Sakonnin Masu Karatu (2009) (6)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

94

Salamun Alaikum, Baban Sadiq, wutar lantarki (electricity); wasu kasashe na duniya suna hada wutar lantarkinsu ne ta karkashin kasa, mu kuma muna hada namu ne ta sama, gashi wasu wuraren ma har da mitar zamani (electricity meter).  To Malam meye bambancinsu?  Kuma ina yi wa Malam fatan alheri da murnar shiga sabuwar shekarar musulunci.  – Aliyu Muktar Sa’id, Kano: 08034332200

Malam Aliyu ga dukkan alamu kana da sha’awa kan fannin fasahar kere-kere ne ko?  Haka na hango.  Dukkan tambayoyin ka can suke nufa.  Na’am, bambanci tsakanin hada wutar lantarki ta kasa ko sama, ya danganta da yanayin wuri, da irin bigiren da kasar take, da kuma halin kudi ta bangaren gwamnati.  A wasu kasashe sukan hada ta kasa ne saboda guje wa iska mai tsanani da suke fuskanta lokaci-lokaci, ko saboda guje wa barayi, da dai sauran hujjoji da su kadai suka sani.  Masu yi ta kasa kuma a zahiri akwai lura da yanayin aljihunsu, ko kuma yanayin kasarsu.  Don haka samun wani tsari ne ya fi inganci ya danganta da abinda kowace kasa ke da ikon yi,  ko kuma irin yanayin da take rayuwa a ciki.  – Baban Sadiq


Assalamu Alaikum, don Allah muna fatan za a yi mana bayani kan GPRS da kuma WAP.  Mun gode. – Hashim Kafinta, Layin NYSC, Kongolam, Jihar Katsina: 08099659379

Malam Hashim mun gode da samun wannan sako naka. Sai dai kamar yadda na sha fada ne, bayanai kan tsarin GPRS da WAP sun yawaita a wannan shafi, don haka idan ba wata munasaba bace ta sake tasowa, sai dai a yi hakuri a je shafin MAKARANTAR KIMIYYA DA FASAHA da ke Intanet, a wannan adireshin: http://fasahar-intanet.blogspot.com.  Wannan shine shafin da muke zuba dukkan kasidun da ake karanta su a wannan shafi.  Za a samu bayanai gamsassu cikin kasida ta musamman da muka rubuta.  Idan kaje kana iya buga kasidar ma kaje ka karanta a gida.  A yi hakuri da wannan. Mun gode.  – Baban Sadiq


Baban Sadiq, na karanta rubutunka na ranar 02/01/2009, kuma ina sanar da kai cewa akwai sabon littafi a kan kiwon lafiya na Hausa da Malam Abdulkarin Usamatu Katsina ya rubuta, kwanan nan.  Yayi kokari sosai wajen bincike, kuma yayi Magana a kan abubuwa da dama.  An kaddamar da littafin a Katsina da Kaduna.  Ka neme shi.  – Ahmad: 08028456627

Malam Ahmad mun gode da wannan sanarwa, Allah saka da alheri.  Lallai wannan littafi abin nema ne, don ire-irensu basu yadu ba kamar yadda bayani ya gabata kwanakin baya.  Mun gode.  – Baban Sadiq


Na karanta shafin kimiya da fasaha da karubuta. don allah ina zan samu wannan littafi da da ambata a shafinka:  Hacking for Dummies by Kevin Beaver?  Don allah ka shigar dani cikin wadanda ake aikoma shafin kimiya da fasaha ta email (email mailing list). Na gode, sai naji daga gareka.  Wassalam.   Musa Ali: yaleintegrate@yahoo.com

Malam Musa na aiko maka sako cewa zan turo maka wannan littafi, amma daga baya nayi tunanin cewa littafin na da girma kuma hakan ke nuna cewa mizaninsa na bukatar lokaci kafin in dora shi a Intanet, daga nan in aiko maka.  Idan na aiko maka, zai sake daukan lokaci  kafin ka iya saukar da shi, musamman ma idan kwamfutar ba taka bace.  Sai in kana bukata in sanya maka shi a cikin fai-fan CD, in aiko maka.  Hakan ma sai in kana da kwamfuta za ka iya amfani dashi.  Amsar bukatarka ta kuma ita ce:  a yanzu bamu aikawa da kasidu ga masu karatu sai dai su je shafin da ake taskance kasidun a Intanet, wanda ke http://fasahar-intanet.blogspot.com.  Da fatan ka gamsu.  – Baban Sadiq


