Sakonnin Masu Karatu (2011) (2)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

67

Salamu alaikum Baban Sadik, Tambayata itace, ko adadi nawa ne da kamfanoni Manhajar Imel a Duniya? Daga: Aliyu Mukhtar Sa’idu (IT) Kano Email: aliitpro2020@yahoo.com 08034332200 / 08186624300.

Kamfanonin manhajar Imel suna da yawa a duniya.  Da farko dai manhajar Imel nau’i biyu ne; akwai wanda ke ta’allake da fasahar Intanet.  Wadannan su ake kira “Internet Mail Program”, kuma ire-irensu sun hada da na kamfanin Yahoo, da Hotmail, da Gmail da dai sauransu.  Sannan akwai manhajar Imel wacce ake loda wa kwamfuta don amfani da su a tsarin sadarwa na gajeren zango ko dogon zango, kamar yadda bayanai suka gabata a sama.  Ire-iren wadannan manhajar Imel ba su bukatar samuwar Intanet a kwamfuta kafin aika ko a karbi sako ta hanyarsu.  Su ma akwai su da yawa; akwai Outlook na kamfanin Microsoft, akwai Thunderbird na kamfanin Mozilla da dai sauransu.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, ina son in saita Imail na wayar salula Nokia x2-01. In na tura musu sai a ce “Invalid Password”, yaya zan yi? – Daga Legas

Akwai alamun dayan abu biyu.  Ko dai ba ka da tsare-tsaren kamfanin waya mai sawwake hanyar sadarwa, wato “Configuration Settings,” ko kuma ka mance kalmomin iznin shiganka na Imel.  Idan har kana iya mu’amala da Intanet a wayar, to, ba matsala, watakila ka mance kalmomin iznin shiganka ne, wato “Password.”  Amma idan ba ka iya mu’amala da Intanet gaba daya a wayar, dole ne ka bukaci kamfanin wayarka ya aiko maka da wadannan tsare-tsare.  Da fatan an gamsu.


Salam, ina jin dadin rubutunka. Don Allah ina son ka yi min bayanin yanda zan yi amfani da faifan dish wajen shiga yanar gizo. Allah ya kara basira. Daga N. I. Usman

Malam Usman hanyar amfani da dish wajen zuko tsarin sadarwa ta Intanet zuwa jikin kwamfuta ba abu bane mai sauki, domin yana bukatar kwarewa a fannin mu’amala da tsarin sadarwar tashoshin tauraron dan Adam, da kuma sanayya kan tsarin sadarwa ta kwamfuta.  Bayan haka, akwai wasu kalmomin sirri da ake shigarwa, wadanda kuma ke caccanzawa a lokuta daban-daban. A takaice dai ba abu bane mai yiwuwa ta dadi, domin yana bukatar dabaru nau’uka daban-daban. Idan akwai kwararru masu gyaran tashoshin tauraron dan adam kana iya tuntubansu.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, wai don Allah wace shekara ce aka kirkiro kwamfuta? Kuma wa ya kirkirota? Kuma dan wace kasa ne? Sannan wane kamfani ne a yanzu ya fi kera kwamfuta? Wacce tafi kowacce tsada? Kuma da gaskene akwai kwamfuta marar malatsi ko daya wato touch screen?  Na gode. Daga Ibrahim Aliyu Marcury

Malam Ibrahim a gaisheka.  Dangane da wanda ya kirkiri kwamfuta, babu mutum guda daya da za a ce shi ne ya kirkiro kwamfuta.  Domin kuwa na’ura ce mai dauke da bangarori da yawa. A takaice dai masana sun nuna cewa kwamfuta ta samo asali ne daga na’urar kidaya, wato “Counting Machine”, irinsu “Abacus” da dai sauransu, kuma wanda ya yi fice dai cikin wannan fanni shi ne Charles Babbage.  Bayan shi, akwai kwararru masana fannin lissafi yan kasar Sin da suka kirkiri irin wannan fasaha.  Kuma daga wannan fasaha ce aka samu fikira da tunanin kirkirar kwamfuta.  Babu wanda za a ce shi ne ya kirkireta shi kadai, sannan babu wata shekara da za a ce lokacin ne kwamfuta ta samu kai tsaye.  Saboda kamar yadda na fada a farko, tana dauke ne da bangarori daban-daban.

