Kimiyyar Kur’ani Da Ta Zamani: A Ina Aka Hadu? (2)

Wannan shi ne kashi na biyu cikin jerin kasidun da muke bincike na musamman kan alakar dake tsakanin kimiyyar Kur’ani da ta Zamani. A sha karatu lafiya.

569

HALITTAR DUNIYA 

———————————————

Binciken Kimiyyar Zamani

Abu na farko da Malaman kimiyyar sararin samaniya (Astronomers ko Astrophysicists) suka binciko dangane da asalin duniya baki dayanta, ba wacce muke rayuwa cikinta ba kadai, shi ne asali a cure take wuri daya; komai a dunkule.  Ma’ana asalin duniya wani curi ne na jiki mulmulalle, ko kuma Sadima, (kamar yadda Farfesa Muhammad Hambali Jinju ya kira shi) wato Primary Nebula kenan a TuranceSai wannan curi ya fashe, ya kuma tarwatse, wato matakin Secondary Separation kenanHakan ya haifar da samuwar kura mai tattare da iska mai dimbin yawa, wato Gaseous Mass.  Wannan tarwatsewar ce ta haifar da samuwar dukkan halittun da ke duniyar, daga wannan duniyar da muke ciki, zuwa wata, da rana da taurari da sauran duniyoyin da muka sansu a yanzu, da ma wadanda Allah kadai ya sansu.  Wannan nau’in fahimta shi ake kira The Big Bang Theory, a Ilimin Sararin Samaniya.

An fara wannan bincike ne shekaru kusan dari hudu da suka gabata, kuma ya zuwa yau, an dada tabbatar da kasancewar hakan a ilimin sararin samaniya ta hanyar amfani da na’urorin hangen nesa da sauran hanyoyi.  Malaman kimiyyar sararin samaniya suka ce wadannan matakai guda biyu da suka samar da duniya da sauran halittun da ke cikinta, sun faru ne cikin biliyoyin shekaru!

Duk da cewa Malamai masu bincike sun dade da yin hasashe kan asalin wannan duniya tamu tun shekaru dari bakwai da suka gabata, babu wanda ya samu dacewa wajen hararo mafi kusancin abin da ke nuna hakan, ya kuma samar da ka’idar Big Bang, sai Immanuel Kant dan kasar Jamus, wanda ya rayu tsakanin shekarun 1724–1804.  A lokacin babu wanda ya kawo hankalinsa ga wannan bincike nashi sai bayan rasuwarsa da shekaru hamsin da hudu, lokacin da wani masani mai suna Pierre-Simon yayi Karin bayai; inda ya kara fito da abin fili kowa ya fahimce shi sosai.  Wannan abu ya faru ne cikin karni na shabakwai (17th Century), wato shekaru dubu daya da dari biyu kenan bayan saukar Al-Kur’ani mai girma.  Idan kuma muka yi la’akari da wannan ka’ida, za mu ga cewa tana ishara ne zuwa ga abubuwa uku, a takaice.  Abu na farko shi ne samuwar wani curin jiki, wato Big Bang, kamar yadda bayani ya gabata.  Sai kuma fashewa da wannan curi yayi, aka samu kura mai dauke da iska mai nauyi, wato Gaseous Mass.  Bayan nan kuma, sai aka samu gungun taurari wadanda suka tattarwatse don samar da taurari da rana da wata da kuma sauran duniyoyin da ke nan a yau (wadanda muka sani da wadanda bamu sansu ba).

A cikin littafinsa mai suna The Story of the Solar System, Mark A. Garlick, yayi dogon bayani da sharhi kan tsawon wannan lokaci, da kuma cewa ba wai wadannan duniyoyi da ake ta bayani kan su guda tara kadai ba, akwai bayanai sabbi da ke nuna cewa akwai wasu duniyoyin ma samammu, wadanda har yanzu hangen mai hangen nesa bai kai kansu ko ba.  A karshe dai, kamar sauran Malaman Kimiyyar sararin samaniya, Mark yace wannan tsari na halittar duniya ya faru ne “siddan”, wato “haka kawai”, ba tare da cewa akwai wani wanda ya haddasa hakan ba.  A takaice dai, “tsawon zamani ne ya samar da su, kuma hakan ne zai yi ajalinsu.”  Wannan tunani nashi ya samu ne sanadiyyar akidarsa ta rashin yarda da cewa Allah ne mai halittar komai da kowa.  Don haka kada mai karatu yayi wani mamaki.

