Saƙonnin Masu Karatu (2022) (14)

An buga wannan maƙala ne a ranar Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 18 ga watan Nuwamba, 2022.

130

A makon jiya mun karanta dambarwar da ke faruwa a kamfanin Twitter, tun bayan karɓar ragamar shugabancin kamfanin da Mista Elon Musk yayi, a matsayinsa na mamallaki kuma shugaban kamfanin.  A yau ma za mu ci gaba ne da amsa tambayoyin masu karatu kamar yadda muka faro makonni 11 da suka gabata.  Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare damu yadda aka saba.

————————

Salamun alaikum Baban Sadiƙ, don Allah ina tambayar mene ne abin da ake haɗa kwamfutoci 5 ko fiye da haka, idan za a yi Presentation da na’urar Projector ɗaya? Na gode: Aliyu Mu’azu daga Zamfara: 08036578357.

Wa alaikumus salam Malam Aliyu, barka dai.  Da fatan kana lafiya.  Wannan na’ura da kake tambaya akai ita ake kira: “Presentation Adapter”, wacce ke zuwa da nau’ukan mahaɗa daban-daban.  Wasu kuma kan kira ta da suna: “Monitor Switcher”, ko “Presentation Switcher” da dai sauransu.  Abinda wannan na’ura ke yi shi ne bayyana fuskar kwamfutarka a fuskokin kwamfutoci ko na’urorin bayyana bayanai (Display Monitors) daban-daban.

Kamar yadda na faɗa a baya, akwai mahaɗa (Display Ports) daban-daban da take zuwa dashi.  Akwai mai zuwa da mahaɗa 4; wannan ita ake kira: “4-Port Presentation Adapter”.  Akwai mai zuwa da mahaɗa 5, kamar yadda ka bayyana. Bayan nan, akwai wacce ma ake amfani da tsarin sadarwar wayar-iska ta amfani da  fasahar “Bluetooth” ko “Wi-Fi”, wajen bayyana bayanan.  Wannan nau’i ita ake kira: “Wireless-Bluetooth Presentation Adapter”.  Da zarar ka ɗora manhajar na’urar a kan kwamfutarka, sai ka kunna fasahar Bluetooth dake kan kwamfutar, sannan ka kunna na waɗanda ake son su jona da ita.  Cikin sauƙi za su jona suci gaba da bayyana bayanan.

Waɗannan mahaɗai dai sun haɗa da mahaɗar “VGA”, wacce ita ce mahaɗar asali.  Sai mahaɗar “USB Type-A”, da “USB Type-C” wanda galibin kwamfutocin zamani ke zuwa da ita.  Wannan mahaɗa ta ƙarshe dai ita a galibin sababbin wayoyin salula ma, musamman wayoyin kamfanin Apple da Samsung da wasu cikin manyan wayoyin Tecno ko Infinix.  Sai mahaɗa ta ƙarshe, wato mahaɗar “HDMI”.  Wannan mahaɗar sadarwa ita ce mahaɗa mafi inganci wajen sadarwa da nuna hotunan bidiyo raurau.  Akwai ta akan galibin kwamfutocin tafi-da-gidanka (Laptop), sai kuma wasu daga cikin na kan tebur.

Idan ka tashi saya, kayi nazarin kwamfutar da za ka yi amfani da ita akai, ta ɓangaren mahaɗa; kada kaje ka sayi wacce ba ka da mahaɗarta akan kwamfutar da za ka yi amfani da na’urar.  Kamar yadda na faɗa a baya ne, akwai su kala-kala.  Da fatan ka gamsu.  Allah sa a dace, amin.

- Adv -

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya.  A maƙalan da kayi kwanakin baya mai take: “Kimiyya a Ƙasashen Musulmi”, akwai wurin da ka kira wani masanin likitanci dake Cordoba St. Thomas Acquinas, kuma ka kirashi Alzahrawi Abulcasis.  Shi balarabe ne? Daga: Alhaji Calanga, Soro: 07033332143.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Alhaji Calanga Soro, da fatan kana lafiya.  Ina zaton kana ishara ne ga maƙalarmu mai take: Kimiyya da Fasaha a Ƙasashen Musulmi (9), wanda ci gaba daga fassarar maƙalar Farfesa Jim Al-Khalili, ƙwararre a fannin Nazarin Kimiyyar Fiziyar Nukiliya (Theoretical Nuclear Physics) a Jami’ar Surrey dake ƙasar Burtaniya.  Baƙonmu a shafin, wanda shi ne ya fassara maƙalar, sunansa Malam Muddassir S. Abdullahi, kamar yadda bayani ya gabata a makonnin gabatar da maƙalolin.  A taƙaice dai, kamar ka cakuɗa sunayen ne.  Ga asalin sakin layin da sunan marubucin ya bayyana nan:

