Kasashe Masu Karfin Nukiliya a Duniya (1)

Akwai kasashe da dama da suka mallaki wannan makami na nukiliya. A yau za mu dubi kasashen, da yawan abin da suka mallaka, da kuma siyasar dake cikin dokar mallaka ko hana mallakar wannan makami.

2,250

Kasashe Masu Karfin Nukiliya a Duniya

A yanzu akwai kasashe tara da aka tabbatar suna da wannan makami.  Inda aka bambanta kawai shi ne, yawan makamin da kowace kasa ta mallaka.  Wasu kasashen sun ki bayyana hakikanin abin da suka mallaka.  Wasu ma sun ki yarda a aiwatar da bincike na musamman kan makaminsu.  Wannan tasa sanin hakikanin abin da kowacce daga cikinsu ta mallaka a tantance, ke da wuya matuka.  A halin yanzu za mu yi bayani filla-filla, kan kowacce daga cikinsu, da kuma kiyasin abin da ta mallaka, da lokacin da ta fara mallakarsa, da kuma lokacin da tayi gwaji da dai sauran bayanai masu alaka da hakan.

 

L

Kasa

Adadin Makami Gwajin Farko
1. Amurka 4,075 / 5,535 1945 (“Trinity”)
2. Rasha 5,830 / 16,000 1949 (“RDS-1”)
3. Burtaniya 200 1952 (“Hurricane”)
4. Faransa 350 1960 (“Gerboise Bleue”)
5. Sin 130 / 160 1964 (“596”)
6. Indiya 100 – 140 1974 (“Smiling Buddha”)
7. Pakistan 60 1998 (“Chagai-1”)
8. Koriya ta Arewa 1 – 10 2006 (“The Beginning”)
9. Isra’ila 70 – 200 Babu tabbaci kan gwaji

 

Kasar Amurka

Kamar yadda bayani ya gabata kan tarihi da asalin wannan makami, kasar Amurka ce ta fara kera shi, tare da taimakon wasu kwararru kan harkar kimiyya daga kasashen Ingila da Kanada.  Ta fara aikin ne a shekarar 1937, karkashin wani shiri da ta sanya wa suna ‘The Manhattan Project’, amma bata gama ba sai gab da yakin duniya na biyu.  Daidai lokacin da take tunanin kera wannan makami, akwai rade-radin cewa Hukumar Nazi ta kasar Jamus, na kokarin kera wannan makami, don haka sai tayi gaggawa don tabbatar da cewa ta rigi kasar Jamus din.  In yaso, idan ma yaki ne ya taso, to tana da makamin da Jamus bata dashi, ko kuma a kalla tana da abin kare kanta.  Amma abin bakin ciki, wannan makami bai yi aiki a kan wadanda ake tunani ba, sai a kan ‘yan kasar Jafan, lokacin yaki na biyu.  Amurka tayi gwajin farko ne a shekarar 1945, gwajin da ta sanya wa suna “Trinity”, kuma ita ce kasa daya tilo, wacce ta taba amfani da wannan makami don kai hari ga wata kasa a duniya gaba daya.  Ta kai wannan hari ne da makamin nukiliya nau’in Atomic Bomb, lokacin da ta darkake biranen Hiroshima da Nagasaki.  Ita ce kuma kasa ta farko har wa yau, da ta fara kera makamin nukiliya nau’in Hydrogen Bomb, ta kuma gwada wannan makami da ta sa wa suna “Ivy Mike” ne a shekarar 1952.  A shekarar 1954 kuma ta sake gwajin wani nau’in H-Bomb mai rai, wanda ta ma suna “Castle Bravo”.  A halin yanzu kasar Amurka na da makamin nukiliya da adadinsu ya kai dubu biyar da dari biyar da talatin da biyar (5,535); guda dubu hudu da saba’in da biyar (4,075) masu rai ne, ana iya harba su da zarar bukatar hakan ta kama.

