Mazan Jiya: Abu Raihaan Al-Biroonee (4)

A yau mun karkare tarihin Abur Raihaan ne. Inda muka kawo bayani kan littattafan da ya rubuta, da maudu’in da suke kunshe dashi, da kuma tasirin hakan wajen habbaka ilimin kimiyya, musamman na sararin samaniya.

1,577

Bayan ya kwashe ‘yan shekaru yana wannan aiki ne ya zarce kasar Indiya daga can, lokacin da Sarki Mahmood ya ci daular Hindu (Indiya) da yaki. Ya kasance tare da shi a can, kuma a wannan lokaci ne ya rubuta shahararren littafin nan nasa mai suna Kitaabu Taareekh al-Hind (Littafin Tarihin Hind).  Duk da cewa wannan littafi ne na tarihi kamar yadda sunansa ke nunawa, amma a cike yake da nau’ukan ilmin kimiyya da fasaha da na sararin samaniya.

Littattafan da Ya Rubuta

Abu Raihaan ya rubuta littattafai masu dimbin yawa. Malaman da suka rubuta tarihinsa sun yi sabani kan yawan wadannan littattafai na shi.  Sai dai adadi mafi karanci da suka bayar shi ne 146.  Daga cikin wannan adadi ko abin da ya wuce haka, kashi 65 duk a kan ilmin kimiyyar duniya ne (Astronomy), da fannin lissafi (Mathematics), da fannin lissafi na musamman kan ilmin kasa (Mathematical Geography), da fannin magunguna (Pharmacology), da fannin likitanci (Medicine) da dai sauransu.  Ya samu daman rubutu a wadannan fannoni ne musamman saboda baiwar da Allah ya masa na son ilmi da kuma sanin harsunan duniyar wancan lokaci da yawa da yayi.  Domin bayan harshen garinsu mai suna korasmiya, ya gwanance a harshen Farisanci (Persian), da larabci, da Sanskrit, da Turkanci, da yaren Girka, da Hibru, da kuma Siriyananci.

Da wannan ya samu daman kalato ilmin kimiyya da ke makare wajen malaman kasar Hindu, da Girka, da sauran al’ummomin da yake iya magana da harshensu.  Bai tsaya wajen kalatowa kadai ba, ya yi geji a tsakaninsu, inda ya watsar da na watsarwa; musamman wadanda suka saba wa ka’idar musulunci.  Misali, ya fafata da Shehin malamin nan mai suna Ibn Sina, kan abin da ya shafi dogaro da kuma yarda da ka’idojin malaman Falsafar daular Girka, wadanda Ibn Sina ke bi sau da kafa.  Ba komai ya kawo haka ba sai don galibin sakamakon bincikensu na kimiyya a cakude yake da akidunsu na maguzanci.

Har zuwa yau duniyar kimiyyar sararin samaniya na tinkaho da Abu Raihaan.  Domin ta dalilin bayanan da ya tara kan yanayin Wata da alakarsa da Rana a lokacin da dayansu yake husufi ne, a yau aka gano tsarin gudanuwar Wata wajen tafiya (wato Moon Acceleration), abin da Dunthorne ya tabbatar a shekarar 1749Bayan haka, har zuwa yau ana amfani da bayanansa kan binciken da ya gudanar dangane da halittun da ke sararin samaniya – Rana, da Wata, da Taurari da yanayin gudanuwarsu.  Har wa yau Abu Raihaan babban malami ne kan abin da ya shafi ilmin zanen taswira, wato Cartography.  Domin yana cikin wadanda ake dogaro da zanensu kan Tsohuwar Taswirar Duniya (wato Old Global Map).

Daga cikin manyan littattafansa akwai babban littafinsa kan tsarin tunani da al’adun mutanen daular Hindu mai suna Tahqeequ Maa Lil Hind Min Muqawwilatin Fil ‘Aqli, Ma’aqoolatan am Marzoolatan, wanda a harshen Turanci ake kira Indica.  Littafi ne da ke bayanin dabi’u da al’adu da kuma addinan mutanen kasar Indiya.  Sai kuma wani littafi mai suna Kitaabut tafheem Li-awaa’il Sinaa’atit tanjeem, wanda a harshen Turanci ake kira The Book of Instruction in the Elements of the Art of Astrology.  Littafi ne da ke bayanin hakikanin ilmin taurari. A cikin littafin ne Abu Raihaan ya bambance tsakanin ilimi kan taurari da rayuwarsu, da yanayinsu, da tasirinsu a sararin samaniya, duk a kimiyyance, da kuma ilimin taurari da bokaye ke amfani da shi wajen ikirarin sanin gaibu, ko wani mummunan lamari da ake tunanin zai faru idan tauraruwa kaza ta bullo a misali.

- Adv -

Nau’in ilimin taurari na farko, a cewarsa, shi ne abin da ya kamata a koya kuma a karantar da al’umma, saboda alakarsa da addini kai tsaye.  Amma nau’in ilimin taurari na biyu, shedanci ne, kuma musulunci bai yarda da shi ba. Domin taurari halittun Allah ne kamar sauran halittu, ba su da wani tasiri na musamman a bisa karankansu dangane da canza rayuwar mutane wajen samu ko rashi, wajen amfani da ko cutarwa.

