Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (4)

Idan masu karatu na tare damu, bamu gushe ba wajen kawo hujjoji daga Kur’ani kan ittifakin da ke tsakanin malaman kimiyyar sararin samaniya da na halittu kan gaskiyar abin da ke cikin Kur’ani wanda ya shafi kwarewa da ilimin da suke karantarwa.  A yau zamu sake dulmuya don ci gaba.  A mako mai zuwa kuma zamu yi bankwana, saboda abin da yawa, wai maye ya shiga kasuwa. A yau zamu koma kan tsarin samar da halitta ne.  Ga abin da suka ce nan:

552

KIMIYYAR HALITTU 

————————————

Duk Wata Halitta Mai Rai, Daga Ruwa Aka Samar Da Ita

A cewar malaman kimiyyar halittu na zamani, wato Biologists ko kuma Embryologists, duk wata halitta mai rai na dauke ne da sinadarin da ke samar da ita, wanda suke kira Cytoplasm a Turance.  Kuma wannan sinadari ko matattarar sinadaran da ke tafiyar da rayuwa na Cytoplasm, kashi tamanin cikin dari na abin da ke cikinta ruwa ne.  Har wa yau, da tafiya tayi nisa, bincike yayi tsanani ta hanyar amfani da na’urorin binciken kwakwaf na kimiyya, sai wadannan malamai suka sake sanar da mu cewa “ai duk wata halitta da ke yawo a doron wannan duniya, to kashi hamsin zuwa casa’in na abin da ke jikinta duk ruwa ne.”  Sannan suka sake tabbatar da cewa babu wata halittar da zata iya rayuwa ba tare da ruwa a jikinta ba, ko cikin abin da take ci na abinci. Wannan a fili yake.  Domin ruwan da ke jikin dan Adam shi ne kashi saba’in zuwa casa’in cikin dari na abin da jikinsa ya kumsa.  Duk da cewa idan mutum yayi rauni, jini muke gani yana kwarara; hakan ya faru ne saboda hanyoyin da ke dauke da jini a saman karkashin fata suke, kana iya taba su.  Amma da zarar mutum ya fara gudawa, sai ka nemi kuzarinsa ka rasa.  Duk ruwan da ke jikinsa ya bi kasa.

Ruwa abokin aiki.  Binciken nan an yi shi ne cikin ‘yan karnonin da basu shige biyu ba zuwa uku. To me Kur’ani ya gaya mana, shekaru dubu daya da dari hudu da talatin da suka wuce?

Tabbaci Daga Kur’ani

Hakika Al-Kur’ani ya sanar damu wannan tuni.  A muhallin da ake da karancin ruwa.  A zamanin da babu wanda yake mafarkin samuwar wasu na’urorin bincike irin na zamani da muke da su a yanzu.  Cikin  sahara.  Cikin yashi da duwatsu.  Ga abin da Allah Yace:

“…kuma mun halitta daga ruwa, dukkan wani abu mai rai…”  (Ambiya’: 30)

Wannan aya tafi gamewa, abin da ke nuna cewa dukkan wani abu mai rai, to asalinsa da kuma abin da ke tafiyar da shi, shi ne ruwa.  A wasu wuraren kuma Allah Ya nuna cewa dukkan wata dabba daga ruwa aka halicce ta.  Ga abin da yace:

“…kuma Allah ne Ya halicci kowace dabba daga ruwa.”  (Noor: 45)

A karshe kuma ya sake tantace cewa, kowane jinsin dan Adam, namiji da mace, su ma daga ruwa ya halicce su.  Ga abin da yace:

“…kuma (Allah) Shi ne wanda ya halicci jinsin mutum daga ruwa.”  (Furqaan: 54)

- Adv -

Wannan ke nuna cewa Al-Kur’ani littafi ne da ya zo daga wajen mahaliccin wannan duniya da dukkan abin da ke ciki na halittu, kowane iri ne kuwa.  In kuwa ba haka ba, to babu yadda za a yi shekaru sama da dubu daya wani ya hango wannan sirri da ke tattare da halittu na ilimi.

