbu” ke wakiltarsu, kamar yadda wasu malamai suka fassara.  Amma abin da aka fi danganta shi ga zuciya shi ne “hankali”.  To, ko ma dai mene ne, akwai wani  sha’ani da ke tare da wannan zuciya da Allah ya halitta mana.  Domin yawan Ambato – a Kur’ani, da Hadisi, da zantukan Malamai, da littattafansu, da kasidunsu – duk yana tabbatar da haka.

Wannan ishara da nassoshin shari’a suka yi ga zuciya ya sa manyan Malaman musulunci gaba daya sun mayar da hankulansu zuwa ga wannan bangare na jiki.  Suna masu danganta ayyuka daban-daban gare ta, wadanda suka shafi halayya da dabi’unta – irinsu imani, da taqawa, da yarda, da kunya, da kara, da tawakkali, da sauransu.  Kari a kan haka, sukan hada da “tunani”, daga cikin ayyukan da suka shafi zuciya.  Wannan a fili yake cikin rubuce-rubucensu. Abdullahi bn Mubaarak, daya daga cikin manyan magabata ya rubuta littafi mai suna: “Az-Zuhd”, mai dauke da bayanai kan dabi’un zuci da za su taimaka wa musulumi rage burinsa a rayuwa, don fusktanr lahira.  Imamul Ghazaali, Abu Haamid, shi ma ya yi bayani mai tsawo a shahararren littafinsa mai suna: “Ihyaa’u Uloomad Deen”, da wani littafi dan karami mai suna: “Mukaashafatul Quloob” inda a ciki ya ware babi na musamman kan tunani, wanda hakan ke nuna cewa lallai tunani na daya daga cikin ayyukan zuciya.

Bayan Ghazaali sai Abul Qaasim Al-Qushairee, a cikin shahararren littafinsa mai suna: “Ar-Risaalatul Qushairiyyah.”  Wanann littafi na dauke ne da bayanai kan ayyukan zuciya, wadanda mutum zai lazimce su don gina kyakkyawar alaka tsakaninsa da Allah.  Bayan shi sai Al-Imam Ibn Al-Qayyim, daya daga cikin manyan malaman kasar Sham a karni na 7.  Ya yi bayani mai tsawo a cikin  littafinsa mai suna: “Maddarijus Saalikeen, Baina Manaazili Iyyaaka Na’abudu wa Iyyaaka Nasta’een,” wanda sharhi ne na littafin Imamul Harwee kan dabi’un zuci, masu karfafa imani da alaka tsakanin bawa da Ubangijinsa.  A cikin littafin ya ware babi na musamman kan tunani, ya kuma alakanta hakan ga zuciyar bawa, don samun kyakkyawar saitin imani.

Daga cikin malaman wannan zamani akwai Sheikh Muhammad bn Saalih Al-Munajjid, ya rubuta littafi mai suna: “A’amaalul Quloob,” wato “Ayyukan Zukata.”  A ciki ya ware babi musamman kan tunani, ya kuma kawo wasu daga cikin ayoyin da muka yi bayani kansu a baya.  Daga shi sai Dakta Khaalid bn Abdulkareem Al-Laahim, farfesa mai karantar da fannin karatun Kur’ani a Jami’ar Muhammad bn Sa’ood na kasar Saudiyyah.  Ya rubuta littafi mai suna: “Qiraa’atun Bi Qalbin,” ma’ana: “Tsarin Karatu da Zuciya.”  A shafi na 5, ya kasa nau’ukan karatu, ta la’akari da wajen yinsu, zuwa kashi uku. Kashin farko shi ne yin karatu a bayyane, wanda ya kunshi motsa labba da harshe, da fitar da sautin da ake ji.

