Sakonnin Masu Karatu (2016) (19)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

92

Assalamu alaikum Baban Sadik, don Allah ka turo mini bayanai dangane da hanyoyin da zan fara koyon ilimin kwamfuta don in iya sosai. Danmoyi Hassan: danmoyihassan@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai.  Ka duba akwatin Imel dinka, na aiko maka shawarwarin da na baiwa wasu daga cikin masu karatu kan abin da kake bukata.  Allah sa a dace, ya kuma mana jagora cikin lamuranmu baki daya, amin.


Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da aiki. Da gaske ne sautin wayar salula a kunne a lokacin kira na jawo cutar daji (Cancer)? Haka kuma kankare katin cajin wayar salula da hannu an ce shi ma na kawota? Nasiru Kainuwa Hadejia: 08100229688

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Nasiru.  Wannan zance an sha maimaita shi, haka ma jama’a sun sha mini tambaya kan wannan al’amari shekaru kusan biyar da suka gabata, kuma amsar da nake basu dai ita ce zan baka: cewa har yanzu babu wani ingantaccen bincike na kimiyya, kuma amintacce, wanda ke nuna yawan amfani da wayar salula na haddasa cutar sankara, wato “Cancer” kenan.  Wannan jita-jita ce da kuma dari-dari da wasu ke yi sanadiyyar sinadaran maganadisun lanatarkin sadarwa (Radio Frequency Electromagnetic Radiation) dake fita daga wayar a yayin da mai waya yake yin waya.  Galibin masu yada wannan jita-jita ko yawan damuwa da wannan lamari na kafa hujja ne da wannan sinadari, wanda suka ce bincike ya nuna cewa zai iya haddasa wannan cuta.  Damuwar ta karu sosai cikin shekarar 2011, sadda Hukumar Bincike kan Cutar Sankara ta Duniya (International Agency for Research on Cancer) ta nuna cewa akwai alamun nan gaba wannan sinadari na iya haddasa wannan cuta.

Don samun karin tabbaci, na tuntubi shafin Hukumar dake Lura da Yaduwar Cutar Sankara a kasar Birtaniya, wato: “Cancer Research, UK”.  A cikin bayanan da ta sabunta a shafinta dake: www.cancerresearchuk.org, a ranar 20 ga watan Oktoba na shekarar 2016, ta nuna cewa wannan zance har yanzu babu kamshin gaskiya a cikinsa.  Domin dukkan binciken da aka gabatar a baya masu nuna wata alaka da wannan cuta basu cika sharuddan binciken kimiyya nagartacce da za a iya gina hukunci a kansa ba.  Hukumar tace hatta rahoton da hukumar binciken cutar sankara ta duniya ta fitar a shekarar 2011 bai da nagartar da za a iya dogaro dashi.  Wanda shi yasa ma hukumar ita kanta tace ta sanya wayar salula ne cikin jerin na’urorin da take “lura dasu” don ganin ko wannan sinadari na iya tasiri wajen haddasa wannan cuta.  In kuwa haka ne, ashe babu cikakken tabbaci kenan.

Ba wannan wayar salula kadai ba, hatta na’urar yada siginar Intanet, wato: “WiFi”, da na’urar wutar lantarki na zamani, wato: “Digital Meter,” ana tuhumar suna iya zama sanadi.  Sai dai a shekarar 2012 an sake gudanar da wani bincike wanda ya tabbatar da cewa babu sila, ko alaka na sisin kwabo tsakanin sinadarin da wadannan na’urori ke fitarwa da wannan cuta.  Wannan har wa yau shi ne bayanin da Cibiyar Lura da Cutar Sankara ta kasar Amurka, wato: “National Cancer Institute” ta fitar a shafinka.  Babban dalili shi ne, wannan sinadari da wayoyin salula da sauran na’urorin sadarwa ke fitar ba ya furzar da sinadarin ayon (ion), ba wannan kadai ba, babu sinadarin ayon ma tare dashi.  Amma sinadarin maganadisun lantarkin sadarwa mai fitar da sinadarin ayon (ion) ne ke haddasa cutar sankara.  Don haka, tunda wannan sinadari ba ya dauke da ayon a cikinsa, kenan ba shi bane ke haddasa wannan cuta.

Hukumar Lura da Cutar Sankara ta kasar Birtaniya taci gaba da cewa, ya zuwa yanzu dai babu wani abin dogaro dake tabbatar da wannan zargi, sai ma akasinsa.  Domin, a cewarta, in da gaske ne wannan sinadari na sanadin kamuwa da cutar sankara, a kalla an kwashe shekaru kusan 30 ana amfani da wannan na’urar sadarwa ta wayar salula a kasar Ingila, misali, amma tsawon wannan lokaci, yawan masu cutar sankara bai karu ba.  Da a ce wannan na’ura na haddasa wannan cuta, da ya kamata a ce a duk shekara ana samun karuwar masu kamuwa da cutar fiye da kima, musamman ta la’akari da yawan masu mu’amala da wayar salula a kasar baki daya.  Amma hakan bai kasance.   Ba ma a kasar ba kadai, a duk fadin duniya har yanzu ba a samu wani mutum guda daya da ya taba kamuwa da cutar sankara sanadiyyar yawan amfani da wayar salula ba.

A karshe dai, abin da hukumar ta karkare bayani dashi dai shi ne, idan ma wannan sinadari na haddasa wannan cuta, to, ta yiwu sai bayan lokaci mai tsawon gaske, wanda babu wani bincike na kimiyyar zamanin yau da zai iya hasashen tsawon lokacin da za a iya kamuwa da cutar sanadiyyar amfani da wannan na’ura.  Da fatan ka gamsu.


