Kimiyya da Fasaha a Kasashen Musulmi (1)

Tarihin Ci Gaban Ilmin Kimiyya a Kasashen Musulmi

An buga wannan makala ne a jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 12 ga watan Nuwamba, 2021.

327

A yau mun yi babban bako ne a wannan shafi namu mai albarka, wanda zai taya mu hira ta hanyar tarihi a fannin kimiyya da fasahar qere-qere sadda qasashen musulmi ke kan gaba wajen ci gaba a fannin. Asalin wannan rubutu an buga shi ne cikin harshen Turanci a shahararriyar Mujallar nan ta Fiziya mai suna: Physics World dake qasar Amurka, a shekarar 2010. Farfesa Jim Al-Khalili, wanda qwararre ne a fannin nazarin kimiyyar Fiziyar Nukiliya (Theoritical Nuclear Physics) a Jami’ar Surrey dake qasar Burtaniya ne ya rubuta shi.   Shi ne kuma mawallafin babban littafin nan a kan gudunmowar da Musulmai ko Larabawa suka bayar wajen ci gaban kimiyya da fasaha a duniya mai suna: The House of Wisdom wanda maxaba’ar Penguin Press ta buga a shekarar 2010.  Wanda ya fassara wannan asalin maqalar dai, wanda zai baquncemu nan da wasu makonni dake tafe, shi ne Malam Muddassir S. Abdullahi, kuma qwararren mai aikin fassara da tarjama ne dake zaune a tsakanin Abuja da Kano. Za a iya samun sa a: 08168632515, ko: taubat1234@gmail.com.

——————–

- Adv -

Shekaru xaruruwa da suka shuxe, a zamanin da yankunan qasashen Turai ke cikin duhun kai da qamfar ilimi da bincike da har ta kai ake wa waxannan qarnukan kirari da Dark Ages, wato Shekarun Jahiliyyar Yankin Turai, a lokaci guda, garuruwan Musulmai na wannan lokacin na kan ganiyar su na kaiwa qololuwa a binciken ilimin kimiyya da fasaha da qere-qere da sauran ilimai da cigaban rayuwa. Abun tambayar a nan shine, “yaya qasashen Musulmai suka zamanto kurar baya a vangaren binciken kimiyya da fasaha da qere-qere a yau?” Wannan ce amsar da Farfesa Jim Al-Khalili ya yi qoqarin amsawa a bayanan da za su zo a qasa, da farko, ta hanyar gano sabuban da suka sanya Musulmai suka zamo ba a jin xuriyar su a fagen kimiyya da fasaha da qere-qerena yau, ya kuma rufe rubutun nasa da zayyano matakai da shirye-shiryen da idan an xabbaqa su za su iya dawowa Musulmai kambun su na jagorancin duniya a fagen binciken kimiyya da fasaha da kuma qere-qere a yau. A sha karatu lafiya!

A yanzu, yayin da ka ke biya wannan rubutun, akwai al’ummar Musulmai a duniya sama da miliyan dubu, wato duk mutum xaya duk cikin taron mutane biyar Musulmai ne ko sama da haka da kaxan. Cincirindon wannan al’ummar suna zaune ne mafi yawan su a sama da qasashe 57 dake faxin duniya, ana yiwa taron waxannan qasashe laqabi Taron Qasashen Musulmai, ko ka ce Organization of Islamic Conference (OIC). Waxannan cincirindon taron qasashen sun haxar da wasu daga qasashen da suka fi arziqi a faxin duniya, kamar su Saudiyya da kuma qasar Kuwait, haka kuma akwai da qasashen da suka fi talauci, kamar su Somalia da Sudan. Duk a tsukin shekarun da suka shuxe tattalin arziqin wasu daga waxannan qasashen – kamar irin su Gulf States, da qasar Iran, da Turkiyya, da Morocco, da Egypt, da Malaysia, da kuma Pakistan yana ta qara havvaka a kullum, amma fa idan ka kwatanta qarfi da havakar tattalin arziqin nasu da na qasashen Yamma (America da sauransu) da kuma (Turai) za ka ga bambancin da rarar dake tsakanin su da yawa. Hakan na da alaqa da sakin wawa da qasashen Musulmai suka yiwa Ilimin kimiyya da fasaha da qirqire-qirqire waxanda sune qashin bayan havakar tattalin arziqin kowacce qasa da al’umma.

A bayyane yake ga idanuwa da zuciyoyin shuwagabannin waxannan qasashen cewa havakar tattalin arziqin su, da buwayar qarfin sojan su da kyautata tsaron su kacokan suna dogara ne kacokan a kan qarfin cigaban su a vangaren kimiyya da fasahar zamani da kuma qirqire-qirqire da ake yiwa laqabi da Technological Advances. A inda qarshen balagar zancen ke tiqewa duk lokutan da ake tattauna koma bayan da qasashen Musulmi ke ciki a yau a vangaren cigaban kimiyya da fasaha da qirqire-qirqire maganar ba ta wuce cewa wajibi ne su qara zage dantse su kuma qara duqufa wajen ninninka himmar su wajen bincike a vangaren kimiyya da fasaha da kuma cigaba matuqar suna bixar kama qafafuwan sauran al’ummar duniya da suka yi nisa wajen gina waxannan ilimai na sama da ba su gudunmowar da ta cancanta da su, ta haka ne kaxai za su shigo fagen dagar ga ni-ga ka da gogayya a wannan duniyar ta Idan ba ka yi ba ni wuri a cigaban ilimi da qirqire-qirqire. Duk da idan ka xauko waxannan qasashen ka dube su kayi nazarin su za ka ga gwamnatocin su suna yin qoqari wajen narka da ninninka tallafi da kason da suke ba wa vangaren Ilimin kimiyya da ma ilimi kacokan a ‘yan shekarun nan. Wani qarin abun sha’awa har ila yau shine, akasarin qasashen Musulmai a tsukin nan suna ta qara havvaka da qara zamanantar da cibiyoyin binciken su na kimiyya na qasa da ake kira da National Scientific Infrastructures. Amma me nake nufi a sakin layi na sama yayin da nace akasarin qasashen Musulmai a yau har yanzu ba sa ba wa Ilimin kimiyya da fasaha da kuma qere-qere kulawar da ta kamace su?

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.