Sakonnin Masu Karatu (2009) (2)

Ga ci gaban wasikun da muka samu a makon jiya nan.

65

Assalamu Alaikum, don Allah Baban Sadik ka taimakeni da yadda zan sa Opera Mini a cikin waya ta Nokia 6131, saboda samun saukin mu’amala da fasahar Intanet ta wayar.  Na gode, dalibinka: Danlami Muhammad Doya, Bauchi – 07066501753

Malam Danlami barka da war haka, da fatan kana lafiya.  Idan kana son sanya Opera Mini, dole ne kayi amfani da masarrafar Nokia Suite da wayar ta zo da ita a cikin CD, in akwai.  Idan kuma babu, kaje gidan yanar sadarwar Nokia da ke www.nokia.com, ka matsa alamar “support and applications”, ka saukar a kwamfutarka, ka loda mata (wato Install).  Daga nan sai kaje gidan yanar sadarwar Opera, dake www.opera.com, ka zabi kamfanin wayarka (nokia), za a zarce da kai shafin da zaka zabi nau’in wayarka (wato phone model).  Bayan haka sai ka saukar da masarrafar. Da ka saukar, sai ka loda wa wayarka ta hanyar masarrafar “Nokia Suite” da ka saukar a farko.  Kana gamawa shikenan, sai ka shiga duniyar Intanet.  Da fatar ka gamsu.


Salamu Alaikum Baban Sadik, tambaya ta ita ce: idan mutum yana da “WEBSITE”, wace hanya zai bi ya dora shi a yanar gizo-gizo?:  Aliyu Muktar Sa’idu, Kano – 08034332200

- Adv -

Malam Aliyu sannu da kokari.  Dangane da abin da ya shafi sanya shafukan yanar sadarwa a giza-gizan sadarwa ta duniya, akwai hanyoyi biyu.  Ko dai ka ajiye kwamfuta ta musamman, mai dauke da manhajar mika bayanai ta Intanet, wato “Server Program” (irinsu “FileTransfer Protocol” da sauransu), ka loda mata shafukan, ta yadda duk wanda ke son shiga gidan yanar zai iya samun daman yi.  Zaka yi hakan ne bayan kayi rajistan adireshin gidan yanar, wato “web site address”.  Kuma dole ne wannan kwamfutar ta zama a kunne take da’iman.  Saboda idan ta mutu, to babu yadda za a yi a iya samun shafin naka. 

Hakan kuwa da wahala, musamman a kasa irin tamu.  Sai in janareto zaka saya.  In kuwa ba haka ba, to da zarar ka gama gina gidan yanar sadarwa, sai kawai ka doshi kamfanin sadarwa, wato “Internet Service Providers – ISPs” ko “Website Hosting Company”, kuyi yarjejeniya kan tsarin adana maka shafinka, sannan ka biya su.  Zasu baka suna (username) da kalmar iznin shiga (password) don ka samu damar lura da shafin a ko ina kake.  Akwai ire-iren wadannan kamfanoni a Nijeriya. Idan baka san su ba, ka tambayi masu Mashakatar Lilo da Tsallake-tsallake, wato masu “Cyber Cafes”, za ka samu bayani wajensu mai gamsarwa.  Da fatan ka gamsu.


 Aminci a gareka.  Don Allah menene amfanin “OPERA”, kuma kyauta ake amfani da ita, kuma akwai wayoyin da bata aiki a cikinsu?  – Bashir Ahmad, Kano: 08032493020

Malam Bashir, “Opera Mini” dai manhaja ce da ke iya taimaka wa masu amfani da wayar salula shiga Intanet, wato “Browser” kenan, ko masarrafan lilo a Intanet.  Kyauta ake samunta a gidan yanar sadarwar kamfanin da ke http://www.opera.com/mini/download sai ka dubi bangaren dama daga sama, inda aka rubuta “PC Download”, ka zabi kamfanin wayarka.  Za a kaika inda zaka saukar da jakunkunan bayanan da zasu shigar maka da manhajar cikin wayarka.  Sai dai kuma, dole ya zama kama da kwamfuta, domin a kwamfuta zaka saukar da jakunkunan bayanan, bayan nan, sanna idan “Nokia” ce wayar, sai kayi amfani da manhajar shigar bayanai ta Nokia mai suna “NOKIA PC SUITE”, don loda mata.  Ba matsala, don har na sanya wa waya ta, nau’in “Nokia” 6230i.  Tabbas kam ba kowace waya bace opera ke shiga.  Ba kuma zaka san haka ba sai ka nemo nau’in wayar baka samu ba a shafin.  Hakan ke nuna cewa lallai bata dauka, shi yasa basu sanya ta cikin jerin wayoyin da ke shafin. Allah sa a dace.  Da fatar ka gamsu.  A gaida Umma.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.