Ka’idojin Mu’amala da “Password” (2)

Ga kashi na biyu cikin jerin kasidun dake nazari kan “Kalmar Sirri”, wato “Password” da mahimmancinsa ga mai mu’amala a shafin Intanet. A sha karatu lafiya.

132

Wuraren Shigar da “Password”

Bayan bayani kan rukunan “Password” a bangaren karshe na kasidarmu ta makon jiya, yana da kyau mai karatu ya san a wasu wurare ne ake shigar da “Password.”  Tabbas a yayin bayani kan ma’anar “Password” mun ji cewa daga cikin bangarorin wannan ma’ana akwai wurin da ake shigar da kalmar.  Wannan wuri shi ne mahallin farko da “Password” ke bi a yayin da ake kokarin tantance wanda ya shigar da kalmar, don bashi damar isa ga bayanai ko manhajar da yake son mu’mala dasu/ita.  A asali da kuma tunanin al’ada na mutumin da bai saba mu’amala da hanyoyi da na’urorin sadarwa a baya ba sai yanzu, mun dauka wajen shigar da “Password” wuri daya ne ko biyu rak!  Ko dai wajen shiga Dandalin Facebook, ko kuma wajen shiga kwamfutarmu, idan muna da ita.  Wannan tunanin asali ne, ko tunanin wanda bai saba mu’amala bane da hanyoyi da na’urorin sadarwa na zamani.

Mahallin farko da tafi kowacce tsufa da ake shigar da “Password” a cikinta ita ce babbar manhajar kwamfuta, wato: “Computer Operating System.”  Idan mai karatu bai mance ba, sadda muka yi bayani kan tarihi da samuwar “Password” mun zayyana wata babbar manhajar kwamfuta mai suna “Time Sharing System” (TSS), wacce ita ce babbar manhajar kwamfuta da ta fara zuwa da tsarin tantance mai mu’amala da kwamfuta idan yazo shiga, wato: “User Log In Authentication.”  Duk sadda kazo shiga kwamfuta za a budo maka inda za ka shigar da kalmar “Password” dinka.  Wannan tsari na samuwa ne a daidai lokacin da ake kunna kwamfutar a karon farko bayan an saya.  A wannan lokaci ne ake shirya “Suna” (Username) da kalmar “Password” din mai kwamfutar.  Idan ba a zabi “Password” ba a sadda ake tsara kwamfutar, duk sadda aka kunna ta, za ta budo shafin farko ne (Desktop) kai tsaye.  Amma muddin an sa “Password”, to, za a budo maka shafin shigar da “Password” ne, wato “User Log In Page.”  Wannan shafi akwai manhajar dake motar dashi a sadda ka kunna kwamfutarka.  Wannan manhaja ita ake kira: “Winlogon.exe”

Mahalli na biyu da ake shigar da “Password” a bisa tilas shi ne wajen bude akwatin Imel.  Bayan ka bayar da bayanan da suka shafeka, dole za ka zabi “Suna” (Username) da kuma Kalmar Iznin Shiga (“Password”).  Wadannan abubuwa guda biyu su ne mabudai kamar yadda kuma su ne makullan akwatinka na Imel.  Idan kazo shiga akwatinka na Imel, bayan ka shigar da suna (username), dole ne kuma ka shigar da kalmar zinin shiganka (password) da ka zaba a sadda kake bude Imel din a karon farko.  Imel din na iya zama na kashin kanka ne wanda ka bude a daya daga cikin gidajen yanar sadarwa na Intanet, wato: Internet Mail Program (irin su Gmail, da Yahoomail, da Hotmail), ko ya zama na ma’aikatar da kake wa aiki ne, wanda su ne za su ba ka bayanan duka.  In yaso idan ka shiga sai ka canza “Password” din.  Wannan shi ne mahalli na biyu.

Mahalli na uku wajen shigar da “Password” shi ne Wayar salula.  A zamanin baya a asali wayoyin salula kan zo ne haka kawai, babu wani tsarin kariya a tare dasu, domin a lokacin galibi kira kawai ake iya yi ko amsa kira na murya.  Amma a yau wayoyin salula sun zama wasu kananan kwamfutoci ko ma’adanai na bayanan sirri masu mahimmanci, wanda dole aka sanya musu hanyoyin kariya.  A halin yanzu wayoyin salula na da hanyoyin kariyar bayanai wanda shigar da “Password” ke daya daga cikinsu.  Babbar hanyar kariya ga wayar salula gamammiya ita ce tilasta shigar da wasu bayanai kafin iya mu’amala da wayar bayan an kunna ta.

