Sakonnin Masu Karatu (2011) (14)

A yau za mu koma taskar sakonninku ne. Ga kadan daga ciki na amsa. A sha karatu lafiya.

119

Matashiya

Kamar yadda na sanar a makon da ya gabata, a yau ga mu dauke da amsoshin sakonninku da kuka aiko ta tes, da wadanda kuka aiko ta jakar Imel dinmu.  Kamar yadda na saba, wasu daga cikin sakonnin na amsa su ta hanyar tes ko ta Imel inda aka aiko su.  Ire-iren wadannan sakonni ban kawo su tunda na amsa su tuni.  Bayan haka, akwai wadanda ke bugo waya har yanzu – duk da cewa na roki a daina bugo waya.  A haka dai nakan saurare su, har in ba da amsa iya gwargwadon hali.  Wasu kuma in ce su yi hakuri sai na rubuto musu. Akwai wadanda kuma ke cewa kada in buga sakonsu a shafin jarida, su ma nakan yi iya kokari wajen ganin ban buga ba, ta hanyar ba su jawabin tambayarsu.  Bayan haka, har yanzu akwai masu damu na da filashin.  Ire-iren wadannan mutane ina rokonsu da su ji tsoron Allah su daina.  Ba na ganinsu, amma Allah na ganinsu kuma ya sansu, ya kuma san abin da suke yi, zai kuma yi musu sakamakon da ya dace da ayyukansu, ba ruwana.

Har wa yau, akwai wanda ya rubuto yana neman fassarar wasu kalmomi a gaggauce, saboda an bashi aikin gida ne (wato Assignment) a makaranta, kuma lokacin da ya aiko ya nuna yana son amsar a ranar don idan gari ya waye zai gabatar a makaranta.  A gaskiya ban samu damar bashi amsa ba, saboda sakonsa ya same ni cikin yanayin zirga-zirga ne.  Ire-iren wadannan bukatu yana da kyau a rika gabatar da su cikin lokaci, don nima in samu damar bincike – idan sakon na bukatar bincike – kafin in san amsar da zan bayar.  Don haka ina neman afuwa daga wurin wanda ya turo wancan bukata da ban samu damar amsawa ba. A gafarce ni, sai wani jikon idan Allah ya sake hada mu.

A karshe kuma akwai wadanda suka rubuto tsokaci mai tsawo, ban san inda zan sa ba – shin tambaya ce, ko nasiha suke mini, ko gargadi, wallaahu a’alamu –  kan batun yadda ruwa ke samuwa.  Da cewa su sunyi imani da abin da Allah ya fada a Kur’ani cewa ruwa daga sama yake, ba tare da wani dogon bayani ba. Da dai sauran bayanai makamantan wannan.  To, ni dai iya abin da na sani kenan na rubuta.  Kuma ba da ka nayi rubutun ba, sai da na gudanar da bincike a kimiyyance, sannan na gudanar da bincike a addinance, ta hanyar nassoshin Kur’ani da na duba, da sharhin malaman tafsiri, da hadisai, da dai sauran hanyoyi.  Na kuma sanar da masu karatu dukkan ayoyin da na ciro, da hujjojin da suke kokarin tabbatarwa.

To amma akwai alamar wasu basu gamsu ba, ko basu fahimci inda na dosa ba, ko kuma ra’ayinsu ya sha bamban da nawa kan wancan lamari, ko kuma basu samu karanta dukkan kasidun ba.  Abin da na so su yi shi ne, su nuna mini inda na yi kuskure, da hujjojinsu, da kuma abin da yake shi ne daidai, don nan gaba in gyara.  To amma hakan bai samu ba.  Wannan nake sauraro.  Allah mana jagora.

A yanzu dai ga amsoshin tambayoyinku nan.  Duk abin da ba a fahimta ba, don Allah, a nemi karin bayani. In Allah ya so zan fadada bayani iya gwargwadon iko.  Allah shi ne masani, mai cikakken sani da fahimta, wacce babu nakasa a tare da ita.  Allah sa mu dace:


Assalamu Alaikum, Baban Sadik, shawara ta gareka ita ce, ina ganin cewar kalmar ‘tes’ da ‘Imel’ ba kalmomin Hausa bane. Ya kamata kayi amfani da ainihin fasarar da za’a fahimci manufar sakonnin. Huta lafiya. Musa Ningi, No.22 Prison Road, Ningi, Jihar Bauchi.

Malam Musa muna godiya da wannan tsokaci da kayi, Allah saka da alheri.  Wato abin da ya sa nake amfani da kalmar “tes” da “Imel” shi ne, don su ne kalmomin da mutane suka fi fahimta, sabanin yadda kake zato.  Duk bahaushen da kace masa “tes” ko “Imel” a wannan zamani, zai fi saurin fahimta nesa ba kusa ba, da kace masa “gejeren sakon waya” ko “wasikar hanyar sadarwa ta Intanet.”  Dalili na biyu kuma shi ne, wadannan kalmomi sun fi sauki ta wajen gajarta, bayan saukin fahimta.  Sannan kuma duk da cewa kalmomin Turanci ne, ba wani laifi, domin aron kalma a ilmance ba laifi bane. 

