Matsalolin Wayar Salula (1)

Kashi na 22 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

210

Matashiya

Ba mu gushe ba cikin bayanan da muke kawowa kan wayoyin salula tun shekarar da ta gabata. A baya idan mai karatu bai manta ba, mun kawo bayanai ne kan Alakar Wayar Salula da Sauran Kayayyakin Sadarwa, inda muka nuna yadda ake mu’amala da wayar salula ta hanyar wayoyin shigar da bayanai nau’in USB, da fasahar Bluetooth da fasahar Infra-red, da dai sauransu.  Muna kawo wadannan bayanai ne don baiwa masu karatu gamsuwa iya gwargwado (ba cikakkiyar gamsuwa ba, don ba mai iya gamsar da bukatun dan adam sai Allah), ganin musamman tambayoyi da bayanan neman karin bayani sun ki karewa a wannan shafi har kullum.

Uzurin da nake wa masu karatu shi ne, don ganin wayoyin salula na cikin abin da a yau aka wayi gari ana aiwatar da sadarwa ne dasu – dare da rana safe da yamma.  Don haka duk yadda na kai da kokarin ganin na yi bayanai masu gamsarwa don toshe hanyar zuwan wasu sakonnin ko tambayoyin, ba zai yiwu ba.  Domin rayuwa ce da ke ci gaba da gudanuwa. Yayin da wannan matsala ta kau, wata matsalar ce za ta maye gurbinta.  Illa dai kamar yadda na sanar a baya, duk wata tambaya da ta ci gaba da maimaituwa, to, ba zan kara amsa ta ba.  Don idan muka ci gaba a haka, to baya za mu ci gaba da komawa.

Daga cikin maimaitattun tambayoyi akwai tambaya kan yadda ake shiga Intanet ta wayar salula, da tambaya kan yadda ake shiga ko yin rajistan shafin Facebook ta wayar salula, da tambaya kan yadda ake bude adireshin Imel ta wayar salula; duk na daina amsa su. Sai dai a madadin haka, akwai wata hanyar tunatarwa da zan bullo da ita da za ta maye gurbin amsar wadannan tambayoyi.  Sai a dakace ni.

A yau muna dauke ne da bayanai kan Nau’ukan Matsalolin Wayar Salula.  Ma’ana, me da me ke haddasa samuwar matsala ga wayar salula?  Ba wai yawan matsalolinta nake nufi ba.  Domin ba zan iya haddade su ba, saboda yawansu.  Ka’idar kawai ita ce mu san abin da ke haddasa wa wayar salula matsaloli, don mu kauce musu.  Rigakafi, inji Malam Bahaushe, ya fi magani.  Dukkan matsalolin wayar salula suna samuwa ne ta dayan hanyoyi guda uku.  Ko dai masu alaka ne da gangar-jikin wayar – kamar karyewa, da fashewa, da tsinkewar wayoyin da ke ciki, da datti, da jikewa – ko suna da alaka ne da ruhin wayar – kamar samuwar kwayoyin cuta a ruhinta, da dogon suma, da kuma gajeren suma – ko kuma a karshe, ya zama masu alaka ne da yanayin sadarwa – wato Network Service Hitch kenan.  A halin yanzu dai ga bayanai nan filla-filla:

- Adv -

Matsalolin Gangar-jiki

Matsalolin wayar salula masu alaka da gangar-jikinta suna da yawa sosai, ya danganci yadda mai wayar ke mu’amala da ita, da yadda yake adana ta, da yadda yake sarrafa ta, da kuma yadda yake lura da wayar.  Da farko dai akwai matsala mai alaka da karyewan wani bangaren jikin wayar, kamar karyewan marfin wayar ta baya; hakan na iya sa batir ya rika faduwa.  Idan haka ta faru ba za a iya amfani da wayar ta dadi ba, don dole za ta rika mutuwa idan batirin ya fadi kasa.  Haka idan marfin gaban ne ya karye, wannan na iya sa maballan wayar (wato Keypad) su rika faduwa kasa, ba za su matsu ta dadi ba, balle a iya aiwatar da kira ko rubuta tes.  Bayan haka, duk wayar da wani bangaren marfinta ya karye, to abu mafi a’ala shi ne a canza, in kuwa ba haka ba, matsala mai girma na iya aukuwa.

Sai matsaloli masu alaka da fashewa.  Kamar fashewar fuskar wayar (wato Screen kenan), yana iya sa wayar ta dauke, a daina ganin bayanan da ke fuskar, balle a yi mu’amala da ita yadda ake so.  Idan fuskar waya ta fashe ko ta tsage, abin da ya fi kawai shi ne a canza.  Tabbas yana da tsada, musamman idan babbar waya ce, amma canzawar shi ne mafi alheri, don kauce wa yaduwar matsalolin zuwa wasu sassanta.  Haka kuma akwai matsalar tsinkewar wayoyin da ke jone da bangarorin wayar daga ciki, sanadiyyar faduwa a wuri mai tsauri – kamar dutse, ko marmara, ko kwalta, ko jikin kankare  a misali.

Sannan, iya girma da nauyin waya, iya yadda za ta ji jiki idan ta fado kan wuri mai tsauri.  Wasu wayoyi musamman irin Nokia, sukan wargaje gaba daya idan suka fadi, har ka tattaro su ka jona su sannan wayar ta ci gaba da rayuwa. Wannan na faruwa ne saboda ingancin kira da kamfanin ke tabbatarwa. Amma kuma dole ne a rika kiyayewa.  Domin akwai ranar da idan ta sha kasa, ko an hada ta fa ba za ta farfado ba.  Idan wayoyin da ke rike da wasu bangarorin waya, musamman lasifika, da fuskar wayar, da bangaren jiyar da magana (wato Mouthpiece), ko cibiyar cajin waya (wato Charging Point) suka tsinke, to wadannan bangarori na iya daina aiki.

Ma’ana, ko dai a kira ka, amma ka kasa jin mai kira, ko kana ji amma ba a jinka, ko ka sa wayar a caji amma ta ki yi, ko kuma ka kasa ganin bayanan da wayar ke nunawa a fuskarta, saboda babu sadarwa a tsakanin bangarorin wayar, sanadiyyar tsinkewar wasu wayoyi daga ciki.

Wasu matsalolin kuma na samuwa ne sanadiyyar datti da ke taruwa a karkashin marfin wayar ko maballanta (wato keypad), ko wasu daga cikin kafofi kanana da ke jikin wayar.  Idan datti ya toshe tsakanin gangar-jikin waya daga kasa, da hakoran maballan shigar da bayanai, to ba za ka iya shigar da lambobi ba, ko rubuta tes.  Dole sai an kai wa mai gyara.  Haka idan wayar ta fada cikin ruwa, ko ka ajiye ta a wani wuri mai danshi na tsawon lokaci, tana iya daukewa, har sai ka shanya.  Idan kuma ruwan ya shige ta sosai, to tana iya daukewa.  Don haka sai a kiyaye.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.