Hanyoyin Kwarewa a Fannin Fasahar Sadarwa (1)

Daga wannan mako in Allah Yaso, za mu fara fadakar da masu karatu kan fannonin da mutum zai iya kwarewa a kai cikin fannin kimiyyar fasahar sadarwa na zamani, wato “Information Communications Technology.” Kasidar yau dai gabatarwa ce. A sha karatu lafiya.

778

Gabatarwa

Bayan zama don waiwaye a makon da ya gabata, a yau za mu bude wani sabon shafi, don canza salon tafiya cikin abin da ya shafi wannan ilimi na fasahar sadarwa na zamani.  Idan mai karatu bai manta ba, a wancan kasida ta “Waiwaye Adon Tafiya” ne muka yi alkawarin fara kawo kasidu kan hanyoyin kwarewa kan fasahar sadarwa; wato yadda za a yi mai karatu ya samu wani fanni don kwarewa a cikinsa, in ma ta kama ka rike wannan fanni a matsayin sana’a.  Wannan zango da muka faro a halin yanzu zai yi tsawo; za mu kawo kasidu nau’i daban-daban har guda goma sha biyu, don yin bayani kan wadannan hanyoyi da kuma fannonin da ke cikin wannan bangare mai tashe a wannan zamani.

Kafin mu yi nisa, zan so mai karatu ya fahimci cewa kwarewa kan duk abin da ka samu kan ka kana mai yi a kullum, yana da muhimmanci, don baka san inda zai dangana da kai ba.  Duk da yake galibi mun fara karanta wannan shafi ne don sha’awa, a tabbace yake yanzu cewa da dama cikin mu mun fahimci muhimmancin wannan fanni har mun fara koyon kwamfuta.  Na samu sakonnin masu karatu da dama da ke sanar dani cewa sanadiyyar wadannan kasidu da suke karantawa, sun wayi gari suna masu sha’awan wannan fanni, kuma ma har makarantar kwamfuta suka shiga.  Wasu kuma suna rubutowa ko bugowa don neman shawara kan fannin da yafi dacewa su kware a kai.  In haka ne, ashe wannan ke nuna tasirin abin da ake karantawa a wannan shafi mai albarka.

Wannan yasa na ga cewa, tunda har an kai ga shiga makaranta don koyon kwamfuta, to ashe akwai watakilancin wata rana ana iya daukan wannan fanni a matsayin haryar tafiyar da rayuwa ko dogaro.  Wannan zai tilasta wa dukkan wanda ya dauki wannan hanya a matsayin rayuwa irin ta sana’a, ya kware kan abin da yake yi, don inganta aikinsa.

Har wa yau, kowa da irin fannin da yafi bashi sha’awa; wani yafi son yaji ana Magana kan tsara Mudawwana (Blog), wani kuma kan Gidajen Yanar Sadarwa (Websites), wani kan Hanyar Wasikar Sadarwa wato Imel (Email), wani shi ba abin da yake so illa ya kware kan hanyar Gina Gidan Yanar Sadarwa (Web Design), wani kuma abin da ya shafi wayar salula da karikitanta, da dai sauransu.  To ko ma dai mene ne, ba abin da zai sa ka kware sai in ka dauki hanyar da kafi sha’awa kuma ka mayar da hankali a kai.

Tabbas, bamu taru mun zama daya ba.  Wannan na daga cikin hikimar halitta da Allah Yai amfani da ita.  Da ace an wayi gari dukkan mutane sun ginu a kan iyawa ko kwarewa ne kan abu daya, to babu wata hikima wajen halittar mu launi-launi ko jinsi-jinsi.  In kuwa haka ne, ashe duk wani dan Adam Allah Ya mallaka masa wata baiwa wacce ba lalai bane ya zama wani na da ita.  Wannan tasa ayyukanmu suka banban ta.

- Adv -

A yau za mu yi mukaddima kan shahararrun nau’ukan fannonin da mai karatu zai iya kwarewa a kan su, musamman a wannan kasa tamu Nijeriya.  Hakan na da muhimmanci musamman ganin cewa kwararru a wannan fanni sun yi karanci a Arewacin Nijeriya, idan aka kwatanta yawan kwararrun da ake dasu a Kudancin wannan kasa tamu.  Bayan nan, za mu karkare bayani da kawo hanyoyin da za su iya sawwake mana kwarewa kan kowane irin fanni muka zaba.

