Sakonnin Masu Karatu (2011) (15)

Ci gaban sakonnin da na fara amsa makon jiya.  A sha karatu lafiya.

58

Assalaamu Alaikum Baban Sadik, ina da matsala da wayata wajen yin tes; duk sa’adda na aika tes, ba ya tafiya, sai ya makale a wayar. Amma kuma mutane kan aiko mani tes, babu matsala.  Na kai wayar wajen masu gyara, sun kasa gano abin da ke damunta.  Don Allah a taimaka mini.  –  Umar daga Sakkwato.

Malam Umar, matsalar da ke damun wayarka ba babbar matsala bace, sai dai tasirinta na da girma wajen hana ka sadarwa ta hanyar sakonnin tes, kamar yadda ka gani.  Da farko dai yana da kyau ka san cewa kowane Katin SIM na zuwa ne da saitin hanyoyin sadarwa nau’uka uku; da hanyar sadarwa ta murya, wato Voice Communication, sai hanyar sadarwa ta bayanai, wato Data Communication, bangare na uku kuma shi ne hanyar sadarwa ta rubutacciyar sako, wato tes kenan.  Wannan bangare na karshe shi ake kira Short Message Service, ko SMS a gajarce, kuma daga nan ne kake samun matsala wajen aikawa da sakonnin tes.

Da zarar ka sanya katin a cikin wayarka, sai wadannan tsare-tsare su shige cikin wayar baki daya, ba sai ka gyatta su da kanka ba.  Duk sa’adda aka kira ka, sai tsarin hanyar sadarwar murya ta yi aikinta, wajen hada ka da mai kira.  Idan yanar gizo za ka shiga, ko aikawa da bayanai ta hanyar fasahar Bluetooth ko Infra-red, duk tsare-tsaren za su daidai kansu.  Haka idan ka tashi aikawa da sakon tes, akwai lambobin tashar sadarwar tes, wato Message Center Number, kuma kowane kamfanin wayar sadarwa a duniya na da nashi lambobin da suka sha bamban da na wasu kamfanoni.  Duk sa’adda aka samu matsala ka goge lamba daya daga cikinsu, ko ka kara wata lamba, to, ba za ka iya aikawa da sakonnin tes ba.  Don haka matsalar da ka samu kanka ciki kenan.  Ga abin da za ka yi nan:

Idan karamar waya ce kake amfani da ita, kowace iri ce – ko Nokia, ko Samsung, ko LG da dai sauransu – sai ka shiga Menu, ka je Message, ka gangara inda aka rubuta Message Settings, ka shige ciki. Sai ka gangara inda aka rubuta Message Centers, ko kuma Center Numbers, sai ka matsa.  Za ka ga lambobin.  Idan layin MTN kake amfani da shi, lambobin su ne: +234803000000.  Muddin sifirin nan basu kai shida ba a karshe, to akwai wanda ka goge ko wani ya goge maka cikin kuskure.  Idan kuma suka wuce guda shida, sai ka rage su.  Idan kuma layin Etisalat kake amfani da shi, ga nasu lamboni nan: +2348090001518.  Duk sauran kamfanonin waya suna da nasu su ma.  Sai kowa ya duba nashi ya gani.

Idan kuma kana amfani da babbar waya ce: irinsu Nokia E-Series, ko N-Series, ko Nokia 5320 Xpress Music a misali, za ka samu dan bambanci wajen shiga inda za ka samu wadannan lambobi.  Idan ka je Menu, ka shiga Message, sai ka matsa Options da ke bangaren hagun wayar, za ga zabi kamar haka: Show Open Apps., Create Message, SIM Messages, Cell broadcast, Service Commands, Font Size, Settings, Help, Exit.  Sai kawai ka shiga Settings, ka matsa Text Message, sai ka shiga Message Centers.  Muddin ka gyatta lambobin suka koma yadda suke, to nan take za ka iya aikawa da sakonnin tes.  Da fatan an gamsu.


Salamun Alaikum, tambayata ita ce, me ye bambanci tsakanin wayar Blackberry nau’in Blackberry Touch, da sauran nau’ukan Blackberry?  – Aliyu Muktar Sa’id (IT): 08034332200

Malam Aliyu, bambancin da ke tsakaninsu na tsarin kira ne da kuma kudi.  Ita Blackberry Touch ita ce nau’in wayar Blackberry ta kwana-kwanan nan mai shafaffiyar fuska, wacce ake iya sarrafa ta ta hanyar shigar da bayanai ba tare da matsa ‘yan maballan shigar da bayanai ba kadai, sabanin sauran.  Waya ce mai marfi da ake turawa sama don samun isa ga babban allon shigar da bayanai na musamman.  A takaice dai, wannan nau’in waya ita ce irinta ta farko da aka kera mai marfi, kuma mai hanyar shigar da bayanai kala biyu.  Da fatan ka gamsu.


