Kimiyyar Sararin Samaniya a Sawwake (8)

Ci gaban fassarar littafin Dakta Adnan Abdulhamid mai suna: “Why Astronomy?”

409

Har wa yau Malam Suleiman Khan ya karantar da mu yadda ake tantance adadin tazara ta hanyar amfani da tsarin kusurwori.

Daga baya mun rika amfani da na’urorin gwajin nisa daga kasa masu suna Theodolite da Abney Level a darasin Ilmin Kasa da Dakta Janet Nichol ta dauke mu, don auna tsawon bishiyoyi daga wani sanannen bigire, bayan mun dirke wannan na’ura a gindin bishiyar da muke son gano tsawonta. Wanda ke nazarin tsawon tazarar kan lura da saman bishiyar, sai a tantance kusurwar da ke dauke da tazarar tsawon bishiyar har zuwa samanta.  Samun hakikanin kusurwar da ke dauke da tazarar tsawon bishiyar ya ta’allaka ne da yadda ka dirke wannan na’ura a tushen bishiyar kafin tantancewa.  Adadin tsawon da za a samu ta amfani da wannan na’ura zai zama daidai ne da wanda za a samu idan aka yi amfani da ma’aunin hannu na kai tsaye (Tape) don gwada tsawon bishiyar.

Ta wannan hanya har wa yau na koyi yadda zan rika tantance bambancin tazarar nisa na hotunan da aka dauka daga sararin samaniya ta amfani da jiragen sama masu dauke da na’urar Radar.  Na kuma fahimci haka ne ta hanyar amfani da kusurwa wajen gano tazarar boyayyen bigire, wadda ka’ida ce mai matukar muhimmanci wajen tantance tazara a fannin Ilmin Kasa.  Wasu lokuta nakan tambayi kaina: “Ta yaya zan iya auna tazarar nisan wani tauraro daga inda nake a wannan duniya ta mu?”

Masana fannin Sararin Samaniya kan yi amfani da irin wannan tsari ne wajen gano tsawon abubuwa. Duk da cewa tsarin ya fi haka wahalar fahimta, musamman ganin cewa bambancin tazarar nisan akan kwatanta shi ne da tazarar gudun haske.  Emiliani (1992: 77) ya nuna cewa za a iya auna tazarar nisan wani abu da ke sama; tauraro ne ko wata duniya, ta hanyar auna kusurwar da ke tsakanin bigiren tauraron da ake iya ganinsa, daga wurare biyu mabanbanta a nan kasa.

Tsarin Differential Parallax shi ne bambancin da ke samuwa tsakanin bigirori guda biyu idan mai lura da tauraro ya canza tsayuwansa a yayin da yake auna nisan tazarar wani tauraro (More, 1987).  A fannin Ilmin Sararin Samaniya kuwa, duk wani bambancin tazarar digiri guda idan aka samu, daidai yake da tazarar shekaru 200 na gudun haske.  Shin, zai yiwu a iya gano bambancin tazarar ma’aunin wani abu mai nisa da ke wannan duniya ta mu a aikace kuwa?  Wannan tambaya babu mai ba da amsarta sai masana fannin Sararin Samaniya na hakika. Sai dai kuma abin da yake da muhimmanci mu sani shi ne, ‘yar karamar bambancin tazara wajen nazarin bigiren wani tauraro wani abu ne mai tasiri.  Misali, bambancin tazarar dakika guda kusan daidai yake da tazarar nisan shekaru 3.26 na gudun haske (wato Light Years).  Kalmar “Light Year” na nufin tazarar gudun haske ne na tsawon shekara guda. A duk shekara haske kan yi tafiya ne na nisan tazarar kilomita da ya kai: 299,783 x 60 x 60 x 24 x 365.25km. Ko kuma a sawwake, ya kan yi tafiyar tazarar kilomita 9.48 x 1012 (wato tsawon nisan kilomita tiriliyon tara da biliyon dari hudu da tamanin kenan – 9,480,000,000,000km).

