Sakonnin Masu Karatu (2011) (16)

Ci gaban sakonnin da na fara amsa makon jiya.  A sha karatu lafiya.

155

Barka da war haka Baban Sadiq, ga ‘yan tambayoyi na; 1) Me ake nufi da ICT a harshen Hausa? 2) wace irin gudunmuwa ICT ke ba wa harshen hausa?  3) A fada mini gidajen yanar sadarwa guda 10 da ke bayani da harshen Hausa kamar gumel.com da sauransu: shamoo04@yahoo.com

Cikin yardar Allah na aika maka makalar da Farfesa Abdallah Uba Adamu ya rubuta kan wannan a shekarar 2004, mai take: Hausa and Information Communication Technologies (ICTs).  A ciki za ka samu amsar dukkan wadannan tambayoyi naka. Makalar tana da tsawo, don shafuka 24 ne. Sai ka saukar za ka iya bugawa ko karantawa a shafin kwamfuta; duk wanda ka so yi.  Allah sa mu dace, amin.


Salamu alaikum Baban Sadiq, ni ne Haruna Katsina da na kira ka dazun da safe.  Da ma abin da nake son tambaya shi ne:  akan Gmail ne; yaya yake?  Kuma ya ake amfani da shi? Nayi rejista dinsa amma na dauka duk tare suke da Imail; amfaninsu daya kuma, amma sai naga sabanin haka. Shi ne nake son ayi man bayani akan shi Gmail din tare da kuma shi Imail din baki daya.  Wannan shi ne username din Gmail din da nayi rejista: Ibrahimharuna1@gmail.com. Sannan inda dama ka ba ni adireshin da zan iya samun Imai din, domin waya ta ba ta da Imail. Na gode

Malam Haruna akwai alamar ba ka taba amfani da masarrafar Imel ba.  Ai kalmar Imel gamammen suna ne da ke ishara ga dukkan hanyar wasikar sadarwa ta Intanet, da wacce ake amfani da ita a tsarin sadarwa tsakanin kwamfutoci a gajere da dogon zango.  Da Yahoo Mail, da Hotmail, da Gmail (ko Google Mail), duk nau’ukan Imel ne.  babu wani bambanci tsakanin Imel da Gmail sai na suna.  Idan kana da jakar wasikar Gmail, to ka mallaki Imel a rayuwarka.  Abin da kalmar “Email” ke nufi shi ne, “Electronic Mail.”  Don haka kada ka damu, ka riga ka samu Imel, tunda kana da Gmail. 

Gmail wani nau’in Imel ne da kamfanin Google da ya bude ba da jimawa ba.  Haka Yahoo Mail, nau’in Imel ne na kamfanin Yahoo!  Haka ma Hotmail, nau’in Imel ne na kamfanin Microsoft.  Dangane da wayarka kuma, ban san wace iri bace, amma ina kyautata zaton cewa lallai tana da Imel.  Idan kana son gane haka, ka je “Menu”, sai ka shiga “Message”, daga nan ka matsa wajen “Create Message”, za a budo maka nau’ukan sakonnin da za ka iya rubutawa ka aika.  A misali, za ka ga: “Text Message, Multimedia Message, Audio Message, Email”, a jere.  Sai dai shi tsarin Imel da ke cikin wayoyin salula ya sha bamban da wanda ke jikin Intanet kuma ake shiga ta kwamfuta.  Wanda ke cikin wayar salula na bukatar a saita shi, kuma hakan na bukatar kwarewa, a gaskiya. 

Don haka idan kana bukatar mu’amala da Imel ta wayar salula cikin sauki, ka shiga gidan yanar sadarwar Google ko Gmail ta wayarka kawai (da ke http://mail.google.com), sai ka shigar da bayananka.


Salamu alaikum Baban sadik, Tambayata itace ko mutum zai iya tafiya akan doron Wata (Moon) domin wani bincike a kansa? Daga Aliyu Mukhtar Sa’idu (I.T) Kano, aliitpro2020@.com 08034332200

- Adv -

Malam Aliyu ai tuni har an yi kuwa.  Abu ne mai yiwuwa, kamar yadda tarihi ya nuna lokacin tafiyar su Neil Armstrong a shekarar 1969.  Sun taka saman Wata, inda suka gudanar da binciken da suke son yi.  A karshe suka debo samfurin kasar wurin, don shigowa da shi duniya da ci gaba da gudanar da bincike kan yanayin wurin.  Sai dai kuma ya kamata mu sani, muhallin da ke saman Wata ya sha bamban da irin muhallinmu.  Domin a yayin da muke da iska mai kadawa da muke shakarta a nan, a can babu irin wannan iska.  Don haka masu zuwa duniyar Wata ke sanya wasu tufafi masu dauke da na’urar shakar iska, wacce ke taimaka musu wajen numfasawa yadda ta kamata.  Sannan a can babu tsarin Janyo nauyi kasa, wato “Force of Gravity” kamar yadda muke da shi a sararin wannan duniya tamu.  Wannan tasa za ka gansu kamar suna tafiya ne a saman iska, ba su daidaituwa wuri daya a lokaci daya, saboda karancin tasirin wannan tsari a can.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Abu Sadik, don Allah ina son karin bayani akan intanet da Network. Muh’d L Igabi al-igabaawy1986@yahoo.com

