Saƙonnin Masu Karatu (2022) (12)

Dalilan Rufe Shafuka a Facebook

Idan tsarin dake girke cikin dandalin Facebook ya lura cewa an harbi shafinka da ƙwayar cuta, to, nan take zai rufe shafin, don kada kaci gaba da yaɗa ire-iren waɗannan cututtuka ga wasu.  Dole ya rufe shafinka, duk da cewa ba laifinka bane. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 28 ga watan Oktoba, 2022.

104

Kamar makon jiya, yau ma za mu ci gaba ne da amsa tambayoyin masu karatu.  Kada a mance dai, muna bayani ne kan dalilan dake sa Facebook ke rufe shafukan mutane.  Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare damu yadda aka saba.

——————-

Yaɗa Ƙwayoyin Cuta Ga Wasu

Yadda muke da ƙwayoyin cuta dake warwatse a mahallinmu, haka ake da ƙwayoyin cuta a warwatse a giza-gizan sadarwa na Intanet.  Sai dai, ta yaya suke samuwa?  Su waɗannan ƙwayoyin cuta dai, waɗanda ake kira: “Virus”, ko “Malwares”, ko “Trojans”, kamar yadda sunayensu ke bambanta ta la’akari da munanan tasirinsu ga kwamfutoci da na’urori da kuma manhajojin sadarwa, rubutattun bayanai ne na umarni ga kwamfuta ko wayar salula, ko manhajar sadarwa, amma masu mau ɗauke da munanan tasiri ga wanda aka aika masa, ko wanda yayi ta’ammali dasu.  Yadda cuta ke wa ɗan adam illa a jikinsa, haka waɗannan na’ukan bayanai ke wa na’urorin sadarwa illa.  To ta wace hanya ake ɗaukansu?

Hanya gamammiya na kamuwa da wannan cuta dai ita ce, ta amfani da ma’adana mai ɗauke dasu a kan kwamfuta ko wayarka ta salula.  Sauran hanyoyin hanyoyin sun shafi kamuwa dasu ta hanyar latsa wani saƙon hoto ko bidiyo da aka nannade su a cikinta/sa.  Ko kuma hawa wani shafi na sadarwa dake ɗauke da bayanai masu ɗauke da ire-iren waɗannan nau’ukan gurbatattun bayanai.  Ta ɓangaren Facebook, za ka iya kamuwa da ƙwayar cuta ne idan kayi amfani da shafinka na Facebook wajen hawa wani shafi gurbatacce a Intanet.  Akwai shafukan yanar sadarwa da manhajoji da yawa da ake iya yin rajista da hawansu ta amfani da kalmomin da kake hawa Facebook dasu.

Hanya ta biyu kuma shahararriya da ake iya kamuwa da cutar kwamfuta daga gareta a Facebook, ita ce hanyar kutse.  Akwai masu yin kutse cikin shafukan mutane a Facebook, amma mafi yawancinsu turawa ne. Masu wannan mummunar ta’ada dai suna Harbin shafukan mutane ne da wasu saƙonni, musamman na hotuna da bayanan batsa.  Kawai sai dai kaji mutane suna ce maka: “Wane anya lafiya kuwa?  Mun ga wasu saƙonni ne munana a shafinka. Mun yi tunanin dai ba kai bane ka wallafa.”  Ko wane zance makamancin haka.  Idan kaji haka, to, alamar an harbi shafinka kenan.  A galibin lokuta kuma, ba sace maka suna kalmar sirrinka suke yi ba, sai dai kawai kayi ta ganin sauyi a shafin, har ka gaji ka bar mu.  A wasu lokuta kuma, suna iya cire maka dukkan abokanka, su cire dukkan hotuna da saƙonnin da ka rubuta, su fitar da kai daga dukkan zaurukan da ka shiga, ko shafukan da kake bibiyansu ta hanyar “Like”.