Tsarin Samar da Halitta a Mahaifa

Cikin shekarun baya ne (wajajen shekarun 1970 – 1980) wasu cikin hukumomin kasashen larabawa suka tattara dukkan ayoyin Kur’anin da ke ishara ga yadda dan Adam ko halitta ke samuwa a cikin mahaifa.  Bayan tattara wadannan ayoyin, sai suka fassara su zuwa harshen Turanci, sannan suka doshi wani kwararre kan ilimin samar da halitta a mahaifa (Embryologist), mai suna Farfesa Keith More, babban farfesan ilimin samar da halitta a mahaifa da ke Jami’ar Toronto, a kasar Kanada.  Kafin mu yi nisa, wannan mutum ana ji dashi a duniya har a yau, wajen sanayya kan fannin samar da halitta a mahaifa, wato Embryology.  Kuma galibin jami’o’in duniya na amfani da littafinsa ne don karantar da daliban wannan fanni a matakin farko.  Da suka doshe shi da wadannan ayoyi fassararru, saka ce bukatarsu ita ce, ya karanta su, karatu na hakika, ya kuma fahimce su sosai, sannan, a karo na karshe, ya gwama su da ilimi ko kwarewar da yake da ita kan wannan fanni na samar da halitta.  Idan ya gama, suna jiran jawabinsa.

Farfesa More na gama karanta wadannan ayoyi, sai yace musu dukkan abin da Allah Ya fada kan yadda ake samar da halitta (musamman ta dan Adam) a mahaifa, daidai yake da abin da suke karantarwa da bincike a kai a wannan fanni.  Ya kuma kara da cewa, babu inda aka samu cin karo da abin da Kur’ani ya sanar.  Sai dai akwai wasu ayoyi wadanda bazai iya cewa komai kan daidai ko rashin daidai din abin da suke tabbatarwa ba, a kimiyyance.  Dalili kuwa shi ne, a cewarsa, babu wani bincike ko rubutu na musamman da malaman kimiyyar halittu suka yi a game dasu.  Daya daga cikin wadannan ayoyi, don kada mu tsawaita, ita ce ayar da ke cewa:

“Kayi karatu da sunan Ubangijinka mahalicci.  Ya halicci mutum daga gudan jini.”  (‘Alaq: 1-2)

Bayan ma’anar “gudan jini” da kalmar “’Alaq” ke bayarwa, har wa yau kuma tana nufin “wata halitta mai d’amfarewa ko makalewa a jikin wani abu – irinsu tsutsar-ciki da makamantansu.”  Wannan shi ne abin da ya daure wa Farfesa More kai.  Yace shi tun da ya fara karantar wannan ilimi, bai taba sanin cewa halittar da ke mahaifa, a matakin farko, a irin wannan sifa take kasancewa ba.  Don haka sai nan take ya shiga dakin bincike, inda ya samo dan jaririn halittar da ke matakin farko (wato Embryo), ya sanya shi karkashin na’urar bincike mai kaifin hange. Bayan ya gama nazarin wannan halitta, sai ya dauko kwarangwal din irin wancan halitta da kalmar ke nufi a daya bangaren, sai ya ga kamar Hasan da Huseini ne! Carancas suka yi kama!  Wannan abu ya bashi matukar mamaki.  Sannan yace ya karu da ilmi mai dimbin yawa sanadiyyar samun tarjamar wadannan ayoyin Kur’ani masu nuni ga asalin halitta.  A kan haka Farfesa More ya amsa tambayoyi wajen sama da tamanin da ke magana kan asalin halitta a mahaifa, wadanda kuma ke da asali daga Kur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW).  Inda a karshe ya nuna cewa lallai dukkan nassosin da suka zo cikin Kur’ani masu bayani kan asalin halittar dan Adam a mahaifa sun dace da irin abin da suka sani a wannan fanni.  A karshe ya kara da cewa: “da ace an mini wadannan tambayoyi shekaru talatin da suka wuce ne, da ko rabin su bazan iya amsawa ba, saboda rashin hujjoji daga binciken kimiyya.”

