Kimiyyar Sararin Samaniya a Sawwake (2)

Ci gaban fassarar littafin Dakta Adnan Abdulhamid mai suna: “Why Astronomy?”

504

Haka kuma, nakan so fita yawo tare da mahaifina, musamman idan zai tafi gona.  Shi kam yana iya jure kowace irin tambaya nayi masa.  Wasu lokuta sai ya kece da dariya idan nayi masa tambayar shirme.  Yakan ba ni amsoshi sabanin irin wadanda gwaggo ke ba ni, idan nayi musu tambaya iri daya.  Sai daga baya na fahimci dalili.  Hakan ya faru ne saboda ilmin addini da yake da shi.  Ya tara nagartaccen ilmin addinin musulunci. Domin ina yawan ganinsa kewaye da mutane masu dauke da littattafai, shi kuma yana zaune a tsakinyarsu, yana karantar da su.  Wannan tasa ni ma na fara sha’awar zama malami.

Na kan lura da tazarar nisa da ke tsakanina da karshen gonarmu, sai in ga kamar kasa ta hade da sama tare da launukan bakan gizo da ke bayyana.  Na yi ta mamakin yadda ake samun duhu cikin dare, tare da haske mai dauke da launuka da dama da ke haskakawa lokacin yini. Sai in yi ta tambayar kaina da ma sauran mutane, “Wai ta yaya haka ke kasancewa ne?

Ilmin Sararin Samaniya a Mahangar Musulmai

Sai daga baya na fahimci cewa ashe taurari halittun Allah ne.  Na gane hakan ne ta hanyar ilimi da kuma tarbiyyar musulunci.  Halittu ne su masu biyayya ga umarnin Allah.  An kuma halicce su ne kamar yadda aka halicci sauran ‘yan Adam. Sai dai duk da haka, babu wani cikin taurari ko wata ko rana, da ke yin tasiri wajen sauya abin da Allah Ya kaddara kan mutane ko sauran dabbobin da ke doron wannan kasa. Yin amfani da halittun da ke sama (rana ko wata ko taurari) wajen fassara abin da ke faruwa ga halittu, shi ake kira Ilmin Taurari (Ashraf, 2001:45).  A na shi bangaren, Haque-Copilah (N.D) ya tabbatar da bambancin da ke tsakanin Ilmin Sararin Samaniya (Astronomy), da kuma Ilmin Taurari (Astrology), inda ya fito da abin fili, yace:

- Adv -

“Tabbatar da bambancin da ke tsakanin ilmin sararin samaniya da ilmin taurari abu ne mai matukar muhimmanci, domin da yawa cikin mutane sun dauka ma’anarsu daya ne. Duk da yake ba nesa suke da juna ba. “Ilmin Sararin Samaniya” nau’i ne na ingantaccen ilmin kimiyya, kuma halal ne a koye shi, shi kuma ilimin taurari jabun ilmin kimiyya ne, kuma haram ne.  Ilmin Sararin samaniya ya kunshi ilmin sammai ne, da kuma fahimtar tsarin da ke tafiyar da dabi’un duniyoyin da ke cikinsu, da gungun taurari da ma duniyar baki daya.  A daya bangaren kuma, Ilmin Taurari na amfani ne da yanayi ko dabi’un halittun da ke sararin samaniya (taurari da wata da sauran duniyoyi) wai don gano tasirinsu a kan kaddarar da Allah Ya tsara wa mutane.  Har yanzu ba a taba samun wani cin karo tsakanin karantarwar Ilmin Sararin samaniya, da karantarwar Kur’ani mai girma ba.”

Duk da yake wasu lokuta faruwar abubuwa kan dace da wani yanayi.  Kamar yadda tarihin musulunci ya karantar da mu, lokacin da Ibrahim, dan Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi) ya rasu, sai kuma hakan ya dace da lokacin da rana ta yi husufi.  Wannan tasa mutane suka ta rade-radin cewa hakan ya faru ne don rasuwarsa.  Nan take Annabi ya kawar da wannan mummunar fahimta, cewa wannan husufi bai da nasaba da rasuwar dansa ko kadan.  Inda ya rika cewa, “Hakika, rana da wata ba su yin husufi don mutuwar wani ko don rayuwarsa.”  Don haka Ilmin Taurari ba ilimin kimiyya bane ko kadan; wani ilimi ne da ya samo asali daga miyagun akidu da al’adu.  Al-Kur’ani mai girma ya sanar damu alakar da ke tsakanin masu Ilmin taurari (bokaye) da kuma shedanun da ke labarta musu dan tsakuren abin da suka fahimta daga wahayin da suke zuwa satan jinsa a cikin sammai.  Inda kuma a karshe ake jefo wadannan shedanu da wasu taurari masu harshen wuta.  Allah Madaukakin sarki ya ce:

“Kuma hakika mun kawata samar duniya da fitillu, kuma muka sanya su abin jifa ga shedanu.  Kuma mun tanada musu azabar Sa’ir…” (Sura 67:5, haka kuma a sura ta 37:6-11, da kuma 15:16-18).

Hanyoyin da suke bi wajen tara bayanansu galibi ba su wuce kintanci-fadi da zaton karya mai dauke da yaudara. Don haka, addinin musulunci ya yi na’am da Ilmin Sararin samaniya, amma bai yarda da Ilmin Taurari ba.  Allah Ya ce:

“Suna tambayarka dangane da jira-jiran wata, kace: ‘lokatai ne domin mutane da kuma haji…” (Sura 2: 189).

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.