Sai kashi na biyu da ya kunshi yin karatu a asirce, ta hanyar motsa labba da harshe, amma mai karatu kadai ke jiyar da kansa. Sai kashi na uku wanda ya shafi yin karatu cikin sirri ba tare da motsa labba da harshe ba, sai dai zuciya kadai.  Ya kuma kasa nau’in karatu da zuci zuwa kashi uku; na farko yin karatu a asirce ta hanyar amfani da idanu da kuma zuciya. Na biyu ta hanyar amfani da zuciya da tsantsar hadda da aka yi a baya. Na uku kuma yin amfani da zuci kadai.  Wannan, a cewarsa, tsantsar tunani ne.  A shafi na 6, ya kasa nau’ukan zancen zuci zuwa kashi uku. Na farko shi ne yin magana da zuci kadai, wannan tunani kenan.  Na biyu shi ne yin zance da zuci da kuma harshe; ya zama zancen zuci ne harshe ke furutawa.  Sai na uku, wato yin zancen zuci da harshe, amma ya zama zancen harshe ya saba wa abin da zuciya ke furutawa (ko tunani ko tattaunawa a kai) – wannan, a cewarsa, shi ne munafunci, wanda da shi ne Allah ya sifata munafukai kan abin da ya shafi imani.

Abubuwan Da Ke Dabaibaye da Zuciya

Daga bayanan da suka gabata za mu fahimci lallai zuciya, wato wannan gudan tsoka da ke kirjinmu, tana da bubuwa da yawa da suka dabaibayeta, masu sa a ambace ta maimakon a ambace su.  Wannan ba ya nuna cewa ita kanta ba ta da wani tasiri, a a, akwai alamun ita ma tana da nata tasirin.  Ababen da suka dabaibaye zuciya su ne: “Hankali” (Mind/Sense of reasoning), da “Ruhi” ko “Rai” (Soul), da “An-Nafsu,” wato “zati” ko “hakikanin dan adam” (Self), da “Fahimta” (Understanding/Comprehension), da kuma “Al-Hayaatu”, wato “Rayuwa” (Life). Malaman Musulunci masana harshen Larabci da ilimin shari’a sun nuna cewa, “Ruhin” dan adam (Human Soul), idan tana cikin jikinsa, ita ce ke wakiltar “zatinsa” (“An-Nafs”), wannan ke sa ya samu “Rayuwa” (Life), har ya zama mai hankali, mai tunani – iya gwargwadon shekarunsa.  Da “Fahimta”, da “Irada”, da “Ilimi”, duk suna rataye ne a jikin hankalin dan adam.  Daga cikin wadanda suka yi wannan namijin kokari akwai Taajul Lugha, Muhammad ibn Qaasim, wanda aka fi sani da “Al-Ambaari”, cikin littafinsa mai suna: “Al-Adhdhaadu Fil-Lugha,” da kuma babban Malamin Lugha, wato “Al-Jarjaanee”, cikin littafinsa mai suna: “At-Ta’areefaat.”

To shi kuma hankali, wanda ke rataye da ruhin dan adam mai dauke da wadancan al’amura masu ban al’ajabi, a ina yake damfare a jikin dan adam?  Daga cikin wadanda suka amsa wannan tambaya akwai Dakta Kareema Mutawalli At-Tookhee, cikin littafinta mai suna: “Quloobun Ya’aqiloona Biha,” shafi na 7, bayan ta kawo ayar da ke Suratul Hajj (aya ta 46), ta bibiye ta da sharhin malaman tafsir, a karshe tace: “Wasu masana suna cewa ‘Mahallin hankali shi ne kwakwalwa da ke kai’, hujjarsu ita ce, a duk sadda aka daki mutum a ka duka mai karfi, yakan rasa hankalinsa.  Amma ingantaccen zance shi ne, zuciya ce ke dauke da hankali, kamar yadda bayanai suka gabata.”  Wannan shi ne ra’ayin Shawkaani, da Qurtubi, da As-Sa’aalabee da kuma Sheikhul Islam Ibn Taimiyyah; manyan malaman tafisirin Kur’ani.  Shi ne kuma ra’ayin Abdullahi dan Abbass (Allah kara masa yarda).

Mako mai zuwa in Allah ya kaimu, za mu kawo bayanai kan sabon nau’in binciken kimiyya da ake kan yi dangane da alakar da ke tsakanin zuciya da kwakwalwa, bayan nan ne za mu sani, a ilimance, wani bangare ne daga cikinsu ke samar da tunani.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.