Sharhin Littafin “Kwamfuta”, Na Malam Salisu Hassan (Webmaster) (3)

An buga wannan makala ne a jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 17 ga watan Janairu, 2020.

322

Dangane da tsarin rubutu kuwa, Malam Salisu ya zuba harshen turanci sosai a cikin littafin. A tunanina, dalilin hakan ba ya rasa alaka da abubuwa biyu: na farko shi ne asalin wannan ilimi daga harshen turanci ne.  Don haka, rubuta littafi kan ilimin kwamfuta a harshen Hausa ba zai taba yiwuwa ba sai da tsofa kalmomin turanci, tunda su ne asali.  Na biyu kuma, saboda da yawa cikin waxanda suke da ilimin kwamfuta cikin Hausawa a yau, za ka samu kashi 90 cikin 100 na kalmomin da suka san vangarorin kwamfuta dasu duk cikin harshen turanci ne.  Don haka, kusan dukkan babukan littafin an rubuta su ne cikin harshen turanci, ba da Hausa ba.

Ta vangaren ma’anonin kalmomi kuma, marubucin bai rike wani tsari guda wanda ya tabbata a kai ba.  Da farko dai, galibin kalmomin da ya fassara bai basu suna tilo ko murakkabi ba.  Galibi yakan yi bayanin ma’anar Kalmar ne, sannan ya kawo misali don mai karatu ya fahimci ma’anar.  Misali, a shafi na 75 inda mawallafin ke bayani kan ma’anar “CPU”, ya yi amfani da kalmomi sama da xaya ko biyu tsakanin Hausa da turanci, don fahimtar da mai karatu ma’anar wannan kalma cikin sauki.  Ga yadda yasa abin nan:

CPU ko kuma a kira shi da Processor wani lokaci ma shi ake kira da ƙwaƙwalwar kwamfuta … shi ke kasancewa mai fashin baki da fassara ga dukkan abin da yake faruwa a cikin kwamfuta. Iyakar abin da za a iya maka misali shi ne mutumin da ya je ƙasar da ba sa jin yarensa kuma shi ba ya jin yarensu dole yana buƙatar  tafinta wannan tafintan shi ke jin yaren shi kuma yana jin yaren su.

A wasu wuraren kuma yakan yi amfani da Kalmar turanci kai tsaye ba tare da kawo ma’anarta ga mai karatu ba, musamman idan a baya ya ambaci Kalmar.  A wasu lokuta kuma yakan yi haka tun kafin ya ambaci Kalmar a wani wuri da ya gabata. Kyakkyawar misali na shafi na 94 a Babi na 4 (Input Devices), inda yake bayani kan ma’anar kalmomin “Input” da kuma “Device”.  Yana cewa:

Input na nufin shigar da data ko program ko umurni ta hanyar da ɗan adam zai iya umurtar kwamfuta da shi. Device kuma na nufin kayan lantarki…

- Adv -

A baya ya kawo ma’anar “data” a Babi na 1, amma da yazo Babi na 4 sai ya sake ambatar Kalmar cikin harshen turanci, maimakon harshen Hausa kamar yadda wasu za su zata.  A xaya vangaren kuma, ya ambaci kalmar “program” a turance a nan, wanda bai riga ya ambaci Kalmar a ko ina ba kafin wannan wuri. Wannan salo ne da marubucin ya xauka saboda wasu dalilai.

Shawarwari

Bayan nazari da bita kan littafin “Kwamfuta” har sau uku da nayi, daga cikin abubuwan da za su taimaka wajen qara inganta littafin shi ne, rage yawan kalmomin turanci ta hanyar fassara su cikin gajerun jumloli.  Wannan zai qara fahimtar da mai karatu cikin sauqi.  Ta vangaren jumlolin littafin kuma, zai dace a rage tsayinsu.  Saboda gajerun jumloli sun fi saurin isar da ma’ana, musamman ga littafin da ke qoqarin isar da wani sabon ilimi irin wannan, wanda rubuce-rubuce basu yaxu a fannin, cikin harshen Hausa. Haka nan, zai dace idan aka ba da ma’anar kalma a farko cikin wani babi a harshen Hausa, to, idan aka zo ambaton Kalmar a wani wuri a ambaceta cikin ma’anar da aka bata a harshen Hausa; in yaso sai a sanya asalin Kalmar turancin a cikin baka biyu, misali: “Beran kwamfuta” (Mouse).  Ko “Allon shigar da bayanai” (Keyboard).  Hakan zai qara tunatar da mai karatu asalin Kalmar da aka ciro Kalmar Hausar.  Bayan haka, zai dace ayi bitar ma’anar wasu kalmomi.  Misali a shafi na 231, mawallafin ya fassara Kalmar “Internet” da “Web” da ma’anar “Yanar Gizo”, maimakon “Yanar Sadarwa”, wanda shi ne yafi isar da ma’ana mai inganci.  Haka Kalmar “Script” a fannin gina manhajar kwamfuta, an fassarata da: “Surkullen yaren kwamfuta”.  Wannan bazai baiwa mai karatu kyakkyawar fahimta kan sakon da Kalmar ke isarwa ba. “Script” nau’i ne na yaren gina manhaja ko shafukan Intanet.  Sannan Kalmar “surkulle” na ishara ne ga wani abin da ba shi da haqiqa; kamar rufa ido ne.  Wannan ya sava wa ilimin gina manhajar kwamfuta, wanda haqiqa ne shi, ba surkulle ba.  Ba dukkan mai karatu zai fahimci asalin ma’anar ba.  Ina ganin bitar ma’anar Kalmar zai dace don isar da ma’ana mai inganci.

Kammalawa

A karshe, wannan littafi ne da duk mai son fahimtar yadda kwamfuta ke aiki da gudanuwa zai fa’idantu sosai dashi.  Duk da cewa akwai kalmomin turanci da dama, kamar yadda na sanar a baya, hikimar hakan a fili yake. Rubuce-rubuce a harshen Hausa kan fannin kimiyya da fasahar sadarwa, musamman na kwamfuta, basu yaxu sosai ba a qasar Hausa.  Daga cikin manyan qalubale dake gaban harshen Hausa wajen ci gaba a wannan fanni, akwai rashin daidaituwar ma’anonin kalmomin turanci na wannan fanni.  Ma’ana, samun daidaito tsakanin masana kan ma’anar kalma, misali: “Click” – “Matsa” ko “Danna”?  Haka idan ka xauki Kalmar: “Storage” – “Ma’adana” take nufi ko “Ma’ajiya”?  Ga Kalmar; “Memory” – “Kwakwalwa” take nufi ko “Ma’adana”?  Da sauran ire-irensu.

Wannan qalubale ne da ya kamata masana harshen Hausa a jami’o’inmu su tunkara, tare da haxa kai wajen ganin an tabbatar da abin da zai zama abin dogaro.  Lokacin da marubucin wannan littafi ya aiko mini don tofa albarkacin bakina, abu na farko da ya fado zuciyata Kenan.  Shi yasa a karshe da na gama bitar littafin, daga cikin uzurin da na bashi na rashin tabo ko Magana kan ma’anonin da ya baiwa galibin kalmomin turanci da ya kawo a littafin, shi ne rashin daidaitaccen tsari abin dogaro.  A yanayi irin wannan kuwa, hanya mafi sauqi ita ce samar da daidaitaccen tsari da zai baiwa waxannan kalmomi ma’anonin da aka amince a kansu.  Kafin samuwan hakan kuwa, dole ne mu haqura da abin da ya samu.  A hankali, watarana sai labari.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.