Ma’ana da Tsarin Wayar Salula

Daga wannan mako za mu fara gudanar da bincike na musamman a duk mako kan abin da ya shafi wayar salula gaba dayanta. Wannan kashi na daya kenan, wanda ke kunshe da gabatarwa.

491

Gabatarwa

Saboda samuwa da kuma yaduwar fasahar sadarwa ta wayar salula a yau, an wayi gari, kamar yadda nake sanar da Malam Abubakar AbdurRahman (Dodo), wanda ke lura da wannan shafi na Kimiyya da Fasaha, cewa cikin kashi dari na sakonnin tes da na Imel da nake samu a lokuta dabam-daban daga wajen masu karanta wannan shafi, kashi sittin duk tambayoyi ne a kan ka’ida da kuma yadda ake mu’amala da wayar salula ko kuma hanyoyin sadarwa na zamani da ke jikin wayar; irinsu fasahar Bluetooth da Infra-red da kuma hanyar sadarwa ta Intanet.

Wannan ke nuna cewa galibin masu karatu na da kishirwan bayanai kan wannan fasaha har yanzu. Wannan kuwa dole ya faru, domin fasaha ce wacce a kullum ake amfani da ita.  Kuma duk da cewa na sanya ka’ida da  dokar cewa na rufe karba da kuma buga sakonnin tes da suka shafi wannan fasaha a wannan shafi, har yanzu ba a daina aiko sakonnin tambayoyi da neman Karin bayani a kan wayar salula ba. Duk da barazanar da na yi ta yi kuwa.

A karshe dai nayi tunanin cewa, “tunda daman shafin don masu karatu ake gabatar dashi, don kayatar dasu, da ilmantar dasu, da kuma fadakar dasu kan sabbin abubuwa, me zai hana a dauke dokar, a nemo hanyar gamsarwa?”  Da wannan dai na yanke shawarar gabatar da doguwar kasida mai dauke da dukkan wani abin da ya shafi wannan fasahar sadarwa ta zamani da ake kira wayar salula ko kuma Mobile Phone ko Cell phone, a turance.

Daga wannan mako in Allah Ya yarda, shafin Kimiyya da Fasaha zai ware wani yanki don kwararo bayanai kan yadda tsari da kimtsin wayar salula yake.  Daga ma’ana zuwa asali da samuwar wayar salula, zuwa bayani kan zamunnan wayar salula, da nau’ukan wayar salula; da yanayin sadarwar wayar iska (Wireless Communication), da bangarorin wayar salula, da alakar wayar salula da kwamfuta, da masarrafan da wayar salula ke dauke dasu, da cututtukan wayar salula, da nau’ukan manhajojin wayar salula, da amfanin wayar salula, da cutarwar wayar salula, da tsarin mu’amala ko amfani da wayar salula, da tasirin wayar salula kan rayuwar mai amfani da ita, da aljihunsa, da muhallinsa, da iyalinsa, da kuma al’ummarsa…kai, da duk wani abin da za mu iya tunowa kan abin da ya shafi wannan fasaha a yau.  Don haka sai a bi shafin a hankali.  Hausawa suka ce “hanyar lafiya, a bi ta da shekara.”

Don haka, wadannan kasidu da zasu zo, sakamakon bincike ne mai zurfi, iya gwargwadon hali.  Da fatan masu karatu baza su kosa da tsawonsu ba.  Zan yi hakan ne don neman kosar da ku, iya gwargwado.  Ban ce komai da komai zai samu ba, amma zan zurfafa, zan fadada, zan kuma tsawaita.  A babin fadakarwa, kowane kasida zai zo ne da takensa.  A yau za mu yi tsokaci ne kan “Ma’ana da Asalin Samuwar Wayar Salula” a duniya. Mu je zuwa, wai mahaukaci ya hau kura.

- Adv -

Ma’anar “Wayar Salula”

Da dama cikinmu idan an tambaye mu ma’anar wayar salula, ba abin da za mu ce illa “wayar da ke hannunmu, wacce muke yin kira ko amsa kira da ita.”  Wannan ma’ana ce mai kyau, sai dai kuma a ilmin fasahar sadarwa ta zamani, tana bukatar fadadawa da Karin bayani.  A takaice dai me ake nufi da wayar salula, a ilmance?  Idan aka ce Wayar Salula, ko Mobile Phone ko Cell Phone a turance, ana nufin “Wayar tafi-da-gidanka ko wayar hannu, mai amfani da siginar rediyo (Radio Signal) don karbar kira ko amsa kira tsakaninta da waya ‘yar uwarta, a iya kadadar tashar sadarwa (Base Station).”

