Fasahar 5G: Jita-Jita Da Karerayi Kan 5G (2)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 25 ga watan Disamba, 2020.

251

Karerayi Kan Fasahar 5G (1)

A daya bangaren kuma, akwai karerayi da ake ta yadawa kan fasahar 5G, wadanda lafiyayyen tunani bazai karbesu ba.  Da yawa daga cikin wadannan karerayi sun shahara ne a farkon wannan shekara ta 2020.  Musamman lokacin da cutar Covid-19 ta fara yaduwa a kasashen Turai da Amurka.  Wasu karerayin kuma tsagwaron yaudare ce don kokarin cin ma manufar kasuwanci da tattalin arziki.  Amma kafin nan, zan so mu fahimce cewa galibin karerayin da ake ta yadawa kan alakar fasahar 5G da cutar sankara (Cancer), tsohuwar jita-jita ce, wacce har yanzu babu wani hujja mai karfi, ko ma mai rauni, da za a iya dogaro dashi don yarda da wadannan karerayi.  Yana da kyau mu bibiyi tarihi don samun Karin haske kan wadannan jita-jita mara asali.

A cikin shiri na musamman da tashar rediyon BBC Inquiry ta watsa a ranar 30 ga watan Afrailu, 2020 mai take: “Why Are People Attacking 5G Mobile Masts?”, Tanya Beckett ta bibiyi tarihin jita-jita kan kayayyakin sadarwa da tarihi ya taskance mana su, sama da shekaru 100 kenan. A hirar da tayi da wani Farfesa kan harkar sadarwa dake babbar jami’ar birnin Landan na kasar Burtaniya (University College, London), ya tabbata cewa lokacin da aka fara bullo da allurar riga-kafin cutar “Smallpox” da annobanta ya game duniya, mutane sun ta yada jita-jita cewa hukumomi a kasashen turai suna son mallake hankulan mutane ne, da shigar musu da cuta ta hanyar wannan allura.

Farfesan yaci da cewa, haka sadda aka kirkiri jirgin kasa don samar da sabuwar hanyar safarar mutane da kayayyaki.  Nan ma mutane sun ta yada karerayi.  Daga cikin manyan karerayin da aka ta yadawa akwai karyar cewa hukuma ta kirkirI jirgin kasa ne don ta mallake tunanin mutane, shi yasa idan kana cikin jirgin kasa ana tafiya dakai za ka rika jin ciwon kai, da amai na taso maka.  Sannan wasu ma suka ce ai dabara ce gwamnati tayi don leken asirin rayuwar mutane.  Wadannan su ne karerayin da aka ta yadawa sadda aka kirkiri jirgin kasa.  To amma tunda daman karerayi ne, duk abin da ake ta tunanin zai faru, bai faru ba.  A halin yanzu ma ba wanda ke iya tuna wadancan karerayi, balle ya yarda dasu.

- Adv -

Shekaru 40 da suka shige, sadda wayoyin salula suka fara yaduwa ma, an ci gaba da ire-iren wadannan karerayi.  Wanda kuma duk dai irin karyar ce ake ta yadawa yanzu, sai ma kara mata gishiri da ake tayi; amma duk asalin karerayin daya ne.  A lokacin cewa ake yi wayoyin salula za su yada cutar sankara (Cancer), kamar yadda ake cewa yanzu kan fasahar 5G.  Na biyu, aka ce yawan mu’amala da wayar salula wajen karba ko aiwatar da kira, za ta haifar maka da matsanancin ciwon kai saboda yawan tururin makamashin hasken rediyo da take fitarwa, wato: “radiation”.  Na uku, aka ce tana kashe garkuwar jiki; idan ka saba amfani da wayar salula, a hankali garkuwar jikinta za ta rika yin rauni, har a wayi gari ka zama kamar wanda curtar kanjamau ta kama shi.  Na hudu, aka ce hukumomi sun hada baki ne da kamfanin wayar salula wajen kirkirar wayar salalu don samun damar mallake tunanin mutane, da kuma leken asirin a kansu.