- Adv -

Salaamun Alaikum Baban Sadik, don Allah ina so kayi mini bayani game da na’urar “Tablet PC”. Wato na mallaki na’urar Samsung Galaxy Note 10.1 2014 Edition, kuma ina jin dadin mu’amala da ita sosai, kuma har sau biyu ina mata karin tagomashi. Na karshen shi ne nau’in Android mai suna: Lollipop 5.1.1, yanzu kuma na ji ina matukar sha’awar Marshmallow ko kuma Nougat, na san zaiyi wahala na sake samun wasu bayanan karin tagomashi daga kamfanin kai tsaye (Over the air update). Shin zai yiwu in samu nau’in Marshmallow ko Nougat ta hanyar flashing ko “Custom ROM”? Idan zai yiwu don Allah kayi min bayani yadda ake yi ko kuma wajen wanda zanje yayi min. Sannan kuma idan da hali kayi min karin haske game da REMIX OS. Na gode: salisuabubakar52@yahoo.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Salisu.  Tabbas akwai “Custom ROM” da zai dace da Tab dinka, kuma nau’in Android Mashmallow.  Don haka, zan tura maka shafin da za ka iya sauke shi kyauta, sannan da shafukan da za ka samu karin bayani kan dora ta a kan Tab dinka.  Amma dangane da ko akwai wanda na sani da zai iya maka wannan aiki, ina iya cewa a a.  Sai dai daga yanayin bayaninka na fahimci kana da sanayya kan wadannan abubuwa.  Don haka gwamma in aika maka bayanan don ka gwada yi da kanka.  Zan kuma tura maka wancan bayani da nayi kwanakin baya na yadda ake filashin wayar salula.  Wannan zai sawwake maka abubuwa da dama.

Ta bangaren “Remix OS” kuma, nau’i ne daga cikin nau’ukan babbar manhajar kwamfuta (Operating System) da ake iya dora wa kwamfuta, amma nau’in Android ce.  Tsarinta daya da babbar manhajar Android dake wayarka ta salula ko Tab.  Amma ita nau’in Mashmallow ce, wato: “Android 6” kenan.  Kyauta ake saukar da ita, a kuma dora wa kwamfuta. Wannan babbar manhaja tana da inganci matuka, sannan babu saibi ko nawa tare da ita.  Cikin sauri take kunnuwa, haka ma idan ka kashe ta.  Wani abin sha’awa har wa yau shi ne, idan kana da tsohuwar kwamfuta wacce aka kera ta da jimawa, kana iya saukar da wannan babbar manhaja ta Remix, ka dora mata.  Garau za ta mike, kamar sabuwa.

Sannan kana iya gudanar da galibin abubuwan da kake iya gudanarwa a Windows.  Misali, za ka iya dora mata “Microsoft Office” don kirkira da sarrafa bayanai, sannan akwai manhajoji da dama da za ka iya saukarwa kyauta daga shafin kamfanin kyauta, don amfana da ita.   Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya ameen. Ina bukatar makalarka wacce kayi akan tsibirin bamuda. Don Allah in ka samu dama ka turo min ta wannan adireshin Imail din. Na gode. aminumusaaliyu2016@gmail.com – Aminu Musa Aliyu

Wa alaikumus salam, barka dai.  Na ingiza maka wannan kasida ta adireshin da ka bayar na Imel.  Sai ka duba.  Allah sa a amfana, amin.  Na gode.


Salam Baban Sadik Allah ya kara fasaha. Malam ina son in koyi yadda ake gina manhajar kwamfuta ne.  Da fatan za a taimaka mini da shawarwari. usmanabbas905@gmail.com – Abbas Usman

Wa alaikumus salam Malam Abbas.  Lallai wannan yunkuri ne mai fa’ida, wanda zai yi matukar amfanar jama’armu musamman a wannan lokaci na yawaitan kayayyaki da hanyoyin sadarwa na zamani.  Da farko dai ina maka albishir cewa shi wannan ilimi na koyon kera manhajar kwamfuta ba dole sai an je jami’a ba ake koyonsa.  Kana iya koyonsa ko a cikin dakinka ne.  Abin da kake bukata shi ne sha’awar abin, da hakuri, da juriya, wanda zai sa a dauki tsawon lokaci ana yi.  Ba abu bane da za ka koye shi cikin dare ba.  Bayan haka, kana bukatar kayan aiki, wanda ya kunshi kwamfuta, da tsarin sadarwa na Intanet, da kuma littattafai ko bayanan da za su taimaka maka wajen koyo a aikace.

Shi ilimin gina manhajar kwamfuta nau’in ilimi da ake yinsa a aikace.  Idan zallar karatun kawai kake yi ba za ka taba koyon komai ba.  Shi yasa, hatta littafan dake karantar dashi za ka samu a cike suke da misalai na darussan da ake karantar da kai.  Don haka, in har baka taba mu’amala da kwamfuta ba, to, dole ne ka nemi daya.  Sannan ka koyi yadda ake sarrafa ta; kamar kunnawa, da kashewa, da yin amfani da manhajojin dake cikinta.  Akwai kuma darasi na musamman da na fara cikin harshen Hausa kan ilimin gina manhajar kwamfuta mai take: “Mu Koyi Programming a Sawwake.”  Ina gabatar da wannan darasi ne ta shafina dake Dandalin Facebook.  Idan kana da shafi a can kana iya nema na sai ka amfana.  Ina maka fatan alheri, kuma ya maka jagora, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.