A takaice ma dai, duk harshen da ba ya aron kalmomi daga wasu harsuna, to ba zai taba ci gaba ba. Hatta kai kanka sai da kayi amfani da wannan tsari sannan na fahimci sakonka.  Domin ka yi amfani da “kalma” da kuma “fasara”, wadanda kuma duk ba Hausa bane a asalinsu, Kalmomin larabci ne.  A tsarin aron kalma kuwa ba a bambancewa tsakanin wani harshe da wani.  Aron kalma dai aron kalma ne; daga harshen Larabci ne ko Turanci.  Don haka, dangane da yadda malamai suka tabbatar, ba laifi bane don na yi amfani da wadannan kalmomi. Na kuma tabbata masu karatu na fahimta.  Da ba su fahimta da tuni an dame ni da neman karin bayani.  Tunda na bude wannan shafi shekaru biyar da suka wuce, kai ne mutum na farko da ka yi inkarin wannan tsari, duk da cewa kaima ka fahimci abin da nake nufi.  Da fatan dai ka gamsu da wannan jawabi nawa.


Assalamu alaikum Baban Sadiq, Allah ya kara maka basira amin.  Ina son ka yi mini cikakken bayani ne a kan na’uran nan ta “iPad 2”; yaya tsarin sadarwarta take?  Daga Hambali Azare: 08036966225.

- Adv -

Malam Hambali, iPad 2 dai wata na’urar sadarwa ce da kamfanin Apple Inc ya fara kerawa shekaru kusan uku da suka wuce.  Akwai “iPad Wi-Fi”, da “iPad 3G”, da kuma “iPad 2 Wi-Fi.”  Wannan na’urar sadarwa dai ana amfani da ita ne wajen taskance bayanai rubutattu – musamman littattafai –  da bidiyo, da kuma bayanan sauti.  Haka kuma, akwai masarrafai da dama da ke sawwake mu’amala da wadannan bayanai.  Akwai tsarin sadarwa mai inganci, wanda ke sawwake mu’amala da Fasahar Intanet, wato “Wireless Frequency.”  Fasahar iPad na cikin sababbin kirkirarun kayayyakin fasahar sadarwa masu inganci da tsada da tasiri a duniyar yau.  Sai dai ba wayar salula bace, don ba ta da inda aka sanya katin SIM.  An yi ta ne don mu’amala da bayanai da bidiyo da bayanan sauti da kuma littattafan da suke a tsarin na’urar sadarwar zamani. 

Idan ka saya, ba za ka iya mu’amala da fasahar Intanet ba sai ka sa mata makalutun sadarwa.  Kana iya zuwa kamfanin waya na MTN, ko GLO, ko Etisalat, don su jona ka da tsarin sadarwarsu.  Idan suka jona ka, za ka rika biyan kudin layi a duk wata ko yadda tsarinsu ya kama.  Wannan na’urar sadarwa dai tana da kafar da ake shigar da katin SIM, sannan tana amfani da tsarin sadarwar zamani na GSM.  Mafi karancinta a mizani, wato iPad 2 (16GB), ta kai naira dubu dari da ashirin a nairan Najeriya.  Da fatan ka gamsu.


Me yasa wayoyi kirar CDMA suke daukar zafi kuma cajin batirinsu yake saurin karewa a wurin da babu tsarin sadarwar na katin SIM din da ke kansu? Abubakar Wada Kadi.

Alal hakika ban da masaniya kan cewa wannan matsala ta takaita ne kadai ga wayoyin salula masu amfani da tsarin sadarwa ta CDMA.  Abin da na sani shi ne wayoyin salula kan yi zafi, kuma daga cikin dalilan da ke haddasa musu wannan zafi akwai matsalar batir; ko dai saboda jabun batir, ko kuma batirin da ke cikinsu ya samu matsatsi daga mummunar yanayin zafin rana ko muhallin da wayar ke ajiye.  Cikin shekarar 2003 da 2004 an samu rahotannin wayoyin da suka yi ta fashewa da wuta sanadiyyar zafi da suka yi a kasar Amurka da sauran kasashen Turai.  An kuma danganta dukkan wadannan matsaloli ne ga jabun batira ko kuma zafin yanayi da muhalli.  Daga karshe ma dai an gano cewa ko da ingantattun batira ne suna iya fashewa idan akwai yanayin da suke ciki ya dumama. 