Kafin ayi masa wadannan tambayoyi, Farfesa More ya rubuta shahararren littafinsa mai suna “The Developing Human”.  Amma bayan samun wadannan nassosi na Kur’ani, da kuma karin ilmin da ya samu cikinsu, sai yayi bitar littafin, inda yayi masa gyare-gyare da kuma kare-kare.  Ya fitar dashi cikin shekarar 1982, inda a karshe, saboda tasirin littafin kan abin da ya kunsa na ilmi, sai da yaci gasar “Gwarzon Littafin Shekara kan Kimiyya” (The Best Medical Book of the Year), wanda mutum daya ne ya rubuta shiA halin yanzu an fassara wannan littafi zuwa harsuna da dama, kuma kamar yadda bayani ya gabata, yana cikin littafan da Jami’o’in duniya ke amfani dashi wajen karantar da dalibai a matakin farko.

A shekarar 1981, an yi taron Manyan Likitoci na Duniya a birnin Damman da ke kasar Saudiyya, kuma Farfesa More ya samu halatta. Da jawabi yazo kanshi, sai yace:

 “Hakika ina matukar murna da na samu damar amsa tambayoyi da dama da aka min kan abin da ya shafi samar da halitta a mahaifa, daga nassosin Kur’ani. Daga abin da na karanta cikin wadannan ayoyi, a bayyane yake cewa lallai Muhammad ya samu wadannan bayanai ne daga “Ubangiji” ko “Allah”, domin kusan dukkan wadannan bayanai babu wanda ya isa ya binciko gaskiyarsu sai bayann daruruwan shekaru.  Wannan ke nuna mini cewa lallai Muhammad Manzon Allah ne!”

A nasa bangaren kuma, Dakta Joe Leigh Simpson, shugaban bangaren fannin lafiyar mata da tsarin haihuwa da ke Kwalejin Lafiya ta Houston a kasar Amurka, yace:

“…wadannan hadisai, wato maganganun Muhammad (SAW), babu yadda za a yi a ce wani ya same su ne ta hanyar karatun kimiyya, musamman ta la’akari da tsarin ilmin kimiyyar da ke wancan lokacin da aka saukar.  Wannan shi ke nuna cewa lallai babu wata ja-in-ja tsakanin ilmin kimiyyar tsarin samar da rayuwa (Genetics) da addinin (musulunci).  Kai a takaice ma dai, addinin (musulunci) na iya zama mai bayar da kariya ta hanyar samar da bayanai (daga Ubangiji) ga wasu hanyoyin binciken kimiyya…akwai wasu bayanai daga Kur’ani da aka tabbatar da gaskiyarsu cikin daruruwan shekaru da suka gabata, masu nuna cewa lallai Kur’ani daga Allah yake.”

Wadannan, a takaice su ne abin da mai karatu ya samu a wannan mako. Idan Allah Ya kai mu mako mai zuwa, zamu kawo bangaren karshe na wadannan kasidu da muka faro, masu gwama binciken malaman kimiyyar zamani da abin da ke cikin Kur’ani don tabbatar da cewa lallai duk abin da Kur’ani ya fada, to fa gaskiya ne.  Idan bai maka daidai a cikin kwakwalwarka ba, to ka dauka kwakwalwarka ce ke da tangarda, amma ba wai abin da aka fada ba.  In kuwa za ka kwantar da hankalinka waje daya, ka kuma yi bincike, to lallai zaka samu gaskiya ne abin da aka fada.

Daga bayanan da suka gabata a sama na shedar da wadannan manyan malaman kimiyya suka bayar, muna iya fahimtar lallai akwai kalu-bale mai girma a gabanmu.  Idan har su da suke adawa da addinin da ke da wannan littafi sun samu lokacin yin bincike, ina muke, wajen yin namu binciken, don samun natsuwa da kuma karin yakini ga Ubangiji?

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.