Kalmar Intanet dai na nufin hade-haden da ke tsakanin kwamfutoci ko sauran kayayyakin sadarwar zamani, da ke taimaka musu wajen aiwatar da sadarwa ba tare da wata matsala ba, a ko ina suke a duniya.  A daya bangaren kuma, kalmar “Network” na nufin hade-haden da ke tsakanin kwamfutoci ne a wani wuri na musamman.  Misali, ana iya hada kwamfutoci kamar goma a gida daya, su rika aiwatar da sadarwa a tsakaninsu. Haka ana iya hada alaka a tsakanin kwamfutocin da ke wani gida da wani gida da ke unguwa guda, ko gari guda, ko jiha guda.  Duk wadannan tsare-tsare ana kiransu “Network”.  Idan a gida daya ne, sai a kira su “Locak Area Network” (LAN).  Idan a tsakanin gari da gari ne, ko unguwa da unguwa, sai a kira shi “Wide Area Network” (WAN).  Bambancin da ke tsakaninsu shi ne, Intanet ta fi fadi sama da “Network.” 

A takaice ka iya cewa, Intanet hadaka ce ta nau’ukan “Network” a duniya.  A yayin da tsarin Network ke da iya haddi da tsaro da kuma mai lura da tsarin (wato Network Administrator), a tsarin Intanet babu wannan.  Ita Intanet muhalli ne ko wata duniya ce mara iyaka.  Ta ko ina kana iya shiga.  Ta ko ina kana iya fita.  A kowane lokaci kana iya shiga.  A kowane lokaci kana iya fita.  Amma a tsarin Network dole sai an baka iznin shiga, da lokaci, da kuma inda za ka tsaya; baka isa ka wuce ba.  Dukkan wadannan kaidoji ba su a tsarin Intanet.  Da fatan ka gamsu.


Salam ya aiki? Ina da kwamfuta amma ban san yadda zan yi rejistan intanet ba, ko a waya ma ban iya ba. Don Allah yaya zan yi?

Wannan abu ne mai sauki. Ka je ofishin kowanne daga cikin kamfanonin wayar salula da muke da su, ka sanar da su cewa kana son “Internet Modem”, wato makalutun sadarwa ta Intanet.  Za su sayar maka, sannan su jona maka kwamfutar nan take.  Sai dai za ka rika loda kati a duk sadda kudinka ya kare, don ci gaba da samun sadarwa a kwamfutar. Ko a duk sadda iya adadin kwanakin da suka yanke wa kudin.  Ma’ana, idan ka loda kudi, akwai iya adadin bayanan da za a ba ka; kamar 200MB, ko 500MB misali.  Idan wata guda ya kare baka gama cinye wadannan adadin bayanai ba, za a kulle sai ka sa kudi sannan a kara maka wasu a kan wadanda suka rage.  Dangane da wayar salula kuma, ka aika sakon tes ga kamfanin wayar da kake amfani da layinsu, ko kaje ofishinsu kawai zai fi sauki, ka sanar da su cewa kana son a saita maka wayar don ka rika mu’amala da fasahar Intanet, za su saita maka, kyauta.  Da fatan an gamsu.


Assalamu alaikum, Baban Sadiq ina yi maka fatan alheri. Dan Allah mene ne banbancin MMS da kuma SMS a wajen tura sakwanni? Daga Yusuf Muhammad Gagarawa, Jihar Jigawa, Najeriya. 08061123657, 08154627050

Malam Yusuf muna godiya da addu’a. Haruffan MMS na nufin “Multimedia Message” ne, wato tsarin aika sakonni na murya ko hotuna ko bidiyo.  A daya bangaren kuma, haruffan SMS na nufin “Short Message Service” ne, wato tsarin aika gajerun sakonni rubutattu ta wayar salula. Bambancin da ke tsakaninsu dai na yanayi ne, da kuma hanyar da suke bi wajen aikawa.  MMS dai ta kunshi sauti ne da hotuna masu motsi da daskararru, a yayin da SMS ta kunshi rubutattun sakonni kadai.  Tsarin MMS na bin tafarkin yanayin sadarwar wayar salula mai amfani da fasahar Intanet ne, a yayin da tsarin SMS ke amfani da tsarin yanayin sadarwar wayar salula kadai.  Don haka ko babu tsarin Intanet a wayar salula za ka iya aika sakon SMS, amma tsarin MMS dole sai da tsarin Intanet a tare da ita.  Da fatan an gamsu.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. ALIYU IBRAHIM says

    ILIMI NADA DADI ?

Leave A Reply

Your email address will not be published.