Sakonnin Masu Karatu (2011) (13)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

84

Baban Sadik: ban gane ba na ji kace wai ruwan sama maimaituwa yake, bayan  fadin Ubangiji “mun saukar da ruwa daga sama mai tsarki.”  Kuma ko da dandanonsu ne ya sha bamban da na rijiya ko na kogi, haka abin yake  ga tsirrai. Domin duk tsirran da ya sha ruwan sama ya fi wanda aka yi masa bayi. Wannan yana nuna maka da cewa sinadaran da ke cikin ruwan sama yayi daban da na teku. Ruwan teku yana dandanon gishiri. Daga Ghali Bauchi

Malam Ghali sannu da aiki, kuma na gode da wannan fadakarwa da tsokaci.  Hakika na karu sosai da wannan bayani naka.  Duk da cewa har yanzu dai ina kan baka na, domin akwai bangaren hujjojin da ka kawo wadanda basu kai su tunkude abin da na rubuta ba, sai ma kara karfafa su da suka yi.  Da farko dai tukun, cewa da Allah yayi ya saukar da ruwa mai tsarki, haka abin yake. Sannan batun dandano, da tasiri a kan shuke-shuke, wannan ba abin mamaki bane don ruwan sama ya zarce sauran nau’uka, domin kamar yadda na sanar, ruwan sama na maimaituwa ne a wani yanayi da tsari, wanda dole ne a samu bambancin dandano tsakaninsa da sauran nau’ukan ruwa da ke duniya.  Kuma sanadiyyar wannan tasiri ne ma ake samun kankara da ke sauka daga gira-gizai.  Kamar yadda na tabbatar a kasidar, ruwa ba daga jikin sama bane yake zuba, daga jikin gira-gizai ne, haka Malaman tafsirin Kur’ani suka tabbatar. 

Har wa yau ba abin mamaki bane don ruwan sama ya fi tasiri wajen tsirrai kan sauran nau’ukan ruwa. Wannan albarka ne da Allah ya sa a cikinsa.  Albarka kuwa shi ne dukkan wani nau’in alheri da ke samuwa daga wani abu ko wani mutum ko wani gari misali. Kasancewar ruwan sama na da albarka ba ya hana sauran nau’ukan ruwa su zama haka, sai dai kowanne da nashi bangaren da Allah ya killace masa.  Misali, ga ruwan zamzam nan, yana da albarka shi ma, amma daga karkashin kasa yake bubbuga. 

Amma idan ka ce don Allah yace ruwan sama mai tsarki ne, kuma da haka kake ganin dole ya zama daga wani muhalli ne ba maimaituwa yake ba ta hanyar dalilan kimiyya da suka tabbata ta hanyar bincike, a nan dole ka kawo wa jama’a hujja; daga ina ruwan ke zuwa?  Domin ruwan sama na cikin ayoyin Ubangiji da ya kirayi duniya gaba daya ta yi dubi gare shi, dubi irin na tunani da nazari, don gano kudurar Allah.  Wannan na cikin aya ta 168 da ke cikin Suratul Bakara.  Shi kuma Allah ba ya kalubalantar mutane su yi nazari kan abin da idan sun kalle shi ba za su fahimci sakon da ke cikinsa ba, a dabi’ance.  Domin dukkan ayoyin da Allah ya samar a cikin halittunsa duk wani mai hankali na iya fahimtarsu idan ya yi musu kallo na nazari da fahimta, ko da kuwa ba musulmi bane shi.  Kuma tunda ruwan sama da tsarin saukansa na cikin ayoyin Allah da ya samar, dole ne ya zama duk wanda ya yi nazari kan samuwansa, da yadda yake haduwa, da yadda yake tasiri idan ya sauka, zai gane abin da ake kiransa a kai.  Shi kuma kallo da yin nazari kan abu bai takaitu ga kallo na ido kadai ba, a a, duk wata hanya da za ta iya taimakawa a fahimci tsarin abin ana iya amfani da ita don fahimtar abin da ake son fahimta. 