A cikin shiri na musamman da ya gabatar mai take: “The 5G Con That Could Make You Sick”, wanda tashar rediyon BBC Assignment ta watsa a ranar 18 ga watan Yuni, 2020, Tom Wright ya yi hira da wani masanin kimiyyar sadarwa don neman karin bayani kan dalilan da suka sa mutane a kasar Burtaniya suke ta kona na’urar yada siginar Intanet na fasahar 5G, musamman a birane irin su Liverpool.  A farkon shirin, Wright ya kunna wani shiri da tashar talabijin BBC ya watsa a shekarar 2007, cikin shirinsa mai suna: “BBC Panorama”, lokacin da hukumar Burtaniya tayi yunkurin sanya na’urorin yada siginar Intanet a makarantun kasar gaba daya, wato: “Wi-Fi” kenan. Shirin na dauke ne da jita-jitan mutane kala-kala kan ire-iren abubuwan da ake cewa wannan na’ura tana haddasa wa na rashin lafiya da sauransu.

Cikin bayaninsa ne wannan kwararre ya tabbatar da cewa lallai an ta watsa jita-jita ba adadi, sanadiyyar wannan yunkuri.  Wannan yasa abin ya zama kamar wata annoba ce ta afka wa kasar.  Hankalin jama’a ya tashi, kowa ya tsorata.  Domin wasu daga cikin masu yada jita-jita sun ce idan aka sa wannan na’ura a makarantu, matsanciyar ciwon kai za ta yadu, da tsantsar damuwa, sannan na’urar za ta kashe garkuwar mutanen da suke kusa da inda na’ura take, saboda yada makamashin hasken rediyo da take a lokacin da ake amfani da ita.  Har a lokacin aka samu wadanda da zarar sun kusanci wannan na’ura, sai kawai suji ciwon kai ya kama su nan take.

Hakan ya ja hankalin wani Farfesa dake kasar Jamus mai suna Dr. Makel.  Inda ya gudanar da binciken kimiyya na musamman don kokarin gano gaskiyar wannan lamari.  Sai ya samu na’urar “Wi-Fi”, ya jona ta da na’urar dake tunkuda siginar Intanet gareta, wato: “Router” kenan.  Sannan ya samu wadanda zai gudanar da gwajin a kansu, ya kunna musu wancan shiri na BBC Panorama, suna kallo, kuma ya dora wa kowanne daga cikinsu wata na’ura wacce ya jona ta da wancan na’ura ta “Wi-Fi”.  Amma sai ya kashe na’urar “Router”, wacce ita ce ke kai siginar zuwa na’urar “Wi-Fi”.  Amma bai sanar da wadanda yake gwaji a kansu ba.  Sun dauka a kunne take.  Dabarar ita ce, don ya gane in dai da gaske ne wannan sigina da na’urar “Wi-Fi” ke watsawa shi ne ke haddasa wa mutane ciwon kai.  Bayan tsawon mintina 15, sai biyu daga cikin wadanda yake gwaji a kansu suka ce don Allah a cire musu wannan na’ura dake kansu, domin ciwon kai ya fara damunsu.  A karshe ya tabbatar da cewa galibin masu cewa suna kamuwa da ciwon kai, ba komai bane ke haddasa musu sai don da zarar sun fara kallon wannan shiri na BBC Panorama, nan take sai tunaninsu ya sauya, damuwa ta addabesu, har ciwon kai ya fara kama su.  In ba haka ba, a ka’ida bai kamata su samu wata matsala ba.  Tunda sadda suke kallon shirin, na’urar dake isar da siginar Intanet ga na’urar “Wi-Fi” a kashe take.  Kenan, duk da cewa na’urar “Wi-Fi” a kunne take, babu wani aiki da take yi.  Ba ta karban wani sako, kuma ba ta isar da komai.  Sannan hakan na nuna cewa babu wani makamashi na hasken rediyo da take watsawa, balle har wani ya kamu da mummunar tasirinsa, in ma yana dauke da tasiri mummuna kenan.

Wannan, a takaice, ke nuna mana cewa jita-jita kan illar makamashin hasken rediyo da wayoyin salula ke fitarwa ko watsawa a sadda ake amfani dasu, ba wani abu bane sabo.  Sai dai bayyanar fasahar 5G ya sake haifar da wasu nau’ukan karerayin da a baya ba a taba yinsu ba.  Wannan shi ne abin da makalar dake tafe ke dauke dashi.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.