Nau’ukan Fannin Fasahar Sadarwa

Yana da kyau mai karatu ya san shahararru cikin wadannan fannoni, a takaice.  A kasidun gaba za mu rinka daukan su daya bayan daya, muna bayani filla-filla don samun gamsuwa.  Da zaran mun kawo karshen wannan zango, ina da tabbacin mai karatu zai samu madafa, ko da kuwa na sha’awan wani fanni ne.  Idan ma ya kasa tsayawa a sha’awa kadai, yana iya mayar da kwarewarsa ta zama sana’a, wacce zai rinka cin tuwo da ita.  A wasu kasashe tuni wasu suka yi kudi kan haka.  Cikin shahararrun fannonin akwai gamammen ilimin kwamfuta da manhajojinta da kuma alakar ta da sauran hanyoyin sadarwa, wato ilimin da a Turance ake kira Computer Science & Education.  Galibi akan yi digiri ne akai, wanda hakan ke samuwa daga jami’a.  Idan mutum ya ga dama, yana iya ci gaba don yin digirgir, ya zama kwararre kan wani fanni da bayaninsa zai zo nan gaba.  Haka kana iya zama mai karantarwa a wannan fanni, ko ka ma hada dukkan biyun.

Sai fannin Desktop Publishing, wato fannin da ya kunshi kwarewa kan iya sarrafa manhajar kwamfuta wajen rubutu da zane da buga littafai ko abin da ya danganci hakan.  Galibi za ka samu masu wannan kwarewa sun bude shago ne, sun zuba kwamfutoci, ana aikin bugawa da dabba’a bayanai, da kuma sawwara su.  Wannan sana’a ce mai matukar muhimmanci, wacce bata bukatar sai ka samu digiri kafin ka shige ta.

Sai fannin Database Administration, wato bangaren ilimin adanawa da kuma taskance bayanai a kwamfuta, shima yana da kyau.  Sai kuma Programming, wanda tuni muka sha bayani a kanshi.  Wannan shi ne ilimin ginawa da kuma tsara manhajojin kwamfuta.  Masu wannan ilimi su suke busa ma kwamfuta da karikitanta rai, har ta fara motsi.  Sai danginsu, wato Software Engineers.  Wannan fanni kusan daya yake da wanda ya gabace shi, babancin su kadan ne.  A fannin Software Engineering, za ka gina manhaja ne, ka tsara shi, ka gwada shi ka rubuta dukkan bayanan suka dangance shi, sannan ka tallata shi.  Dankari!  Sai kuma System/Hardware Maintenance, wato fannin da ke lura da gyaran kwamfuta.  Kamar dai yadda muke da masu gyaran rediyo da talabijin.  Sai kuma Web Design & Maintenance.  Wannan fanni ya kunshi gina gidan yanar sadarwa ne da kuma lura dashi.  Shi ma sana’a ne mai kyau da martaba.

Na gaba shi ne Network Administration, wato ilimin hada alaka tsakanin kwamfuta da ‘yar uwanta, da kuma lura da duk abin da zai iya yanke wannan alaka.  Sai bangaren E-commerce, wanda ya kunshi saye da sayarwa ta hanyar Intanet ko ta amfani da duk wani hanya da ya shafi kayan fasahar sadarwa na zamani.  Idan muka cilla gaba kuma za mu samu Kwararru kan rubutu a fannin fasahar sadarwa.  Wannan fanni na da muhimmanci, don da bazan wadannan kwararru ne kowane fanni na ilimi ke takama.  Za ka iya zama marubuci kan fasahar sadarwa har abada.  A kasidar karshe za mu samu bayanai kan kwarewa a fannin Phone Repairs and Maintenance.  Wannan fanni tuni wasu suka yi tashe a cikin sa.  Ya kuma kunshi kwarewa ne kan gyarawa da kuma lura da wayoyin salula, a kanikance.

Dukkan wadannan fannoni na da muhimmanci musamman a wannan zamani da muke ciki na yaduwar su.  Babu wanda zai kallafa maka kwarewa a kan dukkan su a lokaci guda.  Amma za ka iya kwarewa a kan a kalla daya daga cikinsu.  To me zai iya taimaka maka wajen yin hakan?

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. MURYAR HAUSA24 ONLINE MEDIA says

    MASHA ALLAH

Leave A Reply

Your email address will not be published.