Fasahar “Digital Currency”: Yanayi Da Siffofi

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 16 ga watan Afrailu, 2021.

360

Yanayi da Siffofi

Daga bayanan da suka gabata kan ma’anonin wadannan nau’ukan kudade, za mu fahimci cewa suna dauke ne da siffofi na musamman da suka bambanta su da takardun kudaden dake hannunmu, wadanda hukumomin kasashenmu suka samar kuma suke lura da karuwa ko raguwarsu, don tafiyar da tsarin hada-hadar kudaden dake kasashensu.  Shahararrun daga cikin wadannan siffofi dai su ne kamar haka:

Mahallin Samuwa da Gudanuwa

Nau’ukan kudaden zamani ana iya samar dasu ne kawai ta hanyar sarrafa bayanai a kafafen sadarwa na zamani ko Intanet.  A nan ake samar dasu ta hanyar “hako” su, wato: “Mining” kenan.  Bayan hako su, ana amfani da mahalli na musamman, wanda rumbun adana bayanai ne da aika su na musamman a Intanet, wajen aikawa, da karba, da adanawa, da kuma aiwatar da cinikayya dasu.  Wannan ma’adana kuma ita ake kira: “Blockchain”, kuma ana san nan gaba kadan, kusan dukkan kamfanonin duniya dake Intanet, da manyan bankunan kasashen duniya, da bankunan kasuwanci na duniya, da kuma hukumomin gwamnatocin duniya, duk za a koma amfani da wannan mahalli ne na “Blockchain”.  Wannan ya faru ne saboda cikakken tsari da tsaro da kintsi da kuma amincin da yake dauke dasu.

‘Yancin Samarwa

Sabanin kudaden takardu da Zahiri, nau’ukan kudin Intanet kowa na iya samar dasu.  Da zarar ka san yadda zaka iya hako su, shikenan.  Kana iya samar da naka mahallin ma, wato: “Blockchain”, don gudanar da cinikayyar wasu kudaden ma a Intanet.  Wannan yasa ake da ire-iren wadannan kudade masu dimbin yawa a Intanet.  Kamfanoni na samar da nasu, da shaguwan saye da sayarwa na samarwa don habaka tsarin alaka tsakaninsu da masu hulda dasu.

Babu Tsarin Killacewa da Kayyadewa

- Adv -

A yayin kowace kasa take da nata nau’in kudin, kuma babban bankin kasar ne ke tafiyar da samuwa da yada shi a kasar, tare da hana kowane dan kasar kirkirar wani abu mai kama da kudin kasar, a duniyar Intanet ba haka abin yake ba wajen samarwa da kuma gudanar da sha’anin kudaden zamani.  Babu wata hukuma a duniyar Intanet da aka dora wa alhalin lura da wadannan kudade da wasu ke samarwa, ko kadan.  Wannan ke nuna duk wanda ya cuceka wajen hada-hadar kasuwanci da ire-iren wadannan kudade a Intanet, babu inda za ka kai koke don a kwatar maka hakkinka.  Amma da ace kudin kasarku ne, da zarar wani bankin kasuwanci ya cuceka kana iya kai kara ko koke wajen babban bankin Najeriya misali, don a kwatar maka hakkinka.  A shekarar da ta gabata misali, babban bankin Najeriya ya tilasta bankunan kasuwanci (Commercial Banks) biyan zunzurutun kudade sama da naira Tiriliyan uku, wadanda mutane suka kai koke akansu.  A duniyar Intanet, idan kana hada-hada da wadannan kudade, babu irin wannan tsari.  Dabararka ce za ta fissheka.

Basu Da Kima a Karankansu

Kamar sauran kudade, ba su da kima a karankansu.  Kimarsu na ga kudaden da aka gindaya su gare shi ne.  A halin yanzu duk galibin wadannan kudade ana kimanta su ne da dalar Amurka.  Tunda ita ce nau’in kudin da a duk duniya ake kimanta darajar kudade da ita.  Darajar kudin zamani na “Bitcoin” a yanzu ya doshi dalar Amurka dubu sittin.  Duk wannan farashin kwandala daya ce ta bitcoin.  Amma da za ka dauke dalar amurka da kudin kowace kasa ma, bitcoin zai rasa kimarsa gaba daya.  Ba za ka iya sayan komai dashi ba.

Babu Su a Zahiri

Wannan ita ce mafi shahara cikin siffofin wadannan kudade.  Kudade ne da ake iya ganin lissafin adadinsu a kan kwamfuta ko wayar salula ko na’urar sadarwa.  Kuma ta nan kadai za ka iya aikawa da karbarsu, da sayen hajoji a shagunan dake karbansu, ko a sayi hajarka a biyaka dasu.  Idan kana bukatar makwafinsu a Zahiri, sai dai ka sayar dasu ta hanyar da ka mallake su, idan aka biyaka da dalar amurka ko kudin wata kasa, sai loda a taskar ajiyarka ta banki, daga nan ka cire su, idan hukuma bata hana ba a kasar da kake.  Amma da za ka mallaki bitcoin, ko etherium, ko Litecoin ko duk wani nau’in kudi makamantansu, ko miliyan nawa ne, muddin baka sayar dasu ba, to, ba ka iya mallakarsu a zahirin rayuwa – sai in wasu hajoji zaka saya a shaguna dake Intanet.

Ba Bukatar Tantacewa ta Zahiri

Sabanin tsarin hada-hadar kudade na Zahiri, inda za ka je banki sanya kudi ko cire kudi daga tasrkarka, sai an tantanceka, ta hanyar hoto da katin kasa ko lasisin tuki, a duniyar Intanet ba haka lamarin yake ba.  Kana iya bude taskar ajiya a Intanet don ta’ammali da wadannan kudade ba tare da ka bayar da sunanka na asali ba, balle adireshin gidanka ko wani abu makamancin haka.  Karkashin wannan tsari, duk wanda za ka yi cinikayya dashi wajen saye ko sayar da kudadenka, ba zai sanka, ba kuma zai san daga wace kasa kake ba.  Kamar yadda kaima ba za ka sanshi ba, in dai ba wanda a zahirin rayuwa ka sanshi bane.  Ba kuma za ka iya sanin daga wace kasa yake ba.  Wannan ya saba wa tsarin hada-hadar kudade a zahirin rayuwa.  Domin dole ne a iya tantance abokin hulda, ta kowane hali.  Wannan tsari shi ake kira: “Know Your Customer”, ko “KYC” a gajarce.

Wadannan su ne shahararrun siffofin kudaden zamani da ake ta’ammali dasu a Intanet.  Sashi na gaba zai mana bayani ne kan nau’ukan kudaden “Cryptocurrency”, wanda su ne daman madogaran bincikenmu gaba daya, da tsarin kowanne daga cikinsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.