Galibin wayoyin salula na dauke ne da Katin SIM (Subscriber Identification Module), mai kumshe da lambar  wayar mai ita, da kuma ma’adanar lambobin mutane (Contacts Memory). Wannan ke nuna mana cewa kafin a kira wayar salula da wannan suna har ta amsa, dole ne a samu abubuwa guda hudu tare da ita. Abu na farko shi ne ita kanta wayar, wato wayar hannu.  Abu na biyu kuma shi ne Katin SIM, wanda ke dauke da lambar mai wayar.  Abu na uku kuma shi ne samuwar tsarin sadarwa ta wayar iska mai dauke da siginar rediyo a tsakanin wayar salula da wata wayar.  Sai abu na hudu, wato tashar sadarwa, ko Base Station kamar yadda bayani ya gabata a sama.  Ita kuma tana samuwa ne daga kamfanin sadarwar da ya bayar da Katin SIM din da ke cikin wayar.  Sai da wadannan abubuwa guda hudu za a iya amfani da wayar salula don kiran wani ko amsa kiransa.

Da wayar salula mai dauke da wadancan sifofi guda hudu, kana iya kiran wani da ita, ko ya kira ka, ko kayi amfani da fasahar Intanet in har kamfanin na da wannan tsari, ka iya aika sako ta amfani da fasahar Bluetooth ko Infra-red, ko ka iya amfani da wayar a matsayin makalutun sadarwa ta Intanet, wato Modem, don shiga Yanar Sadarwa ta Duniya.  Da irin wannan waya har wa yau, kana iya aiwatar da harkokin kasuwanci, ka aika da sakonnin tes, ka yi mu’amala da bankinka, ko likitanka, ko malaminka, ko matarka, ko ‘yar uwarka ko kanenka da dai sauran abubuwan da mai amfani da waya ta hanyar kamfani ke iya yi. Da irin wannan tsari na sadarwa ne aka wayi gari duniya ta rikide da zumunci a tsakanin kayayyaki da hanyoyin sadarwa.

Misali, akwai alaka mai karfi na sadarwa a tsakanin wayar salula da kwamfuta – da Intanet ko babu.  Akwai alaka mai kwari tsakanin kwamfuta da gidajen talabijin, da gidajen rediyo.  Akwai alaka har wa yau a tsakanin gidajen jaridu da fasahar Intanet, da wayar salula, da kuma dukkan sauran kafafen watsa labarai.  Sanadiyyar wannan gamayya an samu canjin tsarin kere-keren kayayyakin amfani a gida, inda aka wayi gari ana kera su tare da sinadaran sadarwa mai kulla alaka tsakaninsu da sauran ababen sadarwa da ake amfani da su a gida ko ofis.  Sanadiyyar haka kana iya samun na’urar dumama abinci mai amfani da fasahar Bluetooth, ko na’urar buga bayanai (Printer) mai amfani da fasahar Bluetooth ita ma, kuma da haka kana iya basu umarni su karba ta hanyar wayar salula ko kwamfutarka ko na’urar talabijin dinka.

Wannan gamayya na zumunci a tsakanin kayayyakin sadarwar zamani shi ake kira Network Convergence a fannin fasahar sadarwa ta zamani.  Kuma kashi sittin cikin dari na sanadinsa daga wayar salula ne.  In kuwa haka ne, ta yaya aka samo wannan fasaha mai matukar tasiri a duniya?

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. AMINU ZUBAIRU says

    Assalamu Alaikum, Baban Sadiq ina maka Fatan alkhairi, da godiya kan kokarin da kake yi wajen karantar da mu a harshen hausa, Allah ya biya ka da mafificin alkhairinsa, gaskiya nima ina son in zama kamarka a nan gaba. Allah ya raya mana Sadik. Daga AMINU ZUBAIRU

Leave A Reply

Your email address will not be published.