Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (7)

Kashi na 7 cikin jerin bayanan da muke gabatar da Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani. Aci gaba da kasancewa tare da mu.

94

Hanyoyi da Dabarun Satar Bayanai (3)

Amfani da Shafukan Sada Zumunta

Kasancewar shafukan sada zumunta (Social Media) wuri ne mai kama da kasuwa, inda kowa ke zuwa ya zuba hajarsa, ya nemi abokan kasuwanci, har ya sayar musu idan suna so, yasa ‘Yan Dandatsa ke dabdalarsu a wurin.  Babu inda ake zuwa bayanai araha, a baje su ga dukkan mai bukata – cikin sani ko jahilci – irin dandalin sada zumunta.  A dandalin sada zumunta ‘Yan dandatsa kan samu bayanai ta hanyoyi hudu ne.  Ko dai bayanan da suke kyauta, wadanda a bayyane suke.  Wadannan su ake kira “Public Information.”  Idan ka rubuta sako a “Wall” dinka a Facebook misali, kowa na iya gani, ko da ba su da abota da kai.  Duk da cewa akwai inda zaka je ka kulle, sai abokanka ko kai kadai za ka ga bayanan.  Bayan sakon da ka rubuta ma, hotunanka a Facebook kowa na iya ganinsu, har ya saukar dasu idan yana da bukata.  Sunanka ma ba ka iya boyewa.  Haka lakabinka, da adireshin dake dauke da lakabin Facebook, wato: “Facebook ID.”  Har wa yau akwai yawan abokanka, da yawan hotunanka, da ranar da ka bude shafin. Duk wadannan bayanai a fili suke, kowa na iya gani muddin yana da rajista a dandalin.

Hanya ta biyu ita ce ta yin abota da mai shafin.  A nan zai samu bayanai nau’i na biyu; su ne nau’in bayanan da sai kana da abota da mutum za ka iya ganinsu har ka iya kwafansu.  Idan mai shafin ya kulle wasu bayanai daga jama’a, to, ba za ka iya ganinsu ba.  Misali, mai shafi na iya kulle sakonninsa dake “Wall”, da hotunansa; ya tsara cewa dole sai “wane” kadai daga cikin abokansa yake son ya gansu.  Idan ka fi kowa kwarewa wajen amfani da Facebook, ba za ka ga wadannan sakonni da ya killace su ba.  In ba haka ba, duk abin da ya rubuta ko ya loda a shafinsa, da duk yanayin da ya shiga, da duk wurare ko sakonnin da yayi ta’ammali dasu, da mutanen da ya karbe su a matsayin abokai, duk kana iya ganin bayanan da suka shafe su.

Sai hanya ta uku, wato ya zama ya sace shafinka kai tsaye.  Ko dai a bayyane ko a boye.  A bayyane shi ne, bayan ya kwace shafin sai ya canza Kalmar sirrinka (Password).  Dole za ka gane an kwace maka shafi, domin baza ka iya hawa ba.  A boye kuma shi ne ya gano Kalmar sirrinka ta wata hanya daga cikin hanyoyin da ake iya ganewa, ya rika hawa shafin ba tare da saninka ba.  A wannan mataki dai, ko dai na boye ko na bayyane, ya zama kai Kenan.  Duk bayanan da suka shafeka a shafin zai mallake su.  Wannan kuma zai bashi daman mallakar bayanan sauran abokanka, kai tsaye.

- Adv -

Sai hanya ta karshe, wato ya bude shafi da wani suna da aka sani, ya karbi abotar jama’a da dama.  Wannan zai bashi damar ganin bayanansu, da yin hira dasu da kuma ganin dukkan sakonnin da suke rubutawa ko lodawa a shafukansu.  Wannan daya take da hanya ta biyu da bayaninta ya gabata a sama, bambancin kawai na ga kasancewar shafin da ya mallaka don yin mu’amala dasu a matsayin abokai, ba shafi bane na hakika.  Shafin bogi ne.  Wadannan su ne hanyoyi hudu da ake iya mallakar bayanai a dandalin sada zumunta.  ‘Yan dandatsa kuma na amfani dasu sosai, fiye da kowace a Intanet, wajen tattara bayanan jama’a da manufar aiwatar da ta’addanci ga dukiyarsu ko mutuncinsu ko rayuwarsu ma gaba daya.

Saukar da Hotunan Mutane daga Intanet

Barayin Zati na amfani da hotunan mutanen da suke son sace zatinsu ne bayan sun saukar dasu daga Intanet – ya Allah ta Dandalin Sada Zumunta ne ko ta Gidajen Yanar Sadarwa na labaru da sauransu.  Misali, akwai shahararrun mutane wadanda a kullum ba a rasa hotunansu a shafukan labaru na Intanet, irin shahararrun ‘yan siyasa, da shahararrun malamai, da shugabannin siyasa, da shahararrun attajirai, da shahararrun mawaka, da shahararrun ‘yan wasa.  Duk wadannan nau’ukan mutane, mallakar hotunansu ba wahala.  Domin a kullum ‘yan jarida kan dauke su yayin da suke farautar labaru, su dora a kan shafukansu dake Intanet, don masu neman labaru su karanta.

Wani zai ce, to meye matsalar mallakar hotunan mutum kuma meye alakarsa da Satar Zati?  Amsar wannan a fili yake.  Sukan yi amfani da hotunan ne wajen bude shafi na musamman a Dandalin Sada Zumunta ko wani Gidan yanar sadarwa (Website) da sunan mai hotunan, tun da shahararre ne.  Sannan su alakanta shi da shafin, har ma da bayar da adireshin Imel da lambar waya da za a kira shi ko tuntubeshi.  Idan suka gama samun lagon jama’a, sai su aiwatar da abin da suke so cikin sauki.  Don haka, samuwar hotuna birjik a Intanet musamman a Dandalin Sada Zumunta, hanya ce daga cikin hanyoyi mafi sauki ga wadannan miyagu wajen aiwatar da tsiyatakunsu.

Amfani da Tsantsar Hasashe

Wannan shi ake kira “Guessing” a fannin kariyar bayanai.  Tsari ne da ya kunshi kokarin hararo ko gano bayanan mutum, musamman adireshin Imel da Kalmar sirri (password), ta hanyar hasashe da kirdado.  Mai yin wannan yana yunkurin hakan ne don dacewa da Kalmar sirri ko adireshin Imel din da yake daidai da naka, don samun isa ga bayananka kai tsaye, ko mallakar wata dama da kake ita a wani mahalli na kasuwanci ko mu’amala da jama’a.  Wannan hanya dai tana daga cikin tsofaffin hanyoyin da ‘yan Dandatsa ke amfani dasu wajen aiwatar da kutse, a ko ina ne.  Amma armashinta ya ragu yanzu, sanadiyyar fadakarwa da ake ta yi ga jama’a kan sababbin hanyoyin zaban Kalmar sirri da shi kanshi adireshin Imel din.  A takaice dai suna amfani da wannan hanya wajen kokarin tattaro bayanai kafin su aiwatar da abin da suke son aiwatarwa.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.