Malam Suleiman Khan bai koyar da mu Ilmin Sararin Samaniya kai tsaye ba, amma daga manyan ressan fannin lissafi da ya karantar da mu, wato reshen Ma’aunin alwatika (Trigonometry), da reshen Aljabra (Algebra), da kuma reshen Ma’aunin kusurwowi da layuka – ko Jometary (Geometry), tare da darussan fannin Ilmin Kasa da muka koya a aikace, na koyi yadda zan iya auna kusurwowi, tare da fahimtar tsarin auna tazarar nisa ta amfani da ma’aunin kusurwowi (wato Triangulations).

Shekaru ashirin da suka gabata, sadda Farfesa Ibrahim H. Umar ke karantar da mu tsarin duniyoyin nan guda tara (Solar System), da tsarin gungun taurari (Galaxy), da gajeru da tagwayen taurari, da tsarin motsawar taurari nesa da wannan duniya ta mu (Redshift), da sauran ka’idojin fannin Sararin Samaniya a Darasin Gama-gari da ya dauke mu a matakin farko na Jami’a, na samu kaina cikin farin ciki da annashuwa lokacin da naji ya ambaci kalmar “Light Years” a karon farko.  Manufarsa  wajen karantar da fannin Ilmin Sararin Samaniya shi ne ya cusa wa dalibansa tarbiyya.  A kullum ya kan nuna wa dalibansa cewa fannin Kimiyya ce hanya mafi girma wajen tasiri, da dan adam ya samar wanda kuma ke tabbatar da samuwar Allah madaukakin sarki.  Har yanzu ina iya tuna ‘yan darussan da ya karantar da mu, duk da karancinsu.

Farfesa Umar bai samu daman ci gaba da karantar da mu ba saboda hidimomi da suka masa yawa, musamman ganin cewa shi ne Shugaban jami’ar a wancan lokaci.  Da a ce ya ci gaba da karantar da mu kam, da mun fa’idantu da karantarwa sosai; domin tsarin karantarwarsa ya sha bamban da na sauran malamai.  A lokacin da yake karantar da mu shi ne kadai Farfesa a fannin Kimiyyar Nukiliya a fadin kasar nan baki daya. Ya kammala digirinsa na uku ne a East Anglia da ke kasar Ingila.  Kuma a lokutan baya ya taba zama shugaban Hukumar Binciken Makamashi na kasa (wato Energy Research of Nigeria).

- Adv -

Duniyar Taurari

Wani abu mai kayatarwa dangane da karantarwar Farfesa Umar shi ne iya karantarwa ta hanya mai sauki, duk da cewa wannan fanni ne mai matukar wahalar sha’ani.  A daya daga cikin darussansa ya karantar da mu tsarin sifofin ayarin taurari (wato Constellation).  Ya ce su taurari suna rayuwa ne a tsarin dangi-dangi.  Misalin da ya bamu kan haka ya dada sawwake mana fahimtarmu kan darasin.  Yake cewa, “Mu dauki birnin Kano baki dayansa misali, mai dauke da mutane daban-daban, da suka fito daga zuri’a daban-daban, da gidaje mabanbanta, da unguwanni, wadanda suka samar da gari mai zaman kansa.”  Sai ya dan dakata, daga nan ya ci gaba, “Wadannan daidaikun mutane su ne misalin daidaikun taurari (wato Individual Stars) da kuke gani a sararin sama.  Daga daidaikun taurari ne ake samun dangin taurari (wato Family of Stars).  Daga dangogin taurari kuma ake samun gungun taurari (wato Galaxy), wanda kuma ke samar da ayarin sifofin gungun taurari a duniya daya.”  Malam ya ci gaba da cewa, akwai ire-iren wadannan gungun taurari sama da biliyan a sararin samaniya, kuma Allah ne kadai ya san iya adadinsu, don shi ne mahaliccinsu.

