Web 3.0: Fasahar “Blockchain” (2)

A takaice dai, wannan tsari na fasahar “Blockchain”, gamammen tsari ne na taskar bayanan cinikayya da hada-hadar kasuwanci dake warwatse a giza-gizan sadarwa na duniya (Distributed Ledger System – DLS), wanda idan aka shigar da bayanai cikin taskar, ba’a a iya canzawa, sai dai a sake nade wani bayanin sabo, don dorawa daga inda aka tsaya. – Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 20 ga watan Mayu, 2022.

293

Siffofin Fasahar “Blockchain” (2)

Gamammen Tsari

Wannan rumbun adana bayanai bai kebanci wani kamfani ko wata hukuma a wata kasa ba, a a, tsari ne da ya game duniya, karkashin dunkulallen tsarin sadarwa na Intanet.  Yadda kake iya hawa Intanet ba tare da neman iznin wata hukuma ba, a zahiri, haka wannan tsari na fasahar “Blockchain” yake aiki.  Rumbun adana bayanan a warwatse yake a giza-gizan sadarwa ta duniya.  Duk sadda kayi rajista a tsarin, ka shigar da bayanai, akwai tsarin tantancewa da sakonka zai bi, da zarar tsarin ya gama tantance bayananka, nan take za a dunkule shi cikin gungun bayanai (Block), a kuma lika shi a karshen jerin gungun bayanan dake gudanuwa.  Ko da wani yayi nasarar kutse ya sace Kalmar sirrinka, ya budo wannan gungun bayanai (in ma zai iya kenan), ya canza wani abu, da zarar ya rufe shi, nan take tsarin zai sake yunkurin tantance wannan gungun bayanai nashi, idan tsarin ya lura an canza wani abu, sai ya yanke shi daga jerin gungun bayanan rumbun adana bayanan gaba daya.  Tsarin tantancewar zai gane haka ne ta hanyar kwanan watan dake dauke cikin bayanan.

A takaice dai, wannan tsari na fasahar “Blockchain”, gamammen tsari ne na taskar bayanan cinikayya da hada-hadar kasuwanci dake warwatse a giza-gizan sadarwa na duniya (Distributed Ledger System – DLS), wanda idan aka shigar da bayanai cikin taskar, ba’a a iya canzawa, sai dai a sake nade wani bayanin sabo, don dorawa daga inda aka tsaya.  Wannan na cikin siffofin da suka sa wannan tsarin ma’adana ko rumbun adana bayanai yasha bamban da asalin rumbun adana bayanai da aka saba amfani dashi a Intanet ko hanyoyin sadarwa na zamani; a Intanet ne ko a zahirin rayuwa ta hanyar kwamfutocin dake ofisoshi da kamfanin dake duniya.

Aminci da Kariya

- Adv -

Tsarin fasahar “Blockchain” an gina shi ne don tabbatar da cikakken kariya da samar da aminci ga masu ma’amala dashi.  Shi yasa duk inda aka samu wani sauyi a wani gungun bayanai da wani ya dora a baya, to, said ai a yanke wannan bangare, a ci gaba da tafiya.  Wannan ke sa natsuwa da amintuwa da tsarin a zukatan masu ma’amala dashi.

Cin Gashin Kai

Kamar yadda na sanar a makon jiya, wannan fasaha ta “Blockchain” tsari ne da ke cin gashin kansa; ba wata kasa ce ta samar kuma take tafiyar ko gudanar dashi ba.  wannan ya sha bamban da rumbun adana bayanai da kamfanoni ko hukumomin kasashe ko mutane masu zaman kansu ke samarwa.  Karkashin wannan tsari na fasahar “Blockchain”, dukkan bayanan da aka shigar suna dauke ne a mazubi daya, amma duk wanda ke da rajista da rumbun bayanan na iya isa ga bayanansa a ko ina yake.  Sannan ko da wasu ‘yan dandatsa sun yi kutse cikin kwamfutarsa ko na wasu, ba su iya mallakar wadannan bayanai.  Domin idan sun cakuda nasa bayanan ma, sai dai tsarin ya yanke nashi, amma na sauran jama’a na can ana ci gaba da gudanar dasu.

Sabanin tsarin amfani da rumbun adana bayanai na asali (Traditional Database), wanda ke killace a kwamfuta ko kwamfutocin dake karkashin kulawar banki ko wani kamfani ko wani mai zaman kansa, ko kuma hukumar gwamnati.  A duk sadda wani dan dandatsa yayi nasarar isa ga wannan taska na bayanai, yana kwashe su baki daya, ko ya gurbata su, ko kuma, a karon karshe ya goge ma’adanar gaba daya.

A daya bangaren kuma, babu wata hukuma dake da alhakin kayyade ma’amala a tsarin fasahar “Blockchain”.  Abin da hakan ke nufi kuwa shi ne, a tsarin hada-hadar kudi na banki a yanzu, dole kayi rajista da bankin kasuwanci (Commercial Bank), sannan bayananka da zasu karba, suna adana su ne a rumbun adana bayansu wanda su suke lura dashi, ko suka baiwa wani kamfani alhakin lura dashi.  Sannan idan kana son aika wa wani kudi, dole bankinka ne zai jibinci nauyin yin hakan, ta hanyar neman bankin wanda za ka aika masa kudin, ya aika masa a madadinka.  Sannan dole ne bankinka ya zama yana da asusun ajiya da babban bankin Najeriya (CBN), wanda shi ne zai ke kula da tsarin hada-hadar kudin kasar gaba daya.  Wannan matakin alaka tsakaninka da bankinka, da tsakanin bankinka da dayan bankin wanda kake son aika masa kudi, da kuma tsakaninsu da babban bankin kasa, duk yana jawo tsaiko wajen hada-hadar kudade.  Sannan idan aka samu kuskure wajen aikawa, kafin a gyara, yakan dauki lokaci.  Haka idan bankinka ya zalunce ta hanyar kuskure ko da rashin fahimta, dole ka kai kararsa wajen babban bankin kasa.  Nan ma kafin a share maka hawayenka, ka gama jin jiki.

Kalubalen da wadannan abubuwa ke haifarwa suna da yawa, kuma warware su kan dauki lokaci.  Wannan, a takaice, shi ne abin da fasahar “Blockchain” tazo don magance su, a aikace.  Kuma shi yasa, idan wannan tsari ya habaka karkashin marhalar giza-gizan sadarwa ta 3 da muke hange nan gaba, da yawa cikn matsalolin da muke fuskanta wajen hada-hadar alakokin kasuwanci a Intanet, za su ragu ainun.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.