Saƙonnin Masu Karatu (2022) (9)

Dalilan Rufe Shafi a Facebook

Dalilan dake sa a rufe maka shafinka a Facebook suna da ɗimbin yawa.  Amma za mu iya keɓance su zuwa dalilai 12; duk wani laifi da zai sa a rufe maka shafi, ba ya rasa alaƙa da ɗaya ko biyu daga cikin waɗannan dalilai ko laifuka guda goma shabiyu.  – Jaridar AMINIYA ta ranar Jummu’a, 07 ga watan Oktoba, 2022.

108

Kamar makon jiya, yau ma za mu ci gaba ne da amsa tambayoyin masu karatu.  Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare damu yadda aka saba.

——————-

Dalilan Rufe Account a Facebook

Dalilan dake sa a rufe maka shafinka a Facebook suna da ɗimbin yawa.  Amma za mu iya keɓance su zuwa dalilai 12; duk wani laifi da zai sa a rufe maka shafi, ba ya rasa alaƙa da ɗaya ko biyu daga cikin waɗannan dalilai ko laifuka guda goma shabiyu.  Sai dai kuma, ba kowane lokaci za a gaya maka laifinka ba, sai dai kawai ace maka: “An rufe shafinka” ko “An hana ka aika saƙonni sanadiyyar saɓa dokar ma’amala a wannan kafa ta mu…” ko wani abu makamancin wannan.  A halin yanzu dai ga waɗannan laifuka nan:

Buɗe Shafi Sama da Ɗaya

A ƙa’idar dokar Facebook, shafi ɗaya kaɗai aka yarda ka buɗe don ma’amala da mutane, kuma ya zama da asalin sunanka ne.   Ba laifi kasa laƙabi ko kayi sayen suna, amma ya zama akwai asalin sunanka da mutane suka sanka dashi.  A sadda kake yin rajistar shafi da Facebook a karon farko, wannan ita ce ka’idar farko kuma mafi mahimmanci da ka amince da ita, kafin a baka damar ma’amala da sabon shafinka.  Buɗe shafi biyu da suna ɗaya haramun ne a dokar Facebook, ko da kuwa daga baya ne ka buɗe na biyun bayan watakila ka samu matsala an rufe na farko. Idan ka sake buɗe wani da suna iri ɗaya, da bayanai iri daya, za a gane, kuma nan take za a rufe shafin.  Ko da kuwa da adireshin Imel ne ko da wata lambar wayar daban.  Facebook bai yafe wannan zunubin, ko da ƙiftawar ido. Shi yasa, buɗe wani shafi da adireshin Imel ko lambar waya iri ɗaya da wanda kake amfani dashi ma, ba ya yiyuwa ko kaɗan.

Amma cikin ƙare-ƙaren da shafin Facebook ke ƙoƙarin samarwa, akwai bayar da damar haɗe shafukan da ka buɗe masu alaƙa dakai.  Misali, idan na buɗe shafi mai suna: “Baban Sadik” ta amfani da lambar waya, daga baya na sake buɗe wani mai ɗauke da sunan: “Abdullahi Salihu Abubakar” ta amfani da adireshin Imel ko wata lambar wayar daban, sabon tsarin na iya bani damar alaƙanta su da juna.  Abin nufi, idan na buɗe ɗaya, zan iya ganin sauran.  Wannan zai bani sauƙin ma’amala dasu, sannan duk wanda ya sanni da ɗaya, shafin Facebook zai sanar dashi cewa ina da wani shafin kuma mai suna kaza.  Hikimar ita ce, tunda ba abu bane mai sauƙi a iya kama masu buɗe shafi sama da ɗaya ta amfani da hanyoyi daban-daban, hukumar Facebook ta lura cewa haɗe shafukan da alaƙanta su da mai su, ita ce hanya mafi sauƙi kawai.

- Adv -

Idan hukumar Facebook ta kama ka da laifin buɗe shafuka sama da ɗaya, tana ɗaukan hakan laifi ne mai girma, kuma tana alaƙanta shi da laifin yunƙurin cutar mutane ne.  Don haka, sai ta buƙaci ka aiko wasu bayanai da za su tabbatar da cewa lallai kai ɗin nan da kace kaine wane, to, haƙiƙanin wanen ne.  Idan ɗayan shafin a buɗe yake, za ta barshi, sai ta rufe ɗaya; a barka da guda ɗaya tilo.