Mafi munin wannan yanayi shi ne, duk sadda aka harbi shafinka da wannan nau’in ƙwayar kwamfuta, to, duk abokan da kake dasu su ma nan take za a harbe su cikin sauƙi.  Don haka, idan kaga saƙo ko da ba na banza bane, amma mai ɗauke da saƙonnin tallace-tallace, galibi cikin harshen turancin ingilishi ne – ban taba cin karo da na harshen Hausa ba – to, nan take za a cilla wa abokanka irin wannan saƙon, amma ta hanyar Messenger.  Sai dai kawai kaji suna tambayarka meye dalili?

- Adv -

Idan tsarin dake girke cikin dandalin Facebook ya lura cewa an harbi shafinka da ƙwayar cuta, to, nan take zai rufe shafin, don kada kaci gaba da yaɗa ire-iren waɗannan cututtuka ga wasu.  Dole ya rufe shafinka, duk da cewa ba laifinka bane.  Sai dai shafinka zai ta fitar da hotunan batsa, ko yaɗa saƙonni ga jama’an da basu buƙata ba, wanda duk alamu ne da suka cancanci a kulle wa mutum shafi.

Yawan Aika Saƙonni

Wannan nau’in laifi ne dake da harshe biyu.  Wani zai iya cewa, “an ce dalilin samar da Facebook shi ne don hada abota da ƙarfafa zumunci, to, ai aika saƙonni ɗaya ne daga cikin hanyoyin tabbatar da hakan.  Me yasa kuma yawan aika saƙonni zai zama laifi?”   Wannan tambaya ce mai ma’ana kuma wacce ta cancanci ayi ta a nan.  Sai dai, kamar yadda Hausawa kan ce ne, shari’ah sabanin hankali.

Yawan aika saƙonni na zama laifi ne a yanayi biyu.  Na farko, idan saƙo ne iri ɗaya kake ta aika wa mutane. Ba wai ka rubuta saƙo iri ɗaya a shafinka ake nufi ba.  A a.  Ya zama kana ta rubuta saƙon ne karkashin saƙonnin mutane a matsayin tsokaci (Comment).  Idan ka yawaita aika saƙo iri ɗaya a wurare daban-daban, ana ɗaukan wannan a matsayin yunkurin aika wa mutane saƙo ne na bogi (Spam) don manufar tallata wata haja ko dan takara ko neman shaharantar da wani gwarzo.   Amma da sharafin saƙonnin ya zama sun yawaita; daga dubu zuwa abin da yayi sama.  Injin Facebook ne ke iya yanke hukunci kan lokacin da za a rufe shafin naka.  Domin hukumar Facebook ba ta ɗaukan wannan laifi da sauƙi.

Yawan aika saƙo a yanayi na biyu kuma, shi ne, kayi ta aika saƙo dai har wa yau, karkashin saƙon wasu, amma ba iri ɗaya ba.   Misali, a shafinka ne kayi rubutu, sai mutane na ta tsokaci, sai kaima kana ta bibiyar tsokacinsu kana amsa musu ta hanyar Karin bayani ko nuna godiya.  Idan jawabanka sun yawaita fiye da kima (daga dubu zuwa abin da yayi sama), injin Facebook na iya ɗaukan wannan a matsayin laifi.  Sai dai kuma, a wannan yanayin, za a hana ka ci gaba da yin tsokaci ne karkashin saƙonnin wasu ko naka da ka rubuta a shafinka.  Na tabbata da yawa cikin mutane sun fuskanci irin wannan hukunci.

A karon farko za a baka hutun kwanaki ne taƙaitattu.  Idan aka sake ka, kaci gaba baka daina ba. Za a sake kame hannunka na lokacin da ya shige na farko tsayi.  Idan a karo na uku kaci gaba, to, ana iya rufe shafinka kai tsaye.   Ka zama mara jin magana kenan.

A takaice dai, yawan aika saƙonni barkatai, ko iri ɗaya ko nau’uka daban-daban, na cikin dalilan da hukumar Facebook ke la’akari dasu wajen taƙaita maka rubutu ko ma rufe shafin naka.  Kuma da fatan ka gamsu da waɗannan bayanai.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.