- Adv -

Wannan, kamar yadda tsarin kwamfuta yake, ya danganci yadda mai wayar ya tsara ta ne a farko.  Idan ka tsara a duk sadda ka kunna ko ta shiga halin hutu ta rika kulle kanta ne, sai ka shigar da kalmomin neman izni (passcord/passkey) kafin a bude maka, haka za ta zama.  Idan kuma sai ka yi wasu zane ne (security pattern) a shafin wayar kafin a bude maka, haka za ta zama.  Wadannan hanyoyi ne da a kullum ake dada inganta su don baiwa mai wayar salula natsuwa a zuciyarsa.

Mahalli na hudu wajen shigar da “Password” shi ne yayin mu’amala da na’urar ATM (Automated Teller Machine) wajen cirewa ko sanya kudi a taskar banki.  Idan ka zabi karbar katin ATM don saukake hanyar mu’amala da bankinka, za a baka katin ne tare da wasika mai dauke da kalmar “Password” dinka, wato PIN Cord, ko “Personal Identification Number Cord.”  Wannan wasu lambobi ne guda hudu (dole su zama hudu), wadanda dole ka rika shigar dasu a sadda kazo cire kudi a wannan na’ura ta ATM.  A karon farko idan ka fara amfani da wannan PIN da aka baka, na’urar za ta kaika wajen canza lambobin ne kai tsaye.  Da zarar ka canza zuwa lambobin da kake bukata, sai ka ci gaba da amfani da na’urar.  Wannan ita ma mahalli ce daga cikin mahallan da dole ne kayi amfani da kalmar “Password.”

Mahalli na biyar shi ne na’urar sawwara bayanai, wato: “Photocopier Machine.”   Wannan ita ce na’urar da ake amfani da ita wajen daukan hoton bayanai da aka buga a shafin takarda, don amfani dasu ta wasu hanyoyi daban.  A zamanin baya ire-iren wadannan na’urori ba a sanya musu komai na kariya kafin amfani dasu.  Amma a halin yanzu sukan zo da tsarin kariya na musamman, don tabbatar da cewa sai wanda aka aminta yayi amfani dasu kadai zai yi.  Misali kamar a manyan ofisoshin gwamnati da na masu zaman kansu, wadannan na’urori an tsara su ne ta yadda sai ka shigar da wasu lambobi (PIN Cord) guda hudu kafin su baka damar sawwara takardar da kake son sawwarawa.  Da su da wayoyin salula duk tsarin “Password” dinsu daya ne, wato lambobi ne da basu shige guda hudu.

Mahalli na shida shi ne wajen mu’amala da na’urar wasan kwamfuta, wato: “Game Console.”  Akwai na’urorin wasan kwamfuta (Games) da kamfanoni da dama suka kera: irin su Sony PS2, da Sony PS3, da Sony PS4 na kamfanin Sony Pictures.  Sannan akwai na kamfanin Microsoft mai suna: Xbox.  Dukkan wadannan idan ka tashi mu’amala dasu dole sai ka shigar da kalmar izninin shiga, domin ana jona su ne da talabijin kwamfuta a daya bangaren.  Sannan a daya bangaren kuma suna jone ne da rumbun adana bayanai na kamfanin (misali xBox na kamfanin Microsoft), sai an tantanceka tukun kake iya samun kaiwa ga bayanan.  Sai an samu dacewa tsakanin sunan da ka bayar da kalmar izinin shiganka sannan za a baka damar iya mu’amala da wannan na’ura don buga wasan.

Mahalli na karshe da za mu dakata a kai shi ne wajen mu’amala da tashoshin talabijin masu amfani da tauraron dan Adam, wato: Cable TV Decoders.  A wasu kasashe idan ka sayi layin don kallon ire-iren wadannan tashoshi za a baka suna da kalmar izinin shiga don tantance ka, tunda harka ce ta kasuwanci.  Mu a nan Najeriya galibi kamfanonin tashoshin talabijin na tauraron dan adam sukan shigar da wannan kariya ne ta na’urar da talabijinka ke amfani da ita, wato: Satellite Decoder.  Da zarar ka kunna na’urar, nan take sai na’urar ta nemo maka sigina kai tsaye.  A tare da haka, ba ka iya canza wasu tsare-tsaren dake tashoshin sai ka shigar da “Password” a yayin da kaje bangaren tsare-tsare (Settings).

Wadannan wurare ko mahallai, a takaice, suna daga cikin wuraren da aka fi amfani dasu wajen shigar da “Password” a halin yanzu.  Sai dai kuma, meye dalilin da yasa mutane ke kirkirar “Password”?  A mako mai zuwa in Allah yaso za mu ji wadannan dalilai.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.