Kamfanin Facebook Da Google Sunyi Yunkurin Fadada Adadin Masu Amfani Da Intanet A Nahiyar Kudu-Maso-Gabashin Asiya

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 23 ga watan Afrailu, 2021.

258

A wani yunkuri na hadin gwiwa, kamfanin Facebook da Google (Alphabet Inc.) dake kasar Amurka sun samar da wani shiri don fadada yawan masu amfani da fasahar Intanet a manyan nahiyoyin duniya guda biyu – kasar Amurka da kuma Kudu-Maso-Gabashin Asiya (South East Asia).  Wannan gagarumin aiki dai ya hada da wasu daga cikin manyan kamfanonin wayar salula dake nahiyoyin guda biyu.  Kamfanonin sun kuduri aniyar yin hakan ne don yalwata mafi yawancin daukacin mazauna wadannan nahiyoyi da fasahar Intanet mai inganci, musamman a kasashe irin su Singafo, da Indonesiya; kasar da tafi kowace kasa yawan musulmi mazauna cikinta.

Wannan katafaren aiki dai zai taimaka wajen fadada kadadar sadarwar fasahar Intanet ne a wadannan manyan kasashe, ta hanyar manyan wayoyin sadarwa nau’in “Fiber Optics” da za a shinfida su ta karkashin tekun Pacific, tun daga gabar nahiyar Amurka zuwa gabar tekun Java dake kasar Indonesiya.  Wannan nau’in wayoyi na zamani dai musamman aka tanadesu don aikawa da siginar sadarwa ta Intanet mai cin dogon zango, kuma tsarinsa na iya jure kowane irin hadari ne dake karkashin teku, ciki har da manya kuma zaratan hakoran kifayen dake karkashin manyan tekunan duniya.  Amma kafin kaddamar da wannan aiki sai kamfanonin sun samu amincewar gwamnatotin kasashen da wannan wayar sadarwa za ta bi ta karkashin tekunansu.

Bayani kan wannan shiri na musamman dai ya biyo bayan hira na musamman ne da kamfanin dillacin labaru na Reuters yayi da Kevin Salvador, mukaddashin shugaban bangaren zuba jari a wajen habaka sadarwa na kamfanin Facebook, inda ya sheda wa Reuters cewa tuni kamfanonin biyu sun amince wajen aiwatar da wannan shiri da ya kunshi shirye-shirye biyu.  Na farko, wanda aka yi wa lakabi da “Echo” da kuma “Bifrost”.

Bangaren farko na aikin zai kunshi shimfida wadannan nau’ukan wayoyin sadarwa na “Fiber Optics” ne a kan wata sabuwar titin karkashin teku da ya keta cikin Pacific zuwa gabar tekun Java na kasar Indonesiya.  Wannan bangaren aikin ana sa ran gama shi  zuwa shekarar 2023.  A daya bangaren kuma, kashi na biyu na aikin, wanda aka yi wa lakabi da “Bifrost”, zai lura ne da inganta siginar sadarwa ta Intanet a daukacin nahiyar da kashi 70 cikin 100.  Shi kuma ana sa ran kammala shi ne a shekarar 2024, ta hadin gwiwa da babban kamfanin wayar salula mai suna XL Axiata.

- Adv -

Kafin wannan sabon yunkuri dai, tun cikin shekarar 2020 kamfanin Google ya rattafa hannun yarjejeniya da gwamnatin kasar Indonesiya don karfafa alaka a fannin sadarwar Intanet, tare da shimfida wayoyin sadarwa da tazararsa ta kai kilomita 3,000, wadanda zasu warwatsu tsakanin manyan birane 20 na kasar.  Sannan da samar da manyan wuraren mu’amala da siginar Intanet na kyauta (Free Public Wi-Fi Hotspots) wanda kowa da kowa na iya amfani dashi.

Al’ummar kasar Indonesiya dai galibinsu na amfani da fasahar Intanet ne ta hanyar tsarin kamfanonin waya, wato: “Mobile Data”.  Wanda hakan ke haifar da tsaiko sosai, saboda karancin ingancin siginar sadarwa na Intanet.  Wannan sabon shiri na kamfanin Facebook da Google da aka kammadar zai baiwa jama’a damar amfani da tsarin Intanet mai inganci, kuma cikin farashi mai rahusa.

Tuni dai manyan kamfanonin sadarwar sadarwa Intanet da wayar salula na duniya, irinsu Google, da Facebook, da Amazon, da Microsoft, da Yahoo da sauran makamantansu ke ta kokarin fadada adadin masu ta’ammali da Intanet a duniya ta hanyar wayar salula da sauran na’urorin sadarwa, a tsakanin kasashe marasa galihu a fannin tattalin.  Ire-iren wadannan kasashe suna nahirar Kudancin Amurka ne, da Asia ta gabas, da Afirka gaba dayanta, da Karibiyan da kuma wani bangare na Gabas-ta-Tsakiya.  Hakan ya faru ne kuwa saboda samuwar adadi mai yawa na jama’a wadanda basu da damar amfani da hanyar sadarwa ta zamani cikin sauki kuma a farashi mai rahusa.  Dalili na biyu kuma shi ne don fadada adadin mutanen da wadannan kamfanoni ke hasashen samunsu a matsayin abokan hulda nan gaba cikin sauki.

Galibin mazauna kasashe talakawa dai suna amfani da Intanet ne ta hanyar wayar salula. Bayan tsadan kudin “data” da farashin kira a duk minti daya, mazauna wadannan kasashe dai na fama da rashin ingancin wadannan hajoji da galibi kamfanonin wayar salule ne ke sayar musu.  Ana sa ran yunkuri makamancin wannan ya samar da Karin ingancin sadarwa da farashi mai rahusa ga mazauna wadannan kasashe.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.