Buɗe Shafin Bogi (Fake Account)

Buɗe shafin bogi yana cikin manyan laifukan da hukumar Facebook ba ta yafewa, ko kaɗan.  A shekarar 2020 Hukumar Facebook ta goge saƙonni da shafukan bogi guda biliyan uku da miliyan ɗari uku (3.3 billion).  To wani shafi ne shafin bogi?  Shafin bogi shi ne duk wani shafi da wani zai buɗe da wata manufa ta musamman, ba don alaƙa da asalin mutanen da suka sanshi ba, kamar yadda yake a manufar samar da dandalin Facebook.  Daga cikin siffofin shafin bogi shi ne, ba ya ɗauke da asalin sunan mai shafin ko alkunyansa; ba ya ɗauke da haƙiƙanin hoton mai shafin; ba ya ɗauke da asalin lambar wayarsa ko adireshin Imel dinsa da aka sanshi dashi; sannan an bude shi ne da sunan wani, don shiga rigarsa ko zatinsa.  A taƙaice dai:  shafin bogi shafi ne da aka buɗe shi da manufar da ta saɓa wa manufar samar da dandalin Facebook, don kwaikwayon wani, ko shiga zatin wani, ko yaudara a sunan wani, ko kuma, a karon ƙarshe, cutar wasu da sunan wani.

Akwai shafukan bogi da yawa a Facebook, abin mamaki.  Kuma a kullum goge su ake yi.  Sai dai kuma, ta wace hanya manhajar Facebook ke iya gane shafin bogi?  Shafin bogi na da wasu siffofi na aiki da ba sa ɓoyuwa.  Idan manufar buɗe shafin don bibiyar wani ne, hankalin shafin zai koma kansa ne.  Idan manufar shafin don cutar wasu ne ta hanyar hira (chatting) ko aika sakonni, shafin zai shagaltu da hakan ne.  Haka idan manufar shafin bogi shi ne don samun shahara ƙarƙashin zatin wani shahararre, to, mai shafin zai yawaita aika saƙonnin abota ga ire-iren mutanen da yake son ribatarsu don samun biyan bukatarsa.  Waɗannan alamu na aikatau, alama ce da tsarin Facebook ke amfani dasu wajen rufe ire-iren waɗannan shafuka cikin sauƙi ba tare da wani hayaniya ba.

A daya bangaren kuma, idan manhajojin da aka tanada a Dandalin basu iya tantance shafukan bogi ba, jama’a na iya kai ƙorafi ko saƙon koke, don a cire su.  Ni kaina na sha kai ƙorafin shafukan bogi ba ban san iyakansu ba, waɗanda a ƙarshe hukumar Facebook ta cire su gaba ɗaya.  Galibinsu suna ɗauke ne da sunayen manyan mutane da na san ba su da shafuka ko rajista a Facebook a lokacin.  Wasu ma sarakunan gargajiya ne na Arewa da wasu ke amfani da sunayensu wajen zambatar jama’a.

Akwai wata baiwar Allah da wani cikin ire-iren waɗannan mutane ya cuta.  Shafi ya buɗ na bogi da sunan mai martaba Sarkin Kano na wancan lokaci, sai ya wallafa saƙo ya aika cewa akwai gidauniya da ya buɗe don samar da aiki ga matasa.  Sai ta aika masa saƙo cewa tana son amfana da wannan gidauniya.  Sai ya aika mata lambar wani ƙabilar Ibo (shi ne daman asalin mai lambar), cewa ta kira shi, ta aika masa takardunta.  Da ta sanar dashi cewa ta kira kuma ta aika, amma mutumin yace sai ta aika da kuɗi saboda hidimar haɗa bayanan (Processing fee), sai yace mata eh, kada ta damu, kawai ta bashi.  Ana haka ne na fahimci halin da take ciki, sai na hana ta.  Nace mata muddin bata tsayar da abin a haka ba, wallahi sai ta kashe sama da dubu ɗari, kuma ba abin da za ta samu; hannu wayam za ta tashi.  A ƙarshe da na bincika sai na tarar cewa, da wanda ya buɗe wannan shafi, da wancan ɗan kabilar Ibo dake karɓan kuɗaɗen mutane, duk mutum ɗaya ne.

Idan hukumar Facebook ta kama ka da laifin buɗe shafin bogi, wayyo Allah!  Ka rasa shafin kenan har abada.  Babu batun wai a baka damar kare kanka ko aiko wasu bayanai don tantanceka; tuni ka gama tantance kanka a matsayin tantiri.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.