- Adv -

Kasar Rasha

Ita ce kasa ta biyu da ta mallaki wannan makami na nukiliya bayan kasar Amurka, ta kuma mallaki fasahar yin hakan ne ta hanyar tura kwararru kan kimiyyar makamai ta karkashin kasa, don sato ilimin wannan fasaha daga kasar Amurka.  Tayi gwajin farko a shekarar 1947, da wani makami da ta sanya wa suna “RDS-1”.  Babban abin da ya kara wa kasar Rasha kaimin mallakar wannan makami shi ne don taji dadin adawa da kasar Amurka lokacin da suka shiga shekarar yakin cacar-baki.  Akwai tabbacin a kowane lokaci tana iya fuskantar kalubalen yaki daga kasar Amurka.  Bayan haka, ita ce kasar Turai ta farko da ta fara mallaka tare da yin gwajin makamin nukiliya a dukkan ilahirin nahiyar turai. Ta kuma kera makamin nukiliya nau’in H-Bomb ita ma, cikin shekarar 1953, lokacin da tayi gwajin makamin mai suna “Joe-4”.  Ta kuma zarce, don gwada wani makami mai cin miliyoyin zango a shekarar 1955, mai dauke da nau’in H-Bomb, mai suna “RDS-37”.  Har wa yau, kasar Rasha ce ta taba gwada wani makamin bam, wanda babu wanda ya taba gwada irinsa a duniya, mai suna “Tsar Bomber”.  Wannan makami na dauke ne da tan miliyon dari na makamashin nukiliya.  Duk wannan, ita ma, tayi yi su ne a matsayin tauna aya, don tsakuwa taji tsoro.  A halin yanzu kasar Rasha ta mallaki makamin nukiliya wanda adadinsa ya kai dubu goma sha shidda (16,000).  Guda dubu biyar da dari takwas da talatin (5,830) masu rai ne, sauran kuma na kwance.  Wannan ya sanya Rasha a matsayin kasar da ta zarce kowace kasa yawan makamin nukiliya a duniya.

Kasar Ingila

Ita ce kasa ta uku da mallakar wannan makami, kuma hanyar da ta bi wajen mallaka ba wani boyayye bane.  Kasancewarta cikin kasashen da aka yi amfani da kwararrunsu wajen kirkirar wannan makami a Amurka, shi ya bata damar mallaka a shekarar 1952, lokacin da tayi gwajin farko da ta sanya wa suna ‘Hurricane’.  Wannan gwaji, kasar Ingila bata yi shi a kasarta ba, kamar yadda sauran kasashen da suka gabace ta suka yi.  Ta je kasar Austiraliya ne, cikin tsibirin Monte Bello, daidai wani wuri da yanzu ake kira Maralinga Tjarutja, don yin gwajin.  Bayan tayi, an samu ambaliyar tururin haske (Radiation), wanda ya shafi asalin kabilun da ke wannan bigire masu suna Aborigines.  Don haka kasar Austiraliya tace bata yarda ba, sai da aka biya ta diyya kan haka.  Ita ce kasa ta biyu a Turai da ta mallaki makamin, kuma babban abin da ya zaburar da ita shi ne don nuna wa kasar Rasha cewa ita ma tana nan; kasancewarta kawar Amurka.  Kasar Ingila ta kera makamin nukiliyanta nau’in H-Bomb a shekarar 1957, kuma ta mallaki manyan jiragen ruwa masu karfin kai hari da makamin nukiliya a ko ina a duniya (Ballistic Missile), wajen guda hudu.  A halin yanzu adadin makamin ta na nukiliya sun kai dari biyu (200).

Kasar Faransa

Kasa ta hudu da mallakan wannan makami ita ce kasar Faransa, wacce hankalinta ya kasa kwanciya lokacin da ake ta hargowa tsakanin kasar Amurka da Rasha, kan tsibirin Suwiz (Suez Canal) da ke gab da ita.  Don haka ta mallaki nata makamin cikin shekarar 1960, lokacin da tayi gwajinta na farko, kan wani makami mai suna “Gerboise Bleue”.  Ta yi gwajin makamin nukiliyanta nau’in H-Bomb cikin shekarar 1968, karkashin wani shiri da ta kira “Operation Canopus”.  Ita ma, kamar kasar Ingila, ta mallaki manyan jiragen ruwa masu karfin cilla makamin nukiliya daga teku zuwa kowace kasa ne a duniya.  Har wa yau, tana da jiragen sama masu karfin jefowa ko diro da makamin nukiliya a matsakaicin zango (Medium Range Air-to-surface Missiles), masu suna Rafale Fighter-Bombers.  Cikin Janairun shekarar 2006, shugaban kasa Jacques Chirac ya bayyana cewa, kasar Faransa a shirye take da ta kare kanta daga kowane irin hari ne da ya shafi makamin nukiliya a duniya.  A halin yanzu adadin makaminta ya kai dari uku da hamsin (350).

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.