Su taurari, a cewar Farfesa Umar, suna samuwa ne daga iskar haske mai konewa; gajerun cikinsu su ake kira “wadan taurari,” masu girman cikinsu kuma ana kiransu “manyan taurari.”  Rana tana daga cikin jerin wadan taurari, duk da cewa ta fi wannan duniyar ta mu girma sau 300.  Taurari suna da matukar haske a bisa sura da yanayinsu, ba kamar Wata ba da ke darsano haske daga wani abu daban.  Suna kyalli sosai a yayin da suke konewa.  Malaman Kimiyya sun karkasa taurari ne zuwa gungu-gungu.  Kowane gungun taurari kuma yana da irin nashi sifar da kama.  A takaice dai akwai nau’in gungun taurari guda uku:

Na farko shi ne Gungun Taurari mai sifar kwai, wato Elliptical Shape Galaxies, masu dauke da Gungun Wadan Taurari (Dwarf Stars Elliptical Galaxies) sama da miliyan daya (wato 106), da kuma Gungun Manyan Taurari (Giant Stars Elliptical Galaxies) tiriliyan daya (wato 1012). A cikin wadannan gungun taurari, kowane tauraro yana shawagi ne a tsakiyar da’irar gungun. Kashi sittin cikin dari na taurarin da ke sararin samaniya duk a cikin wannan sifa suke.

Na biyu shi ne Gungun Taurari mai yatsu, wato Spiral Galaxies. Wannan gungu na taurari mai sifar yatsu yana dauke ne da taurarin da adadinsu ya kai biliyan goma zuwa biliyan dari (wato 1010 – 1011).  Nau’in gungun taurari mai wannan sifa su ne kashi talatin cikin dari na taurarin da ake da su a sararin samaniya.

Kashi na uku kuma shi ne Gungun Taurari marasa sifa ta musamman, ko Irregular Galaxies a turance. Su ne nau’in da har yanzu malaman kimiyya basu musu lakabi na musamman ba.  Wadannan gungu su ne marasa sifa ta musamman, kamar irin gungun taurarin da ake musu lakabi da Magellanic Cloud. Kuma saboda tsaban yawansu da cakuduwarsu a wuri guda, ba a iya gane kamannin taurarin da ke cikin wannan gungu. Wasu marubuta kan alakanta samuwar gungun Magellanic Cloud ne zuwa ga matattun taurari wadanda suka kwanta dama. Nau’in gungun taurari marasa sifa ta musamman su ne kashi goma cikin dari na ayarin gungun taurari da ke sararin samaniya.

Cikin bulaguron da yayi a teku daga shekarar 1518 – 1522, Ferdinand Magellan ya gano ire-iren wadannan gungun taurari marasa sifa ta musamman, inda ya tabbatar da cewa sun fi yaduwa ne a bangaren duniya ta Kudu (wato Southern Hemisphere), (James da Martins, 1981: 76).  Wannan tasa ake wa irin wannan gungu na taurari lakabi da Magellanic Cloud.  Har yanzu ana iya ganinsu a sararin samaniya, musamman a cikin duhun dararen bazara.  Wannan gungun taurari da ake kira Magellanic Cloud suna nan kusa damu a iya tazarar nisan kilomita 170,000 na tazarar gudun haske.  Mu ma a nan kasar ta mu ana iya ganin wannan gungun taurari musamman a karkara, lokacin da babu hasken wata.

Shi kuma Virgo wani gungun ayarin taurari ne mai sifar kwai, mai fadin kilomita 25,000 a tazarar gudun haske, kuma ana iya ganinsa ne a tazarar kilomita miliyan 42 a tazarar gudun haske daga wannan duniya tamu.  Wannan ayarin gungun taurari mai suna Virgo shi ne wanda yafi kowanne kusanci da wannan duniya ta mu, idan aka kwantanta nisansa da nisan sauran.  Sauran duniyoyin da ke shawagi a falakin rana kuma an tabbatar da cewa suna cikin gungun taurarin nan masu yatsu ne, kuma ana iya riskarsu a tazarar gudun haske da ya kai nisan kilomita 80,000.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.