Saƙonnin Masu Karatu (2022) (13)

Tsarin MTN Beep Flash

Bayan waɗannan hanyoyi da za ka iya amfani dasu wajen aika kira don jawo hankalin wanda kake son ya kira ka saboda karancin kuɗi dake layin wayarka, akwai wasu hanyoyin da kamfanonin suka samar a baya, waɗanda suka shafi aika saƙon tes ne mai ɗauke da lambar wayar wanda kake son fadakar dashi don ya kira ka.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 4 ga watan Nuwamba, 2022.

165

Kamar makon jiya, yau ma za mu ci gaba ne da amsa tambayoyin masu karatu.  Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare damu yadda aka saba.

——————-

Salaamun alaikum, barka da warhaka Baban Sadiƙ, yaya aiki?  Ina fatan komai lafiya.  Allah Yasa haka, amin.  Don Allah Baban Sadiƙ, yaya sunan irin noƙaƙƙen kiran nan da ake ce wa “Flashing”?  Wannan ne asalin sunansa?  Sannan, idan ka kira lamba sai kaji an ce: “Please wait, your call is being forwarded”, me hakan yake nufi kenan?  Ka huta lafiya. Ni ne: Baffa Kiyawa, Jigawa State.  07035158365

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Baffa.  Tambayarka kan noƙaƙƙen kira da ake yi, ai tuni ka ba da amsar tambayar; sunan kiran shi ne: “Flashing”.  Kuma yana aukuwa ne ta hanyar danna lambar wanda ake son kira kamar za a kira shi da gaske, da zarar wayar ta fara fitar da amon kira, sai a kashe.  Wannan shi ake kira: “Flashing” a harshen sadarwar wayar salula.  Kuma manufarsa ita ce, kokarin jawo hankalin wanda ake kira don ya kira lambar da aka masa filashin da ita, kai tsaye.  Ƙa’idar kira ta hanyar filashin, kana kiran wanda ka sanshi ne, wanda kuma yake da lambar wayarka.  Domin da zarar ya gani, za iyi tunanin ba ka da kuɗi a layinka ne, nan take sai ya kira ka.  Sharadi na uku shi ne, dole ya zama akwai kuɗi a layinka, illa dai ba zai isheka kira bane.  Misali, idan akwai naira ɗaya a layin wayarka, kana iya yin filashin dashi muddin kiran ba zai wuce gida Najeriya ba.

A ɗaya ɓangaren kuma, kuskure ne ka ma mutum filashin da lambar da bai santa ba.  Domin duk kusancinka dashi, idan bai san lambar ba, ba lalai ya kira ka ba.  Saboda ba kowa ke kiran layin da bai sani ba.  Kamar yadda kuma kuskure ne ka ma mutumin da bai sanka ba, bai kuma san layinka ba, ka masa filashin.  Da kayi wa mutum filashin da layin da bai sanka da ita ba, gwamma ka aika masa saƙon tes don sanar dashi cewa kaine wane kake son magana dashi.  Hakan ya fi sauƙi.  Wannan nau’in filashin ita ce sananniya kuma gamammiya.  Kuma sharuɗɗanta dai, kamar yadda na sanar ne a baya, su ne: na ɗaya, ya zama wanda za ka masa filashin, ya san layin.  Na biyu, ya zama ya sanka.  Na uku, ya zama dole akwai kuɗi a layin, ko da naira ɗaya ne.

Sai dai kuma, bayan wancan nau’in kira na filashin wanda dole sai kana da kuɗi a wayarka kafin ka iya gudanar dashi, a halin yanzu galibin kamfanonin wayar tarho sun samar da wani nau’i wanda za ka iya gudanar dashi ba tare da kuɗi a layin wayarka ba.  Ma’ana, ko babu ko sisi a kan layin wayarka za ka iya gudanar da wannan nau’i na kiran filash.  Kamfanin wayar salula na MTN ne ya fara samar da irin wannan nau’in filash din, wanda yasa masa suna: “Beep Flash” ko “Flash Call”.  Wannan sabuwar fasahar kira dai an samar da ita ne karkashin wani tsari mai suna: “MTN Beep.”

- Adv -

Kana iya aiwatar da wannan kira ko babu kuɗi a kan layin wayarka, kamar yadda na ayyana a baya.  Kawai za ka kira layin da kake so ne, idan babu kuɗi a kan layinka, nan take na’urar aika kira za ta sanar dakai cewa babu kuɗi a kan layinka, amma kana iya latsa *904# don sayan katin waya daga bankinka.  Daga nan kiran zai yanke.  Kana ajiye wayar kawai za a aiko maka saƙo dake sanar dakai cewa kayi nasarar aika kiran filash ga layin da ka kira.  A kowane yini kowane mai layin wayar kamfanin MTN na da damar aika irin wannan saƙo sau 20 a duk yini.  Bayan kamfanin MTN, kamfanin Globmobile ma ya samar da irin wannan sabon tsari na aika kira ba tare da ko sisi a kan layin waya ba.

Bayan waɗannan hanyoyi da za ka iya amfani dasu wajen aika kira don jawo hankalin wanda kake son ya kira ka saboda karancin kuɗi dake layin wayarka, akwai wasu hanyoyin da kamfanonin suka samar a baya, waɗanda suka shafi aika saƙon tes ne mai ɗauke da lambar wayar wanda kake son fadakar dashi don ya kira ka.  Shahararriya cikin waɗannan hanyoyi dai ita ce ta kamfanin MTN mai suna: “Please call me.”  Hanya ce da za ka aika da saƙon buƙatar a jawo maka hankalin wani ta hanyar saƙon tes.  Nan take za a aika masa saƙon cewa kana buƙatar ya kira ka.

Dangane da tambayarka ta biyu kuma, kan ma’anar saƙon da na’urar waya ke jiyar dakai a wasu lokuta idan ka kira wani layi a wani yanayi, wato: “Please wait, your call is being forwarded”, hakan na nufin ɗaya ne cikin dalilai uku.  Dalilin farko dake sa kaji irin wannan saƙo shi ne, idan mai lambar wayar ya sanya layinsa a tsarin “Call Forwarding”, wato tsarin dake isar da kira daga wani layi zuwa wani layi daban.  Misali, idan kana an sanka da wata lamba wacce galibin jama’a kan kira ka akai, sai wani dalili yasa dole ka cire lambar don dora wata lamba, ko kuma inda kake babu yanayin sadarwa mai ƙarfi, kuma ba ka son a kasa samunka, kana iya sanya wannan lamba a tsarin “Call Forwarding”, ta yadda duk wanda ya kira ka a layin, sai yanayin ba kyau, nan take za a cilla shi zuwa ɗayan lambar da goya wancan layin a kai.

Dalili na biyu kua, zai iya yiwuwa wanda ka kira, ko lambar da ka kira na wajen da babu yanayin sadarwa (Sabis) mai ƙarfi ne.  Wannan kansa a sanar dakai cewa ka saurara, za a mika kiranka zuwa wata lamba.  Amma a hakika ba abin da zai faru.  Tunda ba a goya lambar da ka kira akan wani layi ba.  Don haka, sai dai kaji kiran ya yanke kawai.

Dalili na uku kuma na ƙarshe, shi ne, lambar da ka kira na iya zama a kashe take, ba wani sabis bane babu a inda mai lambar yake.

Waɗannan, a takaice, su ne dalilan dake iya sa idan ka kira layin waya, kaji ana sanar dakai cewa: “Please wait, your call is being forwarded”.  Da fatan ka gamsu da ɗan bayanin da na gabatar.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.