Ka’idojin Sadarwa ta Imel (1)

Tsarin sadarwa na Imel na tattare da wasu ka’idoji ne dake tabbatar dashi. A wannan kasida da wacce ke biye da ita a makon gaba, za mu dubi wadannan ka’idoji ne a kimiyyance, kuma a fasahance. Wannan ke nuna lallai akwai tsari cikin al’amarin sadarwa na zamani.

423

Gabatarwa

A cikin kasidu biyu da suka gabaci wannan mako mun kawo bayanai ne kan tsari da kuma yadda kwamfutoci ke yin mu’alama a tsakaninsu wajen sadarwa, a ko ina suke kuwa.  Na kuma tabbata mai karatu ya karu da wasu abubuwa, duk kuwa da irin tsaurin da kasidun suka yi wajen fahimta.  A yau cikin yardan Allah za mu yi bayani ne kan Manhaja da Ka’idojin Sadarwa ta Imel, wato abin da a turancin kwamfuta ake kira Email Client and Protocols.  A wannan kasida ne mai karatu zai san irin tsarin da kwamfutarsa ke bi wajen budo masa sakonnin sa na Imel da kuma hanyoyin da take bi wajen aikawa ga wadanda yake son aika musu.  Kuma duk da yake wannan makala na da nasaba da guda biyun da suka gabace ta, akwai dan banbanci dangane da abin da ya shafi hanyar aikawa da kuma budo sakonnin Imel.  Hakan ya faru ne saboda wasu daga cikin ka’idojin da ke da hakkin yin wannan aiki ba a game suke da babban manhajar kwamfuta ba, wanda ke dauke da dukkan tsare-tsaren da suke wancan tsari.  Don haka sai a biyo mu don sanin shin me ake nufi da manhajar Imel, kuma ta yaya ya sha banban da ka’idar sadarwa ta Imel?  Duk mai karatu zai sani in Allah Ya yarda.

Manhajar Imel (E-mail Client)

Manhajar Imel, ko E-mail Client ko E-mail Program a Turance, shi ne manhajar aikawa da kuma karban sakonnin Imel a tsakanin uwan garken da ke dauke da jakan wasikar sadarwa da kuma kwamfutar mai budowa ko aikawa.  Wannan manhaja (E-mail Client/Program) na dauke ne da dukkan hanyoyin da zasu sawwake ma mai mu’amala shiga akwatin jakar wasikun sa (Inbox), da yadda zai aika da sakon (Compose) da dai sauran tsare-tsaren da zasu taimaka masa yin hakan.  Yadda ake gina sauran manhaja ko masarrafan kwamfuta, haka shima ake gina shi.  Sai dai ya sha banban da su, domin dukkan manhajar Imel akan gina su tare da dukkan ka’idojin da suke gudanuwa dasu.  Wadannan ka’idoji kuwa kusan su ne tsarin ma gaba daya.  Idan basu a cikin manhajar Imel, to ba yadda za a yi kuwa ka iya budowa balle ma aikawa da sakon Imel daga kan kwamfutar da kake aiki.  Har way au, wannan ke nuna mana cewa shi fa manhajar Imel wani irin tsari ne mai zaman kansa, ba tare da Fasahar Intanet yak e gaba daya.  Domin yadda fasahar Intanet ke tsaye da kafafuwansa, haka ma Imel yake.  Kawai wajen zama ne ya hada su, sai suka zama kamar daya.

Akwai nau’in manhajar Imel iri biyu; nau’in farko shi ne wanda ake iya amfani da shi a Gajeren Zangon Intanet, wato Local Area Network (LAN), da kuma Faffadan Zangon Intanet, wato Wide Area network (WAN).  Akan loda wannan manhaja ne cikin wata uwan garke (Server) na musamman, a kuma tsara yadda duk kwamfutar da ke cikin wannan zango za ta iya isa gareshi, da dai sauransu.  Wannan Uwan Garke ita ake kira Mail Server.  Wannan zai ba dukkan mai son bude adireshin Imel daman yi a wannan  zango, kamar dai yadda muke yi a gidan yanar sadarwa ta Yahoo! ko Hotmail, misali.  Ta wannan hanya za ka iya aika ma duk wanda ke tsakanin wannan zango da sakon Imel, ya karanta, shima ya aiko maka.

- Adv -

Shahararru daga cikin manhajar Imel masu wannan tsari sun hada da Microsoft Outlook 2000, 2003, da Microsoft Outlook Express.  Saura sun hada da Thunderbird na kamfanin Mozilla, da kuma Eudora.  Akwai wasu ma da dama, amma wadannan su suka fi shahara.  Duk da yake za a iya tsara su, har a rinka karban sakonni daga wasu manhajojin na Imel irinsu Yahoo! da Gmail, misali, amma wannan shi ne tsarinsu na asali.  Don haka ake samun su a kusan dukkan manhayan manhajojin kwamfuta irin su Windows Operating System, Mac, Linux da sauransu.  Sai kuma nau’I na biyu, wanda a Turance ake kiransu Web-based Mail Program.  Su wadannan su ne manhajojin Imel da muka saba dasu; wato manhajojin da ke damfare a gidajen yanar sadarwa masu taimakawa wajen aikawa da kuma karban sakonnin Imel a tsarin sadarwa ta Intanet.  Shahararru daga cikin su ba baki bane garemu; sun hada da Yahoomail, Gmail, Hotmail, AOL Mail, Mail, Inbox da dai sauransu.  Ire-iren wadannan manhajojin Imel, duk kana iya aikawa da kuma karban sakonni ta hanyarsu a tsarin Intanet a duniya gaba daya. Su ma, kamar wadanda suka gabace su, suna jibge ne cikin Iyayen Garken gidajen yanar sadarwan da ke dauke da su, wato Mail Servers.  Kuma kana iya tsara su ta inda duk sakonnin da ake aiko maka su rinka zarcewa kai tsaye cikin kwamfutarka, ta hanyar daya daga cikin manhajar Imel nau’I na farko, idan har kana da adireshin su.  Wannan abu ne mai sauki.

A halin yanzu ina da manhajar Thunderbird a kwamfuta ta wanda na tsara kuma nake karban sakonnin Imel da ake aiko mani ta adireshin Imel da nake dasu na Yahoomail da kuma Gmail (in kana so kaje http://www.mozilla.com)Muddin kana da kwamfutar ka na kanka, yin hakan shi yafi, don za ka samu daman tara sakonnin ka waje daya, kuma kana iya adana su cikin kwamfutarka, in yaso zuwa wani lokaci ka sake karantawa.  Wadannan sune nau’ukan manhajojin Imel da ake dasu yanzu.

Uwar Garke (Mail Server)

Ita Uwar Garke, wato Mail Server, kwamfuta ce mai dauke da masarrafan sadarwa da kuma adana bayanai, kuma a cikinta ne ake lodawa da kuma tsara dukkan hanyoyin mu’amala da wadannan manhajoji na Imel.  Galibin lokuta idan tana dauke da wannan manhaja na Imel wanda mutane ke amfani dashi, to ba a cika loda mata wasu nau’ukan bayanai na daban ba. Bayan haka, wannan kwamfuta ce ke dauke da dukkan sakonnin da ake aikawa ko karba ta hanyar adireshin da aka bude a cikinta.  Kodayake idan ka budo akwatin wasikar sadrwanka a kwamfuta za ka same su gaba daya a waje daya, da zarar ka fita (Sign Out), zasu koma cikin wannan uwar garke ne, kai tsaye. A cikinta ne har wa yau, ake da wasu koguna (jam’in kogo) wadanda a Turancin kwamfuta ake kiransu Ports.  Hanyoyi ne da ake amfani da su wajen aikawa da sakonni.  Kowane kogo na da nashi lamba da ake iya sheda shi da shi, da kuma irin aikin da yake yi.  Akwai koguna uku da wannan kwamfuta ke amfani dasu wajen aikawa da kuma karban sakonnin Imel.  Wadannan koguna su ne: Port 25 (wanda ke lura da hanyar aikawa da sakonni zuwa wata kwamfutar, da zarar ka aika, ta hanyar ka’idar da ke wannan kogo); sai Port 110 (wanda ke lura da budo sakonnin Imel da zarar mai shi ya so yin hakan.  Shima akwai ka’idar da ke wannan aiki a wannan kogo); sai kuma Port 220 (ita wannan kogo takan yi aiki biyu ne; aikawa da kuma karba.  Ita ma tana nan da nata ka’idar da ke wannan aiki).  To wasu ka’idoji ne ke wannan aiki?

Zan ci gaba mako mai zuwa.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.