Sakonnin Masu Karatu (2016) (14)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

116

Assalamu Alaikum!  Menene bambancin dake tsakanin Yahoomail da Gmail? Me yasa Yahoomail ba ya aiki ne? Mudassir Mando, Jahar Kaduna: mudassirmando@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka da warhaka.  Bambancin dake tsakaninsu shi ne, da farko, Yahoomail na kamfanin Yahoo Inc ne, a yayin da Gmail kuma na kamfanin Google Inc ne, dukkansu kamfanoni ne dake da hajojin sadarwa na zamani a kasar Amurka.  Sannan, Yahoomai ya girmi Gmail nesa ba kusa ba.  Amma a halin yanzu saboda wasu dalilai na tsarin kasuwanci da kuma sunnar rayuwar, Gmail yak ere Yahoomail tasiri da shahara da inganci da kayatarwa a duniyar yau.  Wadannan su ne manyan bambance-bambancen dake tsakaninsu.  Kowanne daga cikinsu na da manhajar Imel na wayar salula, wato: “Mobile Phone Application,” wanda za ka iya saukarwa ka loda wa wayarka.

A duk sadda aka aiko maka sakon Imel, muddin yanayin sadarwar Intanet din wayarka a kunne yake, nan take zai shigo.  Haka idan kana bukatar rubutawa tare da aika sakon Imel ma duk za ka iya yi.  Sabanin yadda kake tunani, manhaja ko akwatin Yahoomail tana aiki sosai kuwa.  Sai in ta wayarka ce ba ta yi, wannan kuma wani abu ne daban.  Bayan haka, yadda za ka iya yin rajistar sabon akwatin Imel da manhajar Imel na Gmail, haka ma za ka iya rajistar sabon akwatin Imel da manhajar Imel na Yahoomail.  Idan kana bukatar manhajar Imel na kamfanin Yahoomail, ka hau cibiyar manhaja ta Android mai suna Google Play, sai ka rubuta “Yahoomail!” nan take za a cillo maka ita, sai ka loda wa wayarka.  Da fatan ka gamsu.


Salam Abban Sadik, gaisuwa da jinjina.  A gaskiya muna matukar jin dadi yadda ake yi mana fashin baki a kan fasahar Internet.   Tambayata a yau inaso a min bayani ne, wai shin, me yesa mutum bazai iya bude akwatin Imel na yahoo ta waya ba sai ta kwamfuta?  Domin akwatin Imel na Gmail da sauransu duk ana iya budewa ta waya.  Sako daga Faisal Muhammad Girei, Jahar Adamawa. – faisalmohammedgirei@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka ka dai.  Kamata yayi tambayar taka tace: “Ta wace hanya ake yin rajistar Imel da manhajar Imel na Yahoomail?” Domin abu ne sananne cewa dukkan manhajojin Imel na kamfanin Gmail da Yahoomail suna iya baka damar yin rajistar sabon akwatin Imel kai tsaye, ba sai ka je shafinsu ta hanyar kwamfuta ba.  Idan kana bukata, kuma kana amfani da waya mai dauke da babbar manhajar Android, kaje cibiyar manhaja ta Google Play sai ka rubuta: “Yahoomail”, nan take za a antayo maka ita, sai ka loda wa wayarka kai tsaye.

- Adv -

Idan kuma ba Android kake amfani da it aka hau masarrafar lilo (Browser) sai ka shigar da wannan adireshin: http://m.mail.yahoo.com, idan shafin ya bude, can kasa kadan za ka ga inda aka rubuta: “Sign Up,”  sai ka shiga, za a budo maka fom sai ka cika ka aika.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da aiki kuma yaya fama da jama’a?  Baban Sadik ko akwai hanyoyi da mutum zai bi wajen gano lambar waya da aka kirashi da ita a boye, ma’ana a “Private Number?” Tambayata ta biyu, ko mutum zai iya tura sakon tes ga wani, kuma amma ya zamanto ka boye lambar wayarka ba tare da yasan wa ya tura masa ba? Muna godiya da yadda ake amsa mana tambayoyinmu. Mu wuni lafiya.  Nasiru Kainuwa Hadejia: 08100229688: knw6339@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai.  Babu wata hanya, a tsarin sadarwa ta Najeriya, da za ka iya amfani da ita wajen gano lambar wanda ya kira da boyayyar lambar wayar salula.  Abin da za kayi kawai idan ya dame ka, sai ka loda manhajar TrueCaller ko makamanciyarta don hana shi kiranka nan gaba.  Amma gano shi kai tsaye ba abu bane mai yiwuwa.  Dangane da amsar tambayarka ta biyu, zan iya cewa eh akwai hanyar aika sakon tes da boyayyar lamba.  Wannan tsari shi ake kira “Anonymous Texting,” kuma za ka iya yin haka ta dayan hanyoyi uku ko hudu.  Hanya ta farko ita ce kayi amfani da adireshin Imel na bogi.  Ma’ana kana iya yin rajistan adireshin Imel, sai kayi amfani da adireshin wajen aikawa da sakon ta hanyar kamfanin waya.  Sai dai mu a nan Najeriya ba mu da irin wannan tsari, sai kamfanonin wayar kasar Amurka irin su Verizon, da AT&T da dai sauransu.

Hanya ta biyu, kayi amfani da hanyar hirar ga-ni-ga-ka, wato: “Instant Chat Messenger App,” wanda galibi yanzu ba a cika amfani dasu ba.  Hanya ta uku, kana iya amfani da gidajen yanar sadarwa a Intanet masu baiwa mutum damar aika sakonnin tes kyauta.  Wadannan su ake kira: “Free Bulk SMS Sites.”  Kuma ta hanyar ire-iren wadannan gidajen yanar sadarwa ne wasu ke aikawa da sakonnin gayyatar aure ko wani biki ko taro.  Domin kana iya aika wa mutane sama da dari sako a lokaci guda, duk da ya danganci tsarin shafin.  Akwai wadanda za su baka damar aikawa da sakonni 20 ne kadai, idan ya wuce haka, sai ka biya.  Wasu kuma su baka daman sama da hakan.  Ya danganta.

Hanya ta karshe kuma wanda ita ce mafi sauki idan an dace, shi ne amfani da manhajar wayar salula dake sawwake aikawa da ire-iren wadannan sakonni kai tsaye, tare da boye lambar wayarka.  Idan kana amfani da Android ne, kaje cibiyar Play Store, sai ka rubuta: “Anonymous Texting Apps” za a jero maka su, sai ka zabi wacce tayi maka.  Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.