Ciyar da Najeriya Gaba a Fannin Kimiyya da Kere-Kere (1)

Daga yau za mu fara jera bayanai kan hanyoyin da Najeriya za ta bi wajen ganin an habbaka fannin kimiyya da kere-kere, wanda yana daga cikin fannonin da kowace al’umma ke bukatar bunkasarsa, muddin tana son ci gaba. A wannan makon munyi gabatarwa ne, don fuskantar da mai karatu abin da kasidun ke dauke dasu gaba daya.

567

Mabudin Kunnuwa

Makonni uku kafin Nijeriya ta cika shekaru hamsin da samun ‘yancin siyasa daga kasar Burtaniya da ta mallake ta na tsawon shekaru kusan dari, Sashen Hausa na Rediyon BBC ya gayyace ni don wata hira ta musamman kan ci gaban da kasarmu ta samu tsawon shekaru hamsin tun samun ‘yancin kai, a fannin Kimiyyar Sadarwa, wato Information & Communications Technology (ICTs).  Malam Ibrahim Isa, wanda ya jagoranci wannan hira a madadin gidan rediyon, yana son in sanar da al’ummar kasar nan ne irin halin da muka baro a baya a fannin sadarwar tarho, da kwamfuta, da kuma samuwar Intanet, da halin da ake ciki yanzu, da kuma cewa ko nan gaba kasar nan na iya jagorantar kasashen Afirka a fannin sadarwar wayar salula da kwamfuta da Intanet, da kuma amfani da Tauraron Dan Adam wajen ciyar da al’umma gaba a fannonin ilimi, da likitanci, da sadarwa, da shugabanci.  A cikin wannan hira, wacce ta dauki tsawon mintuna goma a takaice,  na tabbatar da halin da muke ciki iya gwargwado, da irin kokarin da gwamnati ta faro a baya, da kuma abin da take kan yi a yanzu.  A karshe dai, kamar yadda na san da yawa cikin masu karatu suka ji (saboda sakonnin tes da kira da na samu), na tabbatar da cewa har yanzu Nijeriya bata kai ko ina ba a wannan fanni.  Wannan hukunci zai tabbata ne idan muka gwama kasarmu da sauran kasashen Afirka, wadanda muke nahiya daya da su, ba wai da wasu kasashen da suke nesa ba.

To amma duk da haka, wannan ba ya nuna cewa bamu yi wani kokari ba, musamman idan muka dubi halin da a baya muka baro.  Duk da cewa wannan kasa ba ta da wani tabbataccen tsarin samar da ci gaba a fannin kimiyar sadarwar zamani kafin shekarar 2000, amma da Shugaba Olusegun Obasanjo ya dare karagar mulki ya kafa wani kwamiti da yayi nazari ya kuma fitar da shawarwari masu kayatarwa na yadda za a mayar da kasar nan gagarabadau a fannin kimiyyar sadarwa ta zamani, ba a nahiyar Afirka ma kadai ba, har a sahun kasashen duniya baki daya; kafin shekarar 2010.  Wadannan shawarwari sun hada da samar da hukuma mai zaman kanta wacce za ta lura da wannan aiki baki dayansa.  Wannan hukuma ce za ta zama sila tsakanin tsare-tsaren gwamnatin tarayya a daya bangaren, da na jihohi da kuma na kananan hukumomi.  Ta hanyar wannan hukuma, za a ilmantar da jama’ar kasa yadda za su iya amfani da hanyoyi da kayayyakin sadarwa na zamani, za a samar da runbunan adana bayanai a dukkan bangarorin uku, za a samar da gamammen tsarin sadarwa ta Intanet, wanda zai hada dukkan makarantun kasar nan – jami’o’i da sakandare da kuma firamare – da asibitoci, da cibiyoyin binciken kimiyya da kere-kere, da jami’an tsaro, da jami’an shigi-da-fici (kwastan da magireshon) da sauransu.

- Adv -

Bayan haka, shawarwarin, wadanda aka dabba’a su cikin wani kundi mai take: National Information Technology Policy, mai shafuka 52, sun wajabta wa Gwamnatin Tarayya aikin samar da kudaden shiga da kuma hanyoyin hadin gwiwa tsakanin Nijeriya da wasu kasashe da suka ci gaba a wannan fanni.  A takaice dai, wannan kundi na dauke ne da shawarwari mafi kayatarwa, wadanda da zarar an dabbaka kashi sittin cikin dari, ba ma dukkansu ba, kasar nan za ta ci gaba a wannan fanni, har ma ta zama abin koyi.  To amma kaico!  In ka kebe hukuma guda daya da aka kafa mai suna National Information Technology Agency (NITDA), wacce har yanzu take fama da matsalolin kudaden gudanar da aiki, babu abin da aka yi.  Sai cikin watan Mayun wannan shekara ne gwamnati mai ci ta sake kafa wani kwamiti da yayi bitar “ci gaban” da ake tsammanin an samu a baya, sannan ya sake fitar da wani kundi mai take: “ICT 4 Development”, wato “Ciyar da Nijieriya Gaba ta Hanyar Kimiyyar Sadarwa na Zamani”.  Wadannan sababbin tsare-tsare dai ba su da bambanci da abin da wancan na baya ya kunsa, sai bambancin shekarun da aka haddade cewa kasarmu za ta ci gaba, har ta shallake wasu kasashen; zuwa shekara ta 2015.

Wannan hira na daga cikin dalilan da suka sa shafin Kimiyya da Kere-kere ganin dacewar gabatar da bicike na musamman kan ci gaban wannan kasa ba a fannin kimiyyar sadarwar zamani kadai ba, har da fannin kere-kere, wadanda su ne ginshiki wajen ci gaban kowace kasa a duniya.  Domin ta hanyarsu ne kasa ke iya ciyar da al’ummarta har ma ta fitar da ragowar abin da ta noma zuwa wasu kasashe, ta hanyar ci gaba a fannin kimiyya da kere-kere ne kasa za ta iya hada kan al’ummarta a siyasance, ta koya musu tarbiyya ingantacciya; ta hanyar gamammiyar tafarkin sadarwa da ingantaccen rumbun bayanai na kasa.  Har wa yau, ta hanyar inganta wadannan fannoni ne hukuma za ta iya samar da kyakkyawar hanyar bayar da ilmi – daga matakin farko har zuwa kololuwa – ga dukkan al’ummarta. Ta hanyar bunkasa wadannan fannoni guda biyu hukuma na iya samar wa al’ummar kasarta dukkan ababen da suke bukata a fannin kere-kere; daga kayayyakin amfanin gida, zuwa ababen hawa irinsu jiragen sama, da na ruwa, da motoci, da babura, da kuma kekuna.  A daya bangaren kuma, tana iya amfani da wadannan fannoni wajen rage yawan sace-sace, da kashe-kashe, da dukkan wasu ayyukan assha a kasa.  Samuwa da yiwuwar dukkan wadannan ababe a kasa irin Nijeriya ba wani abu bane mai wahala in Allah ya yarda.

Za mu ci gaba

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.