- Adv -

Akwai bangaren gangar-jiki da bangaren manhajarta.  Kowannensu yana da nashi tsari da tarihi.  Akwai kwamfutoci nau’uka daban-daban a yanzu kam, har da marasa malatsi kamar yadda kaji.  Babu wani kamfani har wa yau da za a ce shi ne yafi kera kwamfutoci, da’iman.  Ya danganci lokaci ne kawai.  Akwai kamfanonin da ke gina manhajar kwamfuta zalla, irinsu kamfanin Microsoft, kuma shi ne kamfanin da ke kan gaba dangane da abin da ya shafi manhajar kwamfuta. 

Akwai masu kera gangar-jikin kwamfuta zalla, tare da masarrafar da ke tafiyar da su, irinsu HP, da Dell, da Gateway, da IBM da dai sauransu.  Kwamfutar da tafi kowacce kudi ita ce wacce tafi su yawan mizani, da ingancin masarrafar gudanarwa (Processor), da ingancin kira, da kuma shaharan kamfanin da ya kera kwamfutar.  Samun wadannan sifofi a jikin kwamfuta guda daya ba abu bane mai yiwuwa a yau.  Idan aka samu wacce tafi ingancin masarrafar gudanarwa, za ka samu akwai wacce ta fi ta girman mizani. Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadiq, muna karuwa da wannan shafi Allah ya saka da alheri amin.  Ina neman shawararka wajen bude shafi a Dandalin Facebook; wanne layin sadarwane ya fi, tsakanin layin MTN da Glo da Airtel?  Godiya nake sai na ji ka. Daga salisu Nagaidan mai biredi, Jama’are Jihar Bauchi 08063461480

Malam Salisu muna godiya kamar kullum da addu’o’inku.  Allah bar zumunci, amin.  A gaskiya ba zan iya ce maka ga layin da yafi inganci ba, don ban taba amfani da su duka a dukkan jihohin Najeriya ba.  Abu na biyu kuma shi ne, ya kamata ka san cewa ingancin sadarwar wayar tarho da ta Intanet, duk suna ta’allaka ne da inda kake zaune.  Ba wai abu bane wanda yake bai daya.  Misali, tsarin sadarwar wayar salula a galibin lokuta sun fi karfi da inganci a manyan birane fiye da kauyuka.  Ko kusa ba za ka hada ba.  Sannan a manyan biranen ma sun fi karfi a cikin gari, idan ka kwatanta da karfinsu a wajen birni, kafin a shiga kauyuka.  Don haka sai ka yi la’akari da bayanan da nayi a sama, duk wanda ya dace da yanayinka sai ka dauka.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum, shin wai dole ne duk wanda zai bude shafin Facebook sai yana da rajistar Imel? Bashari I. Gumel

Malam Bashari wannan zance haka yake.  Sai kana da adireshin Imel, idan kuwa ba haka ba, ba za a baka damar budewa ba.  Sai a yi kokari a bude, don a samu damar shiga da damawa da sauran jama’a.


Baban sadik ya aiki? Ina da sakonnin tes a wayata, kuma ina son in canza wayar, ko akwai yadda zan iya kwafar su zuwa wata wayar?  Kuma me ya sa 8 Gigabyte ba ya yi a wasu wayoyin? A. W. Ayagi

Dubun gaisuwa ga Abul Waraqaat.  Ya danganci irin wayar da kuma wadda ake son canzawa.  Idan dukkansu wayoyin Nokia ne, ai ba matsala Malam Rabi’u.  Idan ka kunna sabuwar, sai ka je cikin “Menu” inda aka rubuta “Switch”, sai ka matsa, za a budo maka hanyoyin da ake gudanar da wannan aiki cikin sauki. Ba shi da wahala.  Abin da ya rage shi ne, dole ka kunna fasahar Bluetooth din tsohuwar wayar, wacce kake son kwaso kayayyakinka daga cikinta.  A haka sabuwar za ta kwaso maka dukkan bayananka, daga sakonnin tes, zuwa na murya da bidiyo da hotuna.  Bayan haka, mizanin ma’adanar bayanai na 8Gigabyte ba lallai bane ya yi a jikin kowace wayar salula.  Kowace waya akwai iya girman mizanin da za ta iya dauka, wanda shi yayi daidai da karfin masarrafar gudanarwarta. Da fatan Abul Waraqaat ya gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.