Saƙonnin Masu Karatu (2022) (8)

Dalilan Rufe Shafin Facebook

Nazarin ƙorafinka/ki na iya ɗaukan lokaci…”  ko wani zance makamancin hakan.  A yayin da manhajar kwamfuta ce ke lura da masu saɓa doka kuma nan take su rufe shafukansu idan suka taka doka, amma bayan ka aika bayanan da ake buƙata daga gareka, ɗan adam ne ke nazarinsu don tabbatar da gaskiya ko akasin haka, kan tuhumar da ake maka. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 30 ga watan Satumba, 2022.

111

Kamar makon jiya, yau ma za mu ci gaba ne da amsa tambayoyin masu karatu.  Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare damu yadda aka saba.

——————-

Salamun alaikum Baban Sadiƙ, da fatan ka tashi cikin ƙoshin lafiya.  A cikin bayaninka na sabuwar doka ta Social Media, ban ji ka ambaci manhajar Tiktok ba.   Domin ta fi bamu mastala akan sauran da ka ambata.  Ko sabo da za a rufe Tiktok ɗin ne kamar yadda muka gani a kafar yaɗa labarai?  Daga mai bin shafinka duk mako: Abdulkadir Lawal. 09022403569.

Wa alaikumus salam Malam Abdulƙadir, lafiya ƙalau.  Da farko dai, kafin inje ga amsar tambayarka ko neman ƙarin bayani, labaran dake yawo cewa za a rufe ko kulle shafin Tiktok.  Waɗannan saƙonnin bogi ne dake yawo a kafafen sada zumunta.  Zance makamancin wannan ya samo asali ne daga ƙasar Amurka, sadda aka samu taƙaddama tsakanin gwamnatin Amurka da kamfanonin ƙasar Sin dake da reshe a ƙasar, inda shugaba Trump a wancan lokaci yayi yunƙurin rufe kamfanin Byte Dance, wanda shi ne mamallakin manhajar Tiktok, amma a ƙarshe an daidaita.

Dangane da batun sabuwar dokar ƙayyade ta’ammali da kafafen sadarwa na zamani a Najeriya da nayi sharhinta kuma, na kawo misalai ne na hanyoyin da wasu daga cikin wadannan kafafe suke bi wajen ganin sun ƙayyade tsarin ma’amalar mutane a kafafen nasu.  Na kawo misalin Facebook, da Youtube, da kuma Twitter ne, domin manyan kamfanoni ne, idan aka kwatanta su da Tiktok, sannan sun daɗe ana ta’ammali dasu.  Wannan yasa tasirinsu ga rayuwa yafi gamewa.  Sannan a ƙalla a baya an samu matsaloli tsakaninsu da hukumomin wasu ƙasashe, sanadiyyar dokokin da suka gindaya wa mutane.  Rashin ambaton manhajar Tiktok ko kamfanin Byte Dance, ba ya nuna dokar ba za ta shafe shi ba, kuma ba na yi hakan ne don za a rufe shafin ko manhajar ba, kamar yadda ka hakaito ko kake zato.  Wannan ba haka yake ba.  Na taƙaita bayanai ne kan shahararrun, kuma waɗanda suka fi tasiri a rayuwar mutane.

Da fatan ka gamsu da taƙaitaccen bayani na.

- Adv -

Assalamu alaikum, bayan gaisuwa da fatan alkairi, ina da tambaya ne.  An kulle min shafina na Facebook ne kwatsam, wai akwai wasu dokokinsu da na karya.  Sun buƙaci in turo musu bayanai da nayi amfani da su wajen buɗe account din.   Na kuma yi hakan.  Sun bani wata ɗaya wai za su yi bincike idan ya tabbata na karya dokan za su share ni kwata-kwata daga kan manhajarsu.   Idan kuma ba haka bane to, za su buɗe min.  Wasu dokoki ne suke sa idan mutun ya karya sai su rufe masa account, don mu kiyaye? Sannan ko akwai yadda za a yi mutum ya buɗe account ɗin ba sai ya kai wata ɗayan ba? Daga Abdulaziz Ƙasim, Abuja: 08160193134.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abdulaziz, da fatan kana lafiya kai ma.  Kamar yadda ka sanar, idan aka samu matsala irin wannan hukumar Facebook kan buƙaci ka aika da wasu bayanai da za ta yi nazarinsu don tabbatar da cewa lallai kai dan adam ne, kuma lallai shafin naka ne.  Wannan, a bisa manufarsu, ya zama dole don yi maka adalci wajen hukunci kan abin da suke tuhumarka da shi.  A galibin lokuta sukan sanar da lokacin buɗe maka shafin, kuma su buɗe maka shi cikin lokacin da suka yanka maka, ko ma ƙasa da haka idan sun gamsu da bayananka.  Amma a wasu lokuta akan ɗauki dogon lokaci baki ji wani bayani daga garesu ba.  Hakan kan faru ne sanadiyyar manyan dalilai guda biyu.

Dalilan Jinkiri

Na farko, suna da ƙarancin ma’aikata masu kulawa da ire-iren waɗannan lalurori na mutane.  Hakan ya faru ne saboda galibin ma’aikatansu na aiki ne daga gidajensu, tun sadda aka shiga halin cutar korona.  Da yawa cikin ma’aikantan har yanzu basu dawo ba.  Wannan yasa aka samu ƙarancin masu kula da nazarin ƙorafe-ƙorafen jama’a.  In da ka kula sadda ka gama aika musu saƙon, za ka ga sako cewa: “Ka sauraremu, domin a halin yanzu muna da ƙarancin ma’aikata.  Nazarin ƙorafinka/ki na iya ɗaukan lokaci…”  ko wani zance makamancin hakan.  A yayin da manhajar kwamfuta ce ke lura da masu saɓa doka kuma nan take su rufe shafukansu idan suka taka doka, amma bayan ka aika bayanan da ake buƙata daga gareka, ɗan adam ne ke nazarinsu don tabbatar da gaskiya ko akasin haka, kan tuhumar da ake maka.

Dalili na biyu, tun daga shekarar 2019 kamfanin Facebook bai gushe ba yana ta aiwatar da sauye-sauye a shafinsa, don tabbatar da ƙa’idojin da ya gindaya wa kansa, da waɗanda hukumomin ƙasar Amurka da sauran ƙasashen nahiyar turai suka gindaya masa.  Wannan yasa jama’a da yawa suke ta samun matsaloli da shafukansu.  Domin akwai wasu abubuwa na halayya da ɗabi’a da a baya bai damu dasu ba, amma a yanzu sun zama laifi.  Da zarar ka sake aikata su, sai kawai kaji anyi waje da kai.  Wannan yasa korafe-korafen jama’a suka yawaita.  Kuma nazari kan ƙorafinsu ke ɗaukan lokaci.  A halin yanzu Dandalin Facebook na da ma’aikata sama da dubu goma shabiyar (15,000) da ke aikin tantance ƙorafe-ƙorafen jama’a. Don haka, idan kaji shiru bayan wata daya, kada kayi mamaki.  Akwai wata baiwar Allah da na taimaka mata wajen aika dukkan bayanan da Facebook ya buƙata don tantanceta da barrantar da ita daga zargin da ake mata, aka ce nan da wani lokaci za a sanar da mu halin da ake ciki.  Tun shekarar 2020 muka aika, amma har yanzu ba wani bayani.  Har ma ta gaji ta buɗe wani shafin; ta mance da wancan.

Waɗannan, a taƙaice, su ne dunƙulallun dalilan dake sa kaji shiru ko a samu jinkiri bayan ka aika kokenka ga hukumar Facebook.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.