Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (8)

Kashi na 8 cikin jerin bayanan da muke gabatar da Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani. Aci gaba da kasancewa tare da mu.

95

Alamomin Dake Nuna an Sace Zatinka

Bayan bayanai gamsassu kan nau’ukan hanyoyin satar zati da suka gabata makonni hudu da suka gabata, a yau cikin dacewar Allah za mu fara bayani kan alamomin dake nuna an sace maka zatinka.  Kamar yadda na sanar a farkon wannan kasida a makonnin da suka gabata, gane cewa an sace maka zati abu ne da ba ya bayyana maka sai sadda abin ya auku.  Gano cewa an sace maka zatinka abu ne mai wahala.  Shi yasa a kasashen da suka ci gabata a fannin tattalin arzikin kasa da sadarwa na zamani, wasu kan kashe kansu da zarar sun fahimci an sace musu zati.  Dalili kuwa shi ne, muddin har aka kai lokacin da ka gane an sace zatinka ta kafafen sadarwa na zamani, hakan na nuna cewa an aikin gama ya gama kenan.  Ma’ana, duk wani nau’i na ta’annati ya gabata da sunanka kenan.  Allah tsare mu da yin mummunar gamo irin wannan, amin.

Akwai alamomi guda goma sha hudu dake nuna cewa lallai an sace wa mutum zatinsa.  Wadannan alamomi galibi sun fi faruwa ga wadanda ke kasashen da suka ci gaba.  Daga cikin wadannan alamomin da zan kawo, shida ko bakwai daga cikinsu sun fi shahara a kasashe masu tasowa, musamman Najeriya.  Don haka sai a kiyaye.

Sakon Sanarwar Cire Kudi ko Karban Bashi a Banki

Alama ta farko dake nuna an sace maka zatinka kuma ana yunkurin aikata zamba, shi ne, kawai kana zaune sai kaji sakon sanarwar cire kudi daga asusun bankinka ya shigo, wato: “Debit Alert” kenan, cewa: “Ka cire naira kaza ko dubu kaza, yanzu saura naira kaza ko dubu kaza a taskarka.”  Alhali ko hanyar bankin ma baka kama ba.  Ko kuma ka karbi sako daga banki cewa: “Bashin da ka bukata na dubu kaza, an tabbatar maka.  Nan da dan lokaci kadan za a zuba maka kudin a taskarka.”  Alhali baka bukaci wani bashi daga bankinka ba.

Batun cire kudi daga taska ba tare da masaniyar mai taskar ba, wannan hatta a Najeriya yana faruwa.  Amma na karban bashi, wannan ya fi faruwa a kasashen da suka ci gaba.  Domin a wurinsu ko ta wayar salula za ka iya tuntubar bankinka cewa kana neman bashin kudi, kuma su baka, ba dole sai ka je bankin ba.  Duk da cewa a Najeriya ma akwai bankunan dake hakan, amma bai shahara ba sosai.

- Adv -

Don haka, a duk sadda kaga sako irin wannan ya fado cikin wayarka, ba da masaniyarka ba, to, alamar wani ya sace zatinka kenan.  Abin da wannan ke nufi shi ne, ya sace wasu bayanan dake da alaka da taskarka na banki.  Ko dai katin ATM dinka, ko suna (username) da kalmar sirrin (password) hawa shafin taskar bankinka ko wani abu makamancin hakan.  A wannan yanayi, wajibi ne ka yunkura don tuntubar bankinka da sanar dasu halin da ake ciki.  Za su yi bincike, a nasu bangaren, kuma kaima za su maka tambayoyi.   Muddin suka gano cewa matsalar daga gareka ne, to, ba abin da zasu iya yi.  Sai dai kayi hakuri a kori gaba.  Amma dole ne ka jajirce, muddin kana da tabbacin ba daga bangarenka aka samu matsala ba, domin su za su dage ne cewa basu san komai kan haka ba, musamman idan kudade ne masu yawa.

Alamar Samuwar Matsala a Taskarka

Akwai hukumomin gwamnati masu lura da taskokin bankunan jama’a a galibin kasashe.  A Najeriya misali muna da hukumar EFCC.  Wadannan hukumomi suna da alaka mai karfi tsakaninsu da bankuna, musamman alakar musayar bayanai.  Akwai iya kadadar kima ko adadin kudade da idan za a cire ko za a sa a cikin wata taska, sai bankuna sun sanar da wadannan hukumomi ta hanyar basu bayanan nau’in tasarrafin da akayi a taskar.  Da ranar, da adadin kudin, da bayanan mai taskar, da kuma wanda ya aiwatar da tasarrafin.  Duk sadda aka samu adadin kudin ya wuce abin da doka ta tanada, to, kai tsaye ake tuntubar mai taskar.  To a wasu lokuta yan ta’adda kan saci bayanan mutane na banki, don su aiwatar da wasu nau’ukan tasarrafin kudi a ciki, musamman kazaman kudade.  Idan aka samu matsala, hukuma za ta nemi mai taskar ne kai tsaye.

Don haka, duk sadda ka samu sako daga wata hukumar lura da hada-hadar kudaden haram, cewa ga wani nau’in tasarrafi anyi a taskarka, alhali kai baka ma san dashi ba.  To alamar an sace maka zatinka kenan ta wannan fanni.  Wajibi ne ka natsu, ka fuskanci tambayoyin da ake maka, ka kuma basu dukkan bayanan da suka bukata.  Idan sace maka katinka na ATM aka yi misali a wani lokaci da ya gabata, ka nuna musu takardar sheda da hukumar ‘yan sanda suka baka, da takardar shedar kotu.  Wadannan su ne zasu taimaka wajen tserar dakai, cewa lallai akwai tabbacin wadanda suka sace ne suka aiwatar da wannan ta’annati.  Wannan ita ce alama ta biyu.

Samuwar Katin ATM Din Da Baka Bukata Ba

Alama ta uku ita ce, kana zaune sai kawai kaji kira daga banki ko sakon sanarwa daga banki ya shigo wayarka cewa: “Katin ATM da ka bukata fa ya fito.  Kana iya zuwa banki ka karba.”  Alhali baka bukaci sakon katin ATM ba.  Kuma wanda kake amfani dashi lokacinshi bai kusa karewa ba.  Idan kaga hakan, to, wani bakon haure yana yunkurin sace maka taskar bankinka kenan.  Ta yiwu ya yi amfani da wata dabara a bankin, ya bukaci sakon katin, ta hanyar sanar dasu cewa an sace wanda kake amfani dashi.  Amma ya mance bai bayar da lambar wayarsa ba.  Da yayi amfani da dabaru wajen sauya lambar wayarka, kuma aka amince a bankin ba tare da saninsu ba, da sadda sanon katin ya samu ma, ba za ka sani ba.  Sai dai kawai kaga wanda kake amfani dashi ya tsaya, nan tare.  Domin da zarar an samar da sabo, to, za a goge wanda ke kan taskar ne.

Da zarar ka ga haka, sai ka garzaya bankinka ka sanar dasu, tare da nuna cewa kai fa baka bukaci wani sabon kati ba.  Domin wanda kake amfani dashi lokacinsa bai kare ba, sannan yana nan a hannunka, ba abin da ya same shi.  Dole ne suyi bincike su tabbatar da wanda ya bukaci a bashi sabon katin ta amfani da taskarka.  Domin wannan matsalar ba kanka kadai za ta tsaya ba, a a, alama ce dake nuna cewa tsarin bankin na da matsala wajen iya tantance masu hulda dashi.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.