A nata bangaren ita ma, mujallar Scientific American bugu na 14 lamba ta 4, wacce ta fito a shekarar 2004, tayi tsokaci na musamman kan taurari.  Wannan tsokaci da tayi shi, ta sanya masa take: The Secret Lives of Stars.  A ciki ta kawo kasidu da makaloli masu dimbin alfanu, masu nuna tsarin shekarun taurari, da yanayin girmansu, da kuma cewa bayan wannan babbar fashewa da curarriyar halittar duniya tayi a farko, sai da aka samu shekaru sama da miliyan dari kafin taurari suka fara bayyana don samar da haske.  Mujallar ta kuma tabbatar da cewa akwai bambancin girma da kuma tsawon zamani tsakanin taurarin farko da wadanda ke rayuwa yanzu.  Taurarin farko, a cewar mujallar, suna da girma sosai, inda ta tabbatar da cewa wasunsu ma sun fi rana girma a farkon al’amari, kuma a nesa suke damu; nesa ba kusa ba.  Wadannan bayanai dai sun same su ne ta hanyar ingantattun na’urorin hangen nesa na zamani, da kuma kwararan ka’idojin lissafi masu bayar da sakamako ingantacce kan tsarin abubuwa, wadanda ake iya shirya su ta hanyar kwamfuta a yau, wato Computer Simulation Models.  To me Kur’ani yace kan haka?

Tabbaci daga Kur’ani

Da farko dai, sabanin yadda masu wadancan bincike suka tabbatar cewa babu wanda ya kaddara samuwar wadannan halittu na sama da kasa da taurari da rana da wata sai tsawon zamani, a Al-Kur’ani Allah ya sanar damu cewa shi ne ya yi wannan aiki.  Ya kuma ce ya halicci sammai da kasa ne cikin kwanaki shida.  Ga abin da yace:

“Kuma lallai ne hakika, mun halitta sammai da kasa da abin da ke a tsakaninsu ne, a cikin kwanaki shida, alhali wata ‘yar wahala bata shafe mu ba.” (Qaaf: 38)

Duk da haka, akwai kamshin gaskiya cikin wancan bincike da malaman sararin samaniya suka yi ko suka hango dangane da cewa asalin duniya gaba daya a dunkule take curi guda.  Sai dai sabanin takaitaccen bayanin da suka bamu cikin dan binciken da suka yi, akwai rashin yalwar bayani kan yadda al’amuran suka faru.  Watakila da Musulmai ne su, da sun samu isasshen bayani mai gamsarwa a cikin Kur’ani a yayin da suke wancan bincike.  Duk da yake na san ba iyakan binciken ba kenan, suna nan suna ta yi, kamar yadda Mark Garlick ya fada cikin littafinsa.  A cikin Kur’ani Allah ya yalwata mana bayani kan abin da ya shafi halittar duniya gaba daya da abin da ke cikinta.  Da farko yace asalin duniyar a dinke take, ko a cure kamar yadda suka fada, sannan sai ya bude ta, ya karkasa halittanta. Ga abin da yace:

“Shin wadanda suka kafirta basu gani ba cewa, lallai sammai da kasa sun kasance dinke ne (da juna), sai muka bude su…?” (Ambiya’:30)

Malaman tafsirin Kur’ani sun kawo fassara nau’i biyu kan wannan aya, kuma duk ma’ana daya suke nufi.  Al-Imam Ibn Kasir a cikin tafsirinsa yace: “…ai dukkansu (wato sama da kasa) sun kasance a hade ne da juna; sashe da sashe, a cakude da juna, wani a kan wani, a farkon lamari.  Sai Allah Ya bude wannan daga wannan.  Ya sanya sammai guda bakwai, da kuma kasa guda bakwai.  Ya kuma raba tsakaninsu da iska (wadda ke shawagi a tsakani kenan).  Sai sama ta zubar ruwa, kasa kuma ta fitar da tsirrai.”  Bayan shi, Sheikh Abubakar Jaabir Al-Jazaa’iri shima cikin tafsirinsa ya tafi kan wannan fassara, ya kuma kara da cewa kasancewar sama da kasa na dinke a farko, har wa yau na nufin sama bata zubar da ruwa ne, haka kasa ma bata fitar da tsirrai;  ma’ana a kekashe suke saboda hadewa da juna da suka yi a farkon lamari.  Ga abin da yace:

- Adv -

“…abin nufi shi ne, lallai sammai da kasa abu ne guda daya (a farko), a hade da juna, sai Allah Ya raba tsakaninsu.  Kuma abin da ya kumshi tafsirin wannan aya na ishara zuwa ga ra’ayin Ibn Jareer At-Tabari, na cewa: lallai sama ta kasance ne a shafe – ko a kulle – ba ta saukar da ruwa, haka ma kasa, a kulle take, ba ta fitar da tsirrai.  Ayar na nuni ne ga wadannan fuskoki guda biyu.  Kuma dukkansu ingantattu ne.” 