Littafi na gaba shi ne Al-aathaarul Baaqiyah, anil Quroonil Khaaliyah, littafin da ke bayani kan tarihin al’ummomin da suka gabata, da irin tasirin da suka yi cikin abin da suka bari na kimiyya a duniya.  A cikin littafin yana kokarin gwama tsakanin al’ummomin da suka gabata ne, da irin tasirin da suka yi wajen barin wani abu da ake dogaro da shi na kimiyya.  Kamar irin fasaharsu wajen gano shigan wata, da karewarsa, da amfani da taurari wajen gano bigiren wasu garuwa ko kasashe.  A takaice dai littafi ne na tarihi, wanda ke cakude da ilimin sararin samaniya, da lissafi, da kuma tarihin al’ummomin da suka shige.  Sai kuma littafi mai suna: Qaanoonul Mas’oodi.  Littafi ne na kamus kan abin da ya shafi kalmomi na musamman, da fannoni na musamman, da malamai shahararru kan ilimin Sararin samaniya, da lissafi, da ilimin kasa, da fasahar gine-gine.  Ya sadaukar da littafin ne ga daya daga cikin ‘ya’yan Sarki Mahmood Al-Ghaznawi, mai suna Mas’ood.  Turawa kan kira littafin da suna: The Mas’udi Canon.

Sai littafi na gaba mai suna: At-tafheem Li Sinaa’tit Tanjeem.  Littafi ne mai dauke da tambayoyi da amsa kan ilimin taurari da bambance-bambancen da ke tsakanin nau’ukan ilimin taurari kamar yadda bayani ya gabata a baya, da ilimin lissafi, da ilimin sararin samaniya.  Ya rubuta shi da Larabci, sannan ya juya shi zuwa harshen Farisanci. Sai littafi da ya rubuta kan sinadaran da ke karkashin kasa wadanda Allah ya tanada wa bayinsa mai suna: Al-Jamaahir fee Ma’arifatil Jawaahir.  A harshen Turanci ana kiransa Gems.  Ya sadaukar da wannan littafi ne ga daya daga cikin ‘ya’yan Mas’ud mai suna Mawdood. Sai kuma littattafan da ya rubuta na tarihin garin Khawaarizm, da tarihin Mahmud Al-Ghaznawi da mahaifinsa, da kuma fasahar gano bigire a duniya  mai suna Astrolobe da ya kera, sai littattafan da ya rubuta kan ilimin magunguna da harkar likitanci.

Dukkan wannan kokari da yayi suna nuna tsananin kwazonsa ne wajen tabbatar da ilimi, da son ciyar da al’umma gaba, da kuma karfin imani da sakamakon da Allah ya tanada wa masu ayyuka kyawawa.  Kamar sauran mutane masu numfashi, Abu Raihaan bai dawwama ba a duniya shi ma. A karshe Allah ya karbi rayuwarsa.  Bari in barku da daya daga cikin manyan abokan karatunsa mai suna Abul Hasan ‘Ali bn ‘Eesa, wanda ya zanta da shi cikin numfashinsa na karshe.  Ga abin da yake cewa:

“Na ziyarci Abu Raihaan a lokacin da yake fama da cutar ajali.  Ina shiga inda yake, nan take na gane cewa lallai ya kusa barin wannan duniya.   A cikin wannan hali ne yake sanar da ni cewa, a haduwarmu ta karshe lokacin da muke tattaunawa kan wata mas’ala da ta shafi rabon gado, akwai wani abu da na fada, wanda daga baya ya gane cewa kuskure ne.  Nan take sai na tausaya masa, har na ke ce masa ai yanzu ba lokacin da ya kamata a tattauna batu irin wannan bane; musamman ganin halin da yake ciki na rashin lafiya.  Sai ya ce mini, “Ai ni tuni na san zan bar wannan duniya, amma kuma ba ka ganin ya dace a ce in fahimci wannan mas’alar, da a ce na mutu da jahilcinta?”  Daga nan sai na maimaito masa abin da na fada, sannan ya fara mini bayani dalla-dalla.  Muna gama wannan tattaunawa da shi, sai na tashi na fita.  Fita na ke da wuya, sai na fara jin kururuwa, daga nan na fahimci cewa lallai ya rasu.  Rayuka masu daraja irin wadannan ne ke kasancewa cikin karfi da kuzari har zuwa numfashinsu na karshe.”

Wafati

Abu Raihaan al-Bairooni ya rasu ne ranar 13 ga watan Disamba ta shekarar 1048 miladiyya, daidai da shekara ta 387 kenan bayan Hijira, yana dan shekaru 75.  Allah gafarta masa, ya kuma sanya Aljanna makomarsa da mu baki daya.

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Ummu nana says

    Allan yasaka da alkhairi yakara fahimta yakuma karamana irinku u

  2. MURYAR HAUSA24 ONLINE MEDIA says

    JAZAKALLAHU KHAIRAN!!!

Leave A Reply

Your email address will not be published.