Zuwa Sararin Samaniya: Abu Mai Yiwuwa da Mara Yiwuwa (2)

A wannan makon ma ga mu dauke da karashen jawabin Edward Teller, wanda MALAM SADIK TUKUR GWARZO (sadiqtukurgwarzo@gmail.com) ya hakaito mana. A sha karatu lafiya.

692

Matashiya

A baya na kawo bayanin da shahararren masanin nan Edward Tellar yayi akan tafiya zuwa sararin samaniya cikin shekarar 1961, inda a bayaninsa yake fadar burin da ake son cimmawa idan an fara zuwa sararin samaniya, don haka ga karashen bayaninsa nan:

’’Abin da za mu iya shine mu tura haske wanda zai dauko mana bayanai.  Na san zai yi wahala hasken ya kauce daga inda aka aikeshi matukar an tura shi.  Don haka zai yi ta tafiya har tsawon shekaru, a karshe za mu iya samun kallon Tauraruwa Proxima, sai dai idan aka yi rashin sa’a cewa babu duniyoyin da ake rayuwa a can; shin, zamu tura su gaba ne?  Kun ga wannan zai zama aiki mai wahala kuma mai cin rai.  Alal misali, shin dukkan mutanen dake rayuwa a sauran duniyoyin dake fadin madaukakiyar duniya (Universe), su ma suna bincike ne kamar yadda mukeyi a nan? Kuma shin, a sauran gungun taurarin (Galaxy) dake fadin madaukakiyar duniya da akwai hadari mai kunshe da kura irin na duniyar gungun taurarinmu (Galaxy) wanda yayi mana rumfa daga ganin cikinsa? Kuma shin, akwai kunson taurari a cikin geffan gungun taurarinmu (Galaxy)  inda taurarin ke da kusanci da juna yadda har za’a samu mutanen duniyoyin suna tura sakonni ga junansu da kasuwanci  kuma har za’a iya samun yaki a tsakaninsu (tsakanin duniyar wannan tauraruwa da ta waccan tauraruwa)?

Idan kuwa duk wannan hasashen ya kasance gaskiya, to kuwa zuwanmu can yana da matukar hadari, domin nisan dake tsakanin duniyarmu da taurarin tsakiyar Gungun taurarinmu (Galaxy), nisa ne wanda idan aka tura haske zuwa can duk gudunsa a sararin samaniya sai ya shafe shekaru dubu talatin sannan zai isa.   Sai dai za mu iya zuwa duniyar waje inda za mu samu damar sauraren sigina ta rediyo daga duniyoyin  ta hanyar sauraren (wavelength) nasu, don ta haka za mu iya fahimtar me suke fadawa junansu, daga nan sai mu san makama.

- Adv -

Na san wasu za suyi mamaki sarai daga cikinku akan cewa don me muke ta jajircewa don ganin sai munje tsakiyar gungun taurarinmu (Galaxy), alhali ba ma yin kokarin tafiya zuwa gungun taurari (Galaxy)  mafi kusanci da gungun taurarinmu (Galaxy) mai suna “Andromeda Galaxy”?   Ita kuwa kun sani idan aka tura haske daga wannan duniyar zuwa can sai ya shafe kimanin shekaru miliyan biyu kafin ya isa can, ga shi kuma Einstein yace ba za mu iya tafiya da gudu ba