Wannan fassara har wa yau shi ne ra’ayin Abdullahi dan Abbass, da almajiransa irinsu Mujaahid, da Sa’id bn Jubair, da kuma Al-Hassan Al-basari.

Abu na biyu da malaman kimiyyar sararin samaniya suka tabbatar bayan tarwatsewar wannan duniya ko fashewarta a farko (abin da suka kira Secondary Separation), shi ne  samuwar wata iska mai tattare da kura mai nauyi, wato Gaseous Mass, kamar yadda bayani ya gabata.  A cewarsu, bayan samuwar wannan iska mai kura ne aka samu karkasuwar gungun taurari, wato Galaxies, wadanda a karshe su kuma suka barbaje don samar da duniyoyi dabam-daban da rana da wata da kuma taurari masu matukar girma.  Don haka idan mun fahimce su sosai, abin da wannan ke nufi shi ne, bayan fashewar (ko budewa, kamar yadda Kur’ani ya kira shi), wannan iska mai kura ne ta biyo baya kafin samar da sauran jikinnai (irinsu wata da rana da manyan taurari da kananansu da kuma wannan duniya tamu da sauran makwabtanta).

Amma a Kur’ani Allah Ya sanar damu ne cewa bayan budewar ko fashewar, ya fara halittar kasa ne a dunkule, ya barta haka, sannan ya nufaci sama don tsara halittarta gaba daya.  A karshe kuma ya samar da dukkan ababen da ke kan kasa, irinsu koramu da duwatsu da tsaunuka, da kuma sauran ababen da ke cikinta gaba daya.  Mu bi abin dalla-dalla.  Za mu fahimci lamarin sosai, da inda suka yi daidai da kuma inda ya rage basu gano tsarin ba.  A bincikensu dai basu sanar damu ina aka fara halitta ba. Amma Kur’ani ya sanar damu cewa kasa aka fara halitta, domin ita ce ginshiki, kuma shimfida, sannan aka bibiye ta da rufin da ke samanta, shi ne sammai bakwai da abin da ke cikinsu.  Ga abin da Allah Yace:

“Shi ne wanda ya halitta muku abin da ke cikin kasa gaba daya, sannan ya daidaita zuwa sama, ya daidaita (aikata) su sammai bakwai.  Kuma shi masani ne ga dukkan komai” (Bakara: 29)

Wannan ke nuna mana cewa kasa Allah Ya fara halitta, amma har yanzu Malaman Kimiyyar sararin samaniya basu gano hakan ko ba.  Har wa yau, basu sanar damu ko cikin kwanaki nawa wannan fashewa da kuma karkasuwar halittun sama suka faru ba.  Duk da yake suna ambaton miliyoyin shekaru wajen samuwar taurari, da wasu shekaru wajen samuwar wata da rana da sauransu, wannan baya nufin lokacin da fashewar ta faru ne zuwa lokacin halittarsu kai tsaye.  Suna kimanta shekarunsu ne daga lokacin samuwarsu ko wasu daga cikinsu, zuwa wannan lokaci da muke ciki, kamar yadda mujallar Scientific American ta nuna cikin wancan bugu na musamman da tayi kan rayuwar taurari da yadda alaka ke kasancewa a tsakaninsu.  To amma a Kur’ani Allah Ya sanar damu cewa ya halicci sama da kasa da abin da ke cikin su ne cikin kwanaki shida.  Bayan fashewa ko bude duniya da yayi kamar yadda muka karanta a ayar da ke sama a suratul Ambiya’, sai ya halicci kasar da muke takawa ko rayuwa a kanta cikin kwanaki biyu (daga ranar Lahadi zuwa Litinin), ya barta haka.  Sai ya nufi sama, ita kuma ya halitta ta da abin da ke cikinta cikin kwanaki  biyu (daga Talata zuwa Laraba), sannan ya dawo kan kasa, ya baje ta, ta hanyar samar da dukkan kayayyakin cikinta (don a farko halittar ta kawai yayi), cikin kwanaki biyu (daga Alhamis zuwa Jumma’a).  Ga abin da yace:

“Kace, “ashe lalle ku hakika kuna kafirta a game da wanda ya halitta kasa a cikin kwanuka biyu, kuma kuna sanya masa kishiyoyi?” Wancan fa, shi ne Ubangijin halittu.  Kuma Ya sanya a cikinta, duwatsu kafaffu daga samanta, kuma Ya sanya albarka a cikinta, Ya kaddara abubuwan cinta a cikinta, a cikin kwanuka hudu masu daidaita, domin matambaya.” (Fussilat: 9-10).