- Adv -

Salam Baban Sadik, yaya za ayi na hada wayar salula ta da na’urata mai kwakwalwa don shiga yanar gizo? – Tijjani, Malikawa Petroleum, Kano: 08036919511

Malam Tijjani barka da warhaka.  In na fahimci tambayarka da kyau, kamar kana son yin amfani da wayar salularka a matsayin makalutun sadarwa kenan, wato Modem.  Duk wayar salular da ake iya shiga Intanet da ita, to, ana iya amfani da ita a matsayin makalutun sadarwa ga kwamfuta, don shiga Intanet din.  Ya danganci irin wayar da kake amfani da ita.  Idan nau’in Nokia ce, dole sai ka sauko da masarrafar Nokia PC Suite, daga gidan yanar sadarwar kamfanin wayar.  Ko kuma ka yi amfani da faifan CD din da wayar ta zo da shi, akwai masarrafar a ciki.  Aikin wannan masarrafa shi ne taimaka wa wayar salula yin mu’amala da kwamfuta cikin sauki, wajen loda bayanai, ko sauko da su, ko kara wa wayar tagomashi (Update), ko amfani da wayar a matsayin makalutun sadarwa don shiga Intanet da dai sauransu.

Idan ka gama loda wa kwamfutarka wannan masarrafa, sai ka budo, ka je inda aka rubuta Connect to the Internet.  Da zarar ka matsa, za a bukaci ka jona wayarka da kwamfutarka ta hanyar wayar shigar da bayanai da ta zo da wayar, wato Data Cable.  Idan ka jona, kwamfutar za ta nemo yanayin sadarwar kamfanin wayarka, wato Network.  Bayan ta hada alaka a tsakaninta da kamfanin wayar, sai ta hada ka da Intanet kai tsaye.  Dole ne ya zama akwai kudi a cikin wayarka, sannan ya zama ka hada layin wayarka da tsarin Intanet din kamfanin wayar da kake amfani da layinsu, in kuwa ba haka ba, to sadarwa ba ta yiwuwa.  Idan ba wayar Nokia kake amfani da ita ba, sai ka nemi wannan masarrafa daga faifan CD din da wayar ta zo da shi, ko kuma ka je gidan yanar sadarwar wayar, za ka samu kyauta.  Da fatan ka gamsu.


Salam Baban Sadiq, yaya aiki? Allah ya kara haske amin. Tambayata a nan game da adireshin gidajen yanar sadarwa ne, wato “Website”; a karshen adireshi na kan ga an rubuta “.com”, “.net”, “.ng”… da dai sauransu. To, wadannan haruffa dole ne sai an sa su?  In kuma haka ne, to meye mahimmancinsu, ko gudummawarsu a wajen adireshin gidan yanar sadarwa?  Daga dalibinka – Ali Auwal Jibril: aliauwaljibril@yahoo.com

Baban Sadik da fatan kana lafiya, amin.  A Imail, mene ne bambancin da ke tsakanin “…@yahoo.com”, da “…@yahoo.co.uk”?  –  Muazu Kabiru Gwarzo: 07030449643

Dangane da adireshin gidajen yanar sadarwa, duk inda aka rubuta “.com” a karshe, to yana nufin gidan yanar sadarwar kasuwanci ne ko na wasu mutane masu zaman kansu, ko kuma kamfanoni.  Wannan a farkon lamari kenan.  Amma a yanzu “.com” na nufin na kasuwanci ne zalla, “.net” kuma gidan yanar sadarwar mutane ne galibi, ko wasu kungiyoyi masu zaman kansu.  Shi kuma “.ng” kuma na gidajen yanar sadarwar kamfanoni ko hukumomin da ke Najeriya ne. A takaice dai, duk inda ka ga ire-iren wadannan bambance-bambance, to hakan ke nuna cewa gidan yanar sadarwa ne na musamman dangane da wani abu.

Su kuma adireshin Imel masu karewa da “…@yahoo.co.uk”, su ne adireshin Imel din da aka yi rajistarsu ta gidan yanar sadarwar Yahoo! da aka kebance wa mutanen kasar Ingila ko Burtaniya.  Shi kuma mai karewa da “…@yahoo.com” shi ne wanda aka yi rajistarsa ta hanyar gidan yanar sadarwar Yahoo! na gama-gari, wato Yahoo! International kenan.  Akwai masu karewa da “…@yahoo.fr” na kasar Faransa kenan, da dai sauransu.  Da fatan duk an gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.