Assalamu Alaikum, da fatan kana lafiya, ya aiki?  Dan Allah a fahimtar da ni ya ake yin (rajistar) Imel address a waya?  Ina so nayi a waya ta, ya zan yi?  – Hassan I. Adamu, Kurna, Kano: 08036268059

- Adv -

Malam Hassan na tabbata yanzu kam ka samu cikakken bayani kan yadda wannan tsari yake cikin makon da ya gabata a wannan shafi, da kuma sakonnin da na aiko maka ta wayarka.  Idan baka gamsu ba, ko ka ci karo da wasu matsaloli, to ka bugo min waya sai in kara maka bayani.  Mun gode.  – Baban Sadiq


Salam, Baban Sadik ya aiki?  Da fatan komai na tafiya daidai.  Daga dalibarka, Fatima Bashir Ahmad, Jihar Kano.

Malam Fatima mun gode da gaisuwa, Allah saka da alheri ya kuma bar zumunci.  A gaida Bashir karami, tare da Umman sa.  Mun gode.  – Baban Sadiq


Salamun Alaikum, Baban Sadiq tambaya ta itace, a duniya wace kasa ce ja gaba a harkar kimiyyar  sadarwar bayanai (Information Technology – IT)?  A bani tarihinta.  Allah ya taimake ka da mu almajiran wannan shafi mai albarka na Kimiyya da Fasaha, amin.  – Aliyu Muktar Sa’idu, Kano: 08034332200

Bayani kan kasar da ke ja gaba kan harkar “Information Technology” na bukatar sharhi kan gudunmuwar kowace kasa kan wannan harka.  Duk da yake galibi na ganin kasar Amurka ce, amma bai kamata ta dauki wannan matsayi ita kadai ba; akwai kasashe irin su Jafan, da Koriya ta Kudu, da Singafo, inda a can ake kera dukkan masarrafan da ake lika wa kwamfuta, watau “micro-chips”, ko kuma “Processors”.  Haka kuma, a kasar Sin ana kera da dama cikin kwarangwal din kwamfuta (Computer Hardware), da zuciyarta (motherboard) da sauran karikitai.  Idan muka leka kasar Rasha, sai mu ga ita ce tafi kowace kasa yawan kwararru kan fasahar gina masarrafar kwamfuta, watau “Computer Programmers”.  Haka kasar Indiya na samun kashi wajen goma zuwa ashirin na kudaden shigarta ne daga fannin gina manhajar kwamfuta da ‘yan kasar ke tallatawa a kasar da ma wasu kasashe.  Don haka kasar Amurka dai suna ta tara, ko muce ita ce matattarar kamfanonin da ke yin harkar, amma galibin inda ake harkokin su ne wadannan kasashe.  Allah sa mu dace, amin. – Baban Sadiq


Da fatan Baban Sadiq yana lafiya.  Tambayata a nan ita ce, kamar ni da sana’ata ita ce aikin kafinta, wata manhaja zan shiga domin in duba abubuwan ci gaba a aiki na?  Ko ba a samun irin namu?  Da fatan Malam zai taimaka mini da amsa ta. Na gode, Allah Ya taimakemu baki daya, amin.  – 08065432898

Malam na samu sakonka, kuma lallai akwai “irin naku” a Intanet.  Za ka iya shiga, kayi bincike kan aikin kafinta da ire-iren kayayyakin aikin kafinta na zamani, da yadda za ka iya tsara shagonka tare da kyautata aikin, nesa ba kusa ba.  Abinda kake bukata kawai shine ka san me kake son bincike a kanshi?  Kayan aiki ne, ko tsarin aikin kafinta?  Ko kuma ire-iren abubuwan da ake kerawa na zamani a sana’ar?  Ya kuma zama ka san sunayensu da harshen Turanci, domin cikin wannan harshe ne bayanai suka fi yawaita.  Sai ka je shafin “Google” da ke www.google.com, don binciko wadannan abubuwa.  Don haka akwai irin naku!  Allah sa mu dace baki daya, amin.  – Baban Sadiq


Kammalawa

Wadannan su ne kadan cikin sakonnin da kuka aiko mana.  Wanda bai ji an sanya nasa  sakon ba yayi hakuri, sai wani lokaci.  Bayan haka, muna kara godiya ga masu bugo waya.  Saboda yawansu, da kuma ganin ba wani rajista na ajiye don taskance sunayensu ba, sai dai mu ce Allah saka musu da alheri musamman sanadiyyar kara karfafa min guiwa da suke yi a dukkan lokuta.  Na gode, Allah saka da alheri har wa yau.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.