A bayyane yake cikin wadannan ayoyi biyu cewa an halicci kasa da abin da ke ciki da karkashinta ne cikin kwanaki hudu, a jumlace kenan.  Amma ba lokaci daya bane hakan ya kasance, kamar yadda Allah da kanshi ya fada a cikin wata surar:

“Shin ku ne mafi wuyar halitta ko sama?  Allah ya gina ta.  Ya daukaka rufinta, sannan  ya daidaita ta.  Kuma ya duhuntar da darenta, kuma ya fitar da hantsinta.  Kuma kasa, a bayan haka Ya shimfide ta, ya fitar da ruwan ta daga gareta da wurin makiyayarta, da duwatsu, ya kafe ta, don jin dadi gareku da kuma dabbobinku.”   (Naazi’aat: 27-33)

Kalmar Dahaaha da Allah Yayi amfani da ita na nufin tsarin samar da amfanin cikinta.  Kamar yadda muka karanta a wadannan ayoyi da ke sama.  Kuma hakan ya faru ne bayan samar da sammai bakwai, kamar yadda ayar tayi ishara (don yace “kuma kasa, a bayan haka…”, ma’ana bayan halittar sama kenan).  Idan muka dauki kwanaki biyu na halittar kasa, da kuma kwanaki biyu na samar da abin da ke cikinta, sai mu ga cewa su ne kwanakin hudun da Allah ya fada a surar Fussilat da muka fara kawowa a sama.

To kafin mu zarce zuwa sama, masu binciken kimiyyar sararin samaniya suka ce akwai wata iska mai dauke da kura mai nauyi, wato Gaseous Mass da ta samu bayan fashewar duniya.  Shin Kur’ani ya ambata mana ko yi mana ishara kan wannan iska mai kura da suka kawo kuwa?  Eh, ya kawo mana.  Sai dai sabanin yadda suka siffata abin da “iska mai kura”, Kur’ani ya nuna mana cewa hayaki ne ko tururi, wanda ya samu sanadiyyar halittar kasa da Allah Yayi, kamar yadda Ibn Kasir ya fada cikin tafsirinsa.  Mu koma suratu Fussilat, inda Allah yaci gaba da cewa:

“…Sannan ya daidaita zuwa ga sama, alhali kuwa ita (a lokacin) hayaki ce, sai yace mata, ita da kasa, “Ku zo, bisa ga yarda ko a kan tilas.”  Suka ce “Mun zo, muna masu da’a.”  Sai ya hukunta su sammai bakwai a cikin kwanuka biyu.  Kuma Ya yi wahayi, a cikin kowace sama da al’amarinta, kuma Muka kawata sama ta kusa da fitilu kuma  don tsari.  Wancan kaddarawar Mabuwayi ne, Masani.”  (Fussilat: 11-12) 

A yanzu na tabbata mai karatu ya fahimci yadda lamarin yake.  Cewa da suka yi, asalin duniya a cure take, ko a hade da juna, daga baya suka rabe, gaskiya ne, kamar yadda muka gani.  Cewa da suka yi, bayan fashewar ko rabewar, an samu “iska mai kura” kafin halittar sauran duniyoyi da taurari, ba haka bane dari bisa dari; an dai halicci kasa, sannan aka samu hayaki ko tururi a sama, kafin aka halicci sammai bakwai da dukkan ababen da ke cikinta na taurari da rana da wata da dare da yini da sauransu.  Wannan shi ne abin da Kur’ani ya tabbatar, da kuma Karin bayani kan abin da bincikensu bai kai ba.  In dai aka juri zuwa rafi, wata ran za a samu ruwa.  Domin cikin shekarun baya ne aka samu wani bincike mai tabbatar da cewa lallai alamun da ke jikin wata a halin yanzu na nuna cewa lallai ya taba tsagewa.  Mu kam tuni Kur’ani ya sanar damu haka tun shekaru dubu daya da dari hudu da suka gabata.

A dakace mu!

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    ALLAHU AKBAR!

    ALLAH YA KARA MANA KARFIN IMANI AMIN.

  2. Musbahu says

    Allah ya Karo basira

Leave A Reply

Your email address will not be published.