Cigaba da zurfafa binciken da aka ringa yi a fagen ilimin likitanci (Medicine), da na ilimin sassan jikin ɗan adam (Anatomy) ne silar da har ta kai aka samu littattafan ilimi a ɓangaren likitanci cikin Larabci kamar irin ayyukan su al-Razi (Razes), da na su Ibn Sina (Aviccena) suka maye gurbin ayyukan masana likitanci na dauri na Daular Girkawa kamar su Galen da kuma Hippocrates a faɗin ɗakunan karatu dake a yankin Turai a wancan lokacin. Haka nan, ayyukan da su Ibn Sina da Ibn Rushd (Averroes) suka gudanar a ɓangaren ilimin falsafa ne suka haifar da samuwar manya-manyan masana a yankin Turai a wannan lokacin, kamar su Roger Bacon, da kuma St Thomas Acquinas.  Babban masanin ilimin likitanci kuma likita daga yankin Cordoba ta Andalus da ake kira da al-Zahrawi (Abulcasis) ya ƙirƙiro kayan aikin tiyata (Surgical instruments), sama da guda 200 – da yawa daga cikin su har yanzu ana amfani da su a asibitoci wajen tiyata, kamar su Forceps da Surgical Syringe. 

Shi St. Thomas Acquinas yana cikin malaman dake ƙasar Turai ne. Shi kuma al-Zahrawi (Abulcasis) – kamar yadda ake kiransa a Turai – bayaninsa daban.  In da ka lura, jumla ta ƙare ne bayan ambaton St. Thomas Acquinas.  Jumlar ƙarshe ce ta ambaci sunan al-Zahrawi, wanda shi ne balarabe, ko ince ɗan ƙasar Andalus.  Amma shi St. Thomas Acquinas ɗar ƙasar Turai ne.

Wannan shi ne bayanin, kuma da fatan ka gamsu.  Allah sa mu dace baki ɗaya, amin.

Amincin Allah ya ƙara tabbata a gareka Baban Sadik. Don Allah in da hali, akwai wasu saƙonni da na aiko maka har ka amsa mini su, wajen guda uku ne. A baya na adana su a wata waya amma na neme su na rasa.  Don girman Allah in ba zan takura maka ba, zan so ka sake aiko mini amsar da ka bani.  Domin a duk sadda na karanta su ina matuƙar jin daɗi ne kuma ina ƙaruwa.  Ina ƙara yi maka fatan alheri.  Haƙiƙa ba zan taba mantawa dakai ba a rayuwata ba.   Daga ɗalibinka: Buli Gumel: 08038848964.

Wa alaikumus salam, barka dai.  Da fatan kana lafiya.  Ina matuƙar farin ciki da jin cewa kana samun fa’ida daga ɗan abin da nake rubutawa a wannan shafi mai albarka.  Dangane da buƙatarka kuma, ina ba da haƙuri matuƙa.  Domin na daɗe ina ta neman wannan jawabi da na baka, amma har yanzu ban gani ba, watakila saboda dalilai ne kamar haka.  Na farko, baka rubuto cikakken sunanka ba; na yi amfani da sunan da ka aiko wannan saƙo wajen bincikowa, amma ban samu komai ba.  Na biyu, ban san a wace shekara bace ka rubuto saƙon.  Na uku, da zan iya tuna nau’in tambayoyin da ka mini, watakila hakan zai taimaka wajen zaƙulo su daga shafina dake https://babansadik.com.

Shawarata a nan ita ce, kana iya zuwa Taskar Baban Sadiƙ dake adireshin dake sama, kaje ɓangaren Tambayoyi ko Sakonnin Masu Karatu kayi amfani da sunan da kake tunanin dashi ka aiko mini saƙon a wancan, ta yiwu a dace.  Ina maka fatan alheri.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.