Daga cikin dalilan har wa yau daukan tsawon lokaci ana amfani da waya ko wata masarrafa da ke cikinta.  Wannan shi ma yakan janyo zafi ga wayar salula.  Amma zafin da waya ke yi sanadiyyar rashin yanayin sadarwa a inda waya take, babu wani alaka a tsakaninsu.  Ta yiwu dai batirin da ke wayar ya lalace, ko kuma jabu ne, ba ingantacce ba. A takaice dai, jabun batira sun fi haddasa zafi ga wayar salula fiye da kowace irin matsala.  Don haka ne ma kamfanonin waya a yanzu suka dauki matakin sanya wasu hanyoyin kariya a cikin batiran masu tantance ingantaccen batir da jabunsa. Kuma hakan bai takaitu ga wayoyin salula masu amfani da tsarin sadarwa nau’in CDMA ba.  Wannan shi ne dan abin da na sani.  Da fatan an gamsu.


Baban Sadiq da fatan an tashi lafiya, tambayata ita ce, na bude shafin Facebook, ya yi, amma da na sake budewa jiya sai aka ce mini “Pls be patient while testing the connection for the first time.”  Idan ya dan jima, can sai ya ce: “Connection failed.  Check Your internet setting.”  Ina neman karin bayani.  A. Sadiq

Abin da wannan sako ke nufi shi ne, akwai matsala da tsarin sadarwar Intanet da ke wayar.  Don haka sai a duba a gani.  Idan akwai “Internet Settings” sama da guda daya ne a wayar, sai a zabi guda daya a mayar da shi “Default.”  Idan kuma babu ne gaba daya, sai a aika wa kamfanin waya sako don su turo.  Allah sa a dace.


Assalamu alaikum, da fatan kana lafiya? Dan Allah meye amfanin WLAN Service? Kuma yaya zan yi amfani da shi? Na ga kasidarka game da IPv4 da IPv6, zan iya canzawa daga IPv4 zuwa IPv6?  Dan Allah meye bambamcin tura sako ta imel da tes? Kuma me yasa idan na tura sako ta imel ba ya tafiya? Waya ta {C3 Nokia} ce ko akwai wani abin da ya kamata na yi ne wanda ban yi ba? Wasalam nine ibrahim muh’d, Toro Bauchi 08065750790

Amfanin “Wireless LAN Service” shi ne aiwatar da sadarwar Intanet ta hanyar yanayin sadarwar wayar iska.  Galibin wayoyin salular zamani suna amfani da wannan tsari ne.  Amma ba za ka iya amfani da shi ba sai a wurin da ake da tsari irin wannan. Idan ka kunna shi, wayar za ta sanar da kai cewa “Akwai yanayin sadarwar wayar iska a nan.”  Bayan haka, za ka iya amfani da wannan tsari don shiga Intanet iya gwargwadon yadda tsarin yake.  Akwai tsarin WLAN da ke kulle, wato “Secured WLAN” kenan.  Irin wannan tsari ba ka iya mu’amala da shi sai an tsara maka, ta hanyar shigar da kalmomin sirrin da aka tsare tsarin da su.  Akwai kuma budadden tsarin sadarwar wayar iska, wato “Unsecured WLAN.”  Shi wannan da zarar ka jona wayarka da shi kawai shikenan, sai ka ta kwasan garabasa kyauta. 

Tsarin IPv4 dai shi ne wanda ake amfani da shi har yanzu.  Ba a riga aka yi hijira zuwa IPv6 ba.  Idan lokacin yayi, ba sai ka yi hijira da kanka ba, wayar da kake amfani da ita za ta iya yin haka nan take.  Domin galibin wayoyin salula da kayayyakin sadarwa na zamani a yanzu suna zuwa ne da dukkan tsare-tsaren guda biyu.  Amsar tambayarka ta gaba kuma ita ce, akwai bambanci tsakanin Imel da sakonnin Tes.  Imel dai hanyar aikawa da sakonni ne ta Intanet, wacce ke da tsari da kintsi da hanyarta na musamman, da kuma ka’idojin sadarwa masu taimakawa don yin hakan; a wayar salula ne ko a kwamfuta. 

Amma tsarin Tes kuwa hanyar aikawa da sakonni ne ta amfani da yanayin sadarwar kamfanin wayar tarho, ta wayar iska.  Tsarin Imel a wayar salula da kwamfuta duk yana bukatar sai an tsara shi, wato “Configuring” kenan, a turancin kimiyyar sadarwa. Na kuma tabbata rashin tsarin ne ya sa idan ka yi kokarin aikawa da sakonnin Imel sai ya kasa tafiya.  Ka duba kundin da wayar ta zo dashi, za ka ga yadda ake saitawa.  Amma tsarin Tes a wayar salula ba ya bukatar wani saiti; da zarar ka sayi waya, ka sa mata katin SIM, nan take kana iya rubuta sakonnin tes ka aika.  Domin dukkan tsare-tsarenta na cikin katin SIM, wanda ke aiwatar da sadarwa ta kai tsaye da yanayin sadarwar kamfanin waya.  Da fatan an gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.