Da wannan tsari ne malaman kimiyya suke amfani wajen gano tsarin da ke cikin halittar Allah, musamman sama da kasa da sauran halittu masu rai.  Da haka suka gano wannan tsari na saukar ruwa.  In kuwa haka ne, duk da cewa ba lalai bane su yi daidai dari bisa dari, amma sai an samu tabbaci da kamshin gaskiya cikin binciken. Domin ba abu bane da aka zauna aka kirkira da ka, ko da tunani, da zace-zace.

- Adv -

Amma sauran halittun Allah da suka shafi gaibu, irin su Kursiyyu, da Al’arshi, da ruwan da ke saman sammai bakwai, wanda Al’arshinsa ke kai – kamar yadda ya fada cikin Kur’ani – duk abubuwa ne da hankali ko ilmi ko zurfin binciken mai bincike ba zai taba iya gano su ba, sai dai ayi imani da su saboda imani da aka yi da Allah.  Wannan ta sa ba za ka taba cin karo da wata ayar Kur’ani da ke kira ga masu hankali ko ilmi da su yi bincike kan yadda Kursiyyun Allah ko Al’arshinsa yake ba.  Saboda ba abu bane da za a iya gano shi ta hanyar bincike, sai ta hanyar wahayi da imani da gaibu kawai. 

Don haka ina nan a kan baka na cewa ruwan sama daga gira-gizai yake samuwa, kuma ruwa ne mai maimaituwa a wani tsari da kintsi na musamman, kamar yadda na sanar a wancan kasida tawa.  Sannan Allah yana da ikon sanya duk abin da ya ga daman sa wa a cikin ruwan na albarka da sauransu. Kuma ba abin mamaki bane don dandanonsa ya canza, domin ruwan rijiya ma ai asalinsa daga sama ne, amma dandanonsa sun canza saboda muhallin da suke, na bambancin kasa da sauransu.  Haka ruwan teku, su kuma haka Allah ya halicce su, da dandanon gishiri, kuma akwai shamaki wanda ido ba  ya iya gani a tsakaninsa da ruwan gardi mai zuba daga sama.  A karshe muna binka bashin hujja kan cewa ruwan sama daga wani wuri daban yake zuwa ba daga jikin gira-gizai ba.  Amma a nawa bincike, wanda ya dogara kan ayoyin Kur’ani da sakamakon binciken malaman kimiyya na gamsu da abin da na karanta.  Sai na ji daga gare ka, Malam Ghali.


Salam, na rubuto don in sanar da kai cewa na ga blogs dinka kuma na amfana ni da iyalina kwarai Allah ya saka da alhairi kuma ya kara hasken kwakwalwa amin.  Sani Mafara; 2348062104878

Malam Sani ni ne da godiya.  Domin ba karamin abin farin ciki bane mutum ya fahimci cewa dan kokarin da yake yi, mai cike da karancin ilimi, yana tasiri ba.  Don haka na fi ka farin cikin jin haka.  Allah sa mu dace, ya kuma albarkaci duk wata haza ka da ya bamu, amin.  Na gode.


Don Allah Baban Sadik ina so a turo min kasidar da kuka gabatar kan wayoyin salula kirar nokia ko blackberry.  Kuma ina da waya kirar nokia 3110c amma duk wani kayan application kamar dictionary, da opera da sauransu. Idan aka turo sai ta bata su, (corrupted & invalid appl.) ko menene dalili?  Na gode.  Daga Ibrahim Hamisu, Kurna Filin Durumi. Ibrahimhamisu68@yahoo.com

Malam Ibrahim da farko dai akwai kasidar da muka gabatar kan wayar Blackberry ce, ba Nokia ba, kuma na tura maka kamar yadda ka bukata.  Dangane da abin da ya shafi wayarka kuma, ina ganin dai kamar ta kamu da cutar kwayar kwamfuta ne, wato Virus.  Zai dace ka kaita wajen masu gyara su duba maka.  Domin idan lafiyarta lau bai kamata ta bata duk abin da aka tura mata ba.  An samu canjin dabi’a kenan.  Akwai illa tattare da ita.  Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.