Sakonnin Masu Karatu (2006)

Ga wasu daga cikin wasikun masu karatu nan da suka aiko a lokuta daban-daban.  Da dama daga ciki na bayar da amsarsu.  Ban kuma kawo sakonnin Imel ba, saboda karancin wuri.  Mun gode, Allah Ya saka da alheri, amin.

93

“…bayan gaisuwa tare fa fatar kana lafiya Allah Yasa haka amin.  Dalilin rubuto maka wannan sako shi ne, ni ma’abocin karanta jaridar Aminiya ne kowane sati, kuma filinka na Kimiyya da Fasaha yana daya daga cikin filayen da nake karantawa kwarai da gaske.  Saboda haka nake tambaya kan yadda mutum zai bude adireshin Imel da kuma inda ake zuwa a bude.  Ka aiko min cikakken bayani a wannan lambar da na aiko maka da wannan sako.  Ka huta lafiya.”  –  Abdullahi Mohammad Argungu, 080 23578938


“Wallahi ina murna da irin tambihin da kake mana kan Intanet.  Kuma ina fatan ka taimaka mani da abin da ya dace a zaure na: http://groups.yahoo.com/group/musulmai” – 

Daga 080 30819598


Assalaamu Alaikum (Baban Sadiq), ina son in shiga Intanet ta wayar hannu, amma ban san yadda zan yi ba.  Ina neman taimako a gunka, kan yadda zan yi.”  –  Mohammad Abbas Lafiya, 080 36647666


“Mal. Abdullahi naji dadin write up dinka a kan Gmail, kuma zan yi sign in, in kara samun gogewa akan IT.  God Bless”  –  Abdullahi Azare, 080 36305226


“Salam, yanzu na gama kammala karanta bayananka a Aminiya na 4 ga wata, kan Mudawwana #2.  A gaskiya na sake ilmantuwa.”  –  Shehu Mustapha Chaji, 080 44191221


 “Salam, ina fatan kana lafiya.  Na rubuto ne don gaisuwa kawai.  Da fatan komai yana tafiya daidai.  Na ga gaisuwarka a jaridar Aminiya na makon jiya.  Mun gode.”  –  Muntaka Abdul-Hadi Zaria, 080 36397682


 Salam, ina karanta shafinka a jaridar Aminiya, kuma yana kayatar da mu.  Ina labarin Gamji Chatroom?  Muna bukatar sanin inda aka kwana.”  –  Salisu Hashim Fagge, 08054361950


 “As salaamu Alaikum, Mal. Abdullahi muna jin dadin bayananka, musamman bayani kan gidan (yanar) Kanoonline da kayi.  Allah Ya kara basira, amin.”  –  Sanusi Sani Dala, Suleja,      080 36800241


- Adv -

As salaamu alaikum

Malam Muntaka, da fatan kana nan cikin koshin lafiya, Allah sa haka, amin.  A mini afuwa, na shagala ban samu rubuto jawabi da wuri ba.

Dangane da abinda ya shafi sanya hoto a mudawwana, babu wahala.  Abinda zaka fara yi shine loda hotonka a cikin kwamfutarka, ko kuma a “diskette” ko duk abinda ya sawwaka.  Sai ka bi hanyoyin da ke tafe nan kasa:

  1. Ka shiga Mudawwanarka, sai ka matsa “sign in”, daga can saman hannun dama;
  2. Za a kai ka inda zaka shigar da suna da kalmomin iznin shiganka (username and password), kamar yadda ka saba.  Idan ka shigar, sai ka matsa “sign in”.
  3. Za a kai ka shafin “Dashboard”, idan shafin ya budo, sai ka matsa “settings”.
  4. Idan shafin “settings” ya budo, sai ka je inda aka rubuta “template”, daura kadan da “settings” kenan.
  5. Da zaran “template” ya budo, zaka ga kwarangwal din mudawwanarka gaba daya; daga sama har kasa.  Sai ka matsa inda aka rubuta “add page element”, a sama, daga jerin karikitan da ke hannun damanka kenan.
  6. Da ka matsa, wani dan karamin windo zai budo mai dauke da jerin bayanai hagu da dama.  Sai ka dubi jerin hannun hagu, na uku, in da aka rubuta “picture”, sai ka matsa.  Za a kai ka inda zaka tsara yadda hoton naka zai kasance.  Zaka ga “title”, “caption”, da kuma “image”.  Sai ka ba hoton sunan da kake so ya kasance a samansa.
  7. Daga nan, sai ka matsa “browse”, don nemo hoton da ka ajiye a cikin kwamfutarka ko kuma ma’ajin da ka tanade shi a ciki.  Da ka gama sai ka matsa “save changes”.  Ka jira a gama loda maka shi a mudawwanarka.  Da an gama, za a sanar da kai cewa “your changes have been saved.  View your blog”, ko makamancin haka.
  8. Sai kawai ka matsa “view your blog”, don ganin yadda hoton zai kasance.  Ka gama!

Idan da matsala, ka sanar dani, don Karin bayani.  Khair


Malam Rufa’i,

Da fatan ka tashi lafiya, Allah Yasa haka, amin.  Ai mani afuwa, aiki ne yai mani yawa, sai kuma kailula irin nawa.  A yanzu ga bayanan abinda kake nema, iya gwargwado.

  1. Dangane da abinda ya shafi Dandago, na gode da wannan tunatarwa.  Ka ga ni ma na karu da wannan jawabi.  Khair!
  2. Sai Magana kan Java, da dukkan abinda ya shafe shi, kamar su JavaScript da sauran karikitai.  JAVA suna ne na daya daga cikin ilmummumuka ko fasahan da ake amfani da su wajen gina manhajojin kwamfuta, watau computer softwares.  Akan kira su “Programming Languages”.  Akwai su da yawa, wasu daga cikinsu su ne: BASIC, VISUAL BASIC, C, C++, C#, COBOL, LISP, PEARL da sauransu.  A halin yanzu an fi amfani da fasahar JAVA, saboda saukin koyo da kuma cewa zaka iya amfani da manhajojin da aka gina su da wannan fasaha a kowace irin kwamfuta ne, ko tsari.  An kuma kirkiro wannan fasaha ne tun 1996, in ban mance ba.  Ana amfani da JAVA wajen gina abin wasan kwamfuta (Computer Games), wadanda su ake sanyawa a cikin wayoyin salula da kwamfuta, da dai sauran abubuwa masu muhimmanci a kwamfuta da sauran kayayyakin sadarwa. Shi kuma JavaScript, ba cikakken fasahan gina manhajar kwamfuta bane irin JAVA, a a, shi wani irin nau’I ne na fasahan tsara gidajen yanan sadarwa, watau Script.  A kan yi amfani da shi ne wajen tsara shafukan gidan yanan sadarwa (web pages).  Duk gidan yanan sadarwan da ka shiga ka ci karo da agogo (clock), ko kalanda (calendar) ko kuma kwanan wata (date), to duk da JavaScript aka gina su.  Wanda ya kirkiro wannan fasaha shine Mc Andreessen, mai gidan yanan sadarwan Netscape.

Wannan a takaice, shine abinda zan iya cewa a halin yanzu, sai in munasaban hakan ya kama nan gaba watakil a shafin AMINIYA.  Khair!

Wassalaamu Alaikum!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.