Sakonnin Masu Karatu (2011) (4)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

69

Assalamu alaikum. Baban Sadiq ina fatan kana lafiya, yaya aiki?  Ko za ka yi mana karin bayani kan shafin intanet na manyan harsunan Afrika; an bude ne a halin yanzu, ko nan gaba ne za’a bude?  In dai an bude, yaya adreshin wanan shafin take? Ka huta lafiya.  Daga Abdullahi Zaria.

Malam Abdullah, a halin yanzu akwai shafukan Intanet da ke dauke cikin manyan harsunan Afirka ai, irinsu Suwahili da Hausa da sauransu.  In har kana bukata, bayanai kawai za ka nema masu alaka da harshen da kake so, za ka samu. Ban san adireshin wani shafin Intanet na harshen Suwahili ba, amma akwai na harshen Hausa tinjin a Intanet.  Da fatan ka gamsu.


Salam Baban Sadik, Ina tambaya ne kan duk lokacin da zan kalli wani launin hoto mai motsi wato bidiyo, sai a nuna min cewa sai na yi downloading din adobe flashplayer kuma ko da nayi hakan ba na samun damar ganin bidiyo din. Yaya zan yi? Allah ya kara lafiya.  Maikudi marafa sagagi. aleemarafa@yahoo.com

Abin da ke faruwa shi ne, duk wani abin da za ka iya mu’amala da shi a Intanet ta hanyar wayar salularka, akwai wani manhaja ko masarrafa da aka tanada masa.  Idan wannan masarrafar bata samu ba, babu yadda za a yi ka iya mu’amala da shi.  Shi “Adobe flash player” ‘yar karamar masarrafa ce da ke taimakawa wajen kallon hotuna masu motsi, wato bidiyo, idan ba ka da wannan masarrafa, ba za ka iya ba.  Idan kuma kana da masarrafar, dole sai da ma’adanar bayanai mai dan girma a wayar, wato “Storage”, kamar “Memory Card”, ko ya zama wayar tana da ma’adana mai dan yawa. Domin a duk sadda ka budo wani bidiyo za ka kalla, wayar za ta saukar maka dashi ne cikin ma’adanarta kafin ka fara kallo, in kuma babu isasshen ma’adana, ka ga akwai matsala kenan.  Da fatan ka gamsu.


- Adv -

Assalamu alaikum Baban Sadiq, barkan ka da war haka. Da fatan kana lafiya, Allah Yasa haka, amin. Na kanyi lilo (Browsing) ta opera a wayata ‘kirar Nokia. Amma da zarar na fara, wani lokaci sai ya fidda min wasu kalamai kamar haka: “Application Erro: Out of Memory Error. Java/Lang/OutOfMemoryError” Daga karshe sai wayar ta sake kunna kanta. Shin hakan me yake nufi ne? Kuma ko akwai wata hanyar da za’abi a magance aukuwar hakan? Wassalam. Daga Uncle Bash Jimeta-Yola. bysalihu@gmail.com, 07037133338.

A gaida Uncle Bash namu.  Wato matsalar da wayar ke fuskanta dai shi ne rashin isasshen ma’adanar sarrafa bayanai, wato “Memory” kenan.  Sai ka duba, akwai tabbacin wayar an cike ta da bayanai na sauti ko bidiyo, ta yadda ta makare, babu sauran wurin numfashi a gare ta.  Idan haka ta kasance, dole ta kashe kanta don ta sake farfadowa ko za ta samu wurin numfasawa.  Wato galibin na’urorin sadarwa suna da ma’adanai guda biyu ne. Akwai babbar ma’adana, wacce ke dauke da babbar manhajarta, wato Hard Disk kenan, ko kuma ROM (Read Only Memory).  Amfanin wannan ma’adanar shi ne taskance dukkan manhajoji da masarrafan da na’urar ke amfani da su, a mace. Sai ma’adana ta biyu, wacce ake kira RAM (Random Access Memory), wadda ke aikin adana masarrafai ko manhajojin da aka kunna kuma ake mu’amala da su. 

Misali, idan ka kunna wayar salularka, da zarar ka budo menu a misali, sai bayanan su taso daga ROM zuwa RAM. Ma’adanar RAM kamar farfajiya ce ko falo, inda duk masarrafan da aka kira su suke zama, a gama abin da ake yi da su, sannan su koma inda suka fito su kwanta. To idan kwamfuta ce, ba ta da matsala sosai, domin kowanne cikin ma’adanan nan guda biyu yana da nashi bangare. Amma a wayar salula, ma’adana guda daya ce ake gutsira ta.  Idan ka shake wayar salularka da hotuna da bidiyo da wakokinsu Mai Asharalle a misali, sai ta kasa samun wurin da za ta ajiye wasu manhajojin idan ka kira su kana son yin amfani da su.  Don haka, ka rage yawan bayanan da ka taskance a wayar, ko kuma ka kara mata ma’adana ta hanyar sanya mata “Memory Card.”  Da fatan Malam Bash ya gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadiq, dan Allah meye alakar Bluetooth da USB Cable? Godiya muke. Daga Salisu Nagaidan Jama’are: 08063461480

Malam Salisu ai babu wata alaka a tsakaninsu sai alakar kasancewa hanyoyin shigar da bayanai ne su ko hanyar mikawa, zuwa wayar salula ko kwamfuta.  Ita fasahar Bluetooth tana aiki ne da tsarin sadarwa ta wayar iska, wato “Wireless Communication System,” a yayin da Wayar USB kuma ke amfani aikawa da sakon bayanai ta hanyar damfaruwa a jikin wayar salula ko kwamfutar da ke aikawa ko karba.  Da fatan an gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.