Tsarin Fasahar Faifan DVD (2)

A wannan mako in Allah Ya yarda za muyi tsokaci ne kan tsari da na’ukan fasahar faifan DVD.

255

Matashiya

A makon jiya mun fara bayani kan asali da samuwar fasahar faifan DVD, wato: “Digital Versatile Disc”, da dalilan da suka sa kamfanonin sadarwa da qere-qeren kayayyakin lantarki irin su Toshiba, da Sony, da Philips suka samar, ta haxin gwiwa da kamfanonin kwamfuta irin su IBM, da Apple, da Microsoft da dai sauran makamantansu.  A wannan mako in Allah Ya yarda za muyi tsokaci ne kan tsari da na’ukan fasahar faifan DVD.

Tsari da Kimtsin Fasahar Faifan DVD

Cikin shekarar 1995 dai aka tabbatar da kundin fasahar faifan DVD, bayan daidaituwar da aka samu tsakanin kamfanonin lantarki, kamar yadda bayani ya gabata a makon jiya.  Wannan sabuwar fasaha ta zo da nau’ukan sauye-sauye masu armashi idan aka kwatanta ta da wacce ta gabaceta a wancan lokaci na baya.  Kundin dake xauke da xaukacin siffofi da tsarin fasahar faifan DVD, wato: “DVD Book”, ya tsara yadda faifai zai kasance.

Da farko dai fasahar faifan DVD na xauke ne da mizanin ma’adana mai girman 4.7GB, wato za a iya zuba bayanai sama da tiriliyan huxu da xigo bakwai kenan.  Sannan wannan faifai ya kasu kasha biyu.  Akwai mai falle xaya, wato: “Single Layer DVD” kenan.  Sai kuma mai xauke da tagwayen falle, wato: “Dual Layer DVD”.  Wannan nau’i na biyu yana xauke da mafi girman mizani.  Mafi qarancin mizaninsa shi ne wanda ke iya xaukan bayanai tiriliyan takwas da xigo biyar, wato: 8.5GB.

Faifan DVD dai, kamar faifan CD da bayaninsa ya gabata a makonnin baya, an qera shi ne daga gasasshen roba. Kuma anyi amfani da injin vula roba ne don xabba’a waxannan faya-fayai da ximbin yawa cikin qanqanin lokaci.  Wannan inji dai ana kiransa: “Injection Moulding Machine”.  Wannan inji na xauke ne da wani allura mai qarfin gaske, wanda ke huda roba kowane iri ne.  Sai kuma wasu hannaye na musamman, waxanda ke lailaya roba bayan injin ya huda shi.

Nau’ukan Fasahar Faifan DVD

Kamar yadda bayani ya gabata a sama, akwai manyan nau’uka biyu, dangane da siffa ko maxauki da faifan DVD suka zo dashi.  Ta vangaren nau’in bayanan da Faifan DVD zai iya xauka kuma, akwai nau’uka da dama; wasu masu xauke da fallen faifai xaya (Single Layer) ne, wasu kuma masu xauke da tagwayen fallen faifai (Dual Layer).  Kowanne daga cikin waxannan nau’uka yana da kundin dake xauke da bayanin tsari da kintsinsa a kimiyyance.

- Adv -

Akwai nau’in Faifan DVD mai xaukan sauti zalla.  Wannan shi ake kira: DVD-Audio.  Ire-iren waxannan nau’uka suna zuwa ne xauke da waqoqi, kuma idan ka saya, sai dai ka xora su kan na’urar sarrafa DVD, wato: “DVD Player” don sauraron waqoqin, ko a kwamfuta mai xauke da na’urar sarrafa DVD, wato: DVD+R.  Sai nau’i na biyu mai suna: DVD-Video.  Wannan nau’in shi kuma yana zuwa ne da bayanan bidiyo zalla, musamman daga kamfanonin fina-finai na duniya, irin su: “Warner Bros” da sauransu.  Waxanna nau’uka biyu ba a iya goge abin da ke cikinsu, muddin aka taskance bayanan dake ciki tun daga kamfanin da ya qera su.

Kashi na uku kuma shi ne nau’in DVD-ROM, wanda ke zuwa galibi xauke da babbar manhajar kwamfuta (ko na kamfanin Microsoft ko Apple, misali).  Ko wasu nau’ukan mamhajojin kwamfuta.  Abin da kalma ko haruffan “ROM” ke nufi shi ne: “Read Only Memroy”.  Shi ma idan aka saya, ba a iya goge bayanan dake ciki ko kaxan.  Sun zauna kenan, daram – zuwan sojan badakkare.  Kashi na hudu shi ne: DVD-R, wato: “Recordable” kenan.  Galibi irin wannan nau’in DVD kan zo ne holoqonsa; babu komai a ciki.  Ana saya ne don zuba bayanai a ciki da nufin taskance su kaxai, ko taskance su da kuma saurare ko kallo idan nau’in hoto ne ko bidiyo ko kuma hotuna, misali.  Su ma, da zarar ka taskance bayanan dake cikinsu, to, ba ka iya goge su, ko kaxan.

Sai kashi na biyar, wanda ake kira: DVD-RW, wato: “Rewritable” kenan.  Abin da wannan kalma ke nufi shi ne, kana iya goge bayanan da ka zuba a ciki, sannan ka sake zubawa ko taskance wasu.  Shi ma wannan nau’in DVD ana sayansa ne holoqo; babu komai a ciki.  Idan ka saya, sai ka zuba bayanan da kake buqata.  In kaga dama kuma ka goge su kai tsaye.  Sai kashi shida da ake kira: DVD-RAM, wato: “Random Access Memory”.  Wannan nau’i na DVD kuma ana amfani dashi ne a kwamfuta kaxai.  Faifai ne na DVD wanda ke matsayin ma’adanar wucin-gadi, wato: “RAM” kenan.  Idan aka xora wa kwamfuta, ba a cirewa sai an kashe, misali.  Shi ma ba a iya goge bayanan dake cikinsa.

Bayan waxannan, akwai waxanda suka kevanci kwamfuta ne zalla.  Waxannan su ne masu tagwayen faifai, wanda mizaninsu mafi qaranci shi ne tiriliyan takwas da xigo biyar (8.5GB).  Daga ciki akwai nau’in DVD+R, wanda shi kuma yakan zo ne da bayanai a cikinsa, amma kuma a kwamfuta kaxai ake iya sarrafa su.  Kuma ba a iya goge abin da ke ciki, saboda a kulle suke.  Kusan iri xaya da nau’in DVD-R kenan, bambancinsu kawai shi ne, shi DVD-R kanzo holoqo ne, babu komai a ciki.  Sai kuma nau’in DVD+RW, wanda shi kuma ke zuwa da bayanai a ciki amma a kwamfuta ake iya sarrafa su.  Waxannan nau’uka dai masu xauke da tagwayen faifai ne, wato: “Dual Layer DVD”.  Suna amfani ne da wani tsari mai suna: “Opposite Track Path”, wajen sarrafa bayanan sauti ko bidiyo da suke xauke dashi.  Idan faifan farko ya qare, nan take sai wannan tsari na OTP yayi farat ya tsallaka zuwa titin dake xauke da faifan bayanai na biyu, don ci gaba.

Girma da Yanayi

Ta vangaren zahirin siffa, faifan DVD ya kasu kashi biyu, nan ma.  Kashin farko su ake kira: “MiniDVD”, masu qaramin ruwa kenan.  Galibi basu shahara a qasashenmu ba, savanin na biyun.  Nau’in MiniDVD sun kasu kashi 4 ne.  Akwai MiniDVD-1, mai girman mizani 1.4GB.  Sai MiniDVD-2 mai girman mizani 2.65GB.  Sai MiniDVD-3, mai girman mizani 2.92GB. Sai kuma na qarshe, wato MiniDVD-4, wanda ke xauke da mizani 5.31GB.  Daga nau’in MiniDVD-1 har zuwa MiniDVD-4, duk girman jikinsu xaya; mizani ne kawai ya bambanta su.  Faxinsu duk bai wuce santimita 8 (8cm).

Nau’i na biyu kuma su ake kira: “Standard DVD”; su kuma sun kai guda biyar, ta la’akari da mizaninsu.  Akwai DVD5, mai mizanin 4.7GB.  Wannan shi ne wanda ya shahara a qasashenmu.  Sai kuma DVD9 mai girman mizani 8.54GB.  Wannan galibi akan same su ne xauke da manhajojin kwamfuta.  Sai DVD10, wanda ke xauke da mizani 9.40GB.  Sai DVD14 mai xauke da mizani 13.24GB.  Sai na qarshe, wato DVD18 wanda ke xauke da girman mizani 17.08GB.  Su ma, kamar kashi na farko, daga DVD5 zuwa DVD18, duk girmansu xaya.  Mizani ne kaxai ya bambanta su.  Faxinsu ya kai santimita 12 (12cm).

Tsarin Sarrafa Bayanai

Fasahar faifan DVD ya fi CD inganci da kuma gaggawar sadar da bayanai wajen taskancewa, ko wajen nunawa da bayyanawa.  A yayin da fasahar CD ke cillo haskensa don taskance bayanai a tazarar nanometer 780 (780nm), fasahar DVD na cillo haske ne a tazarar nanometer 650 (650nm).  Dukkansu suna amfani ne da hasken lantarki nau’in leza, mai launi ja.  Sinadaran dake cikin hasken ya xara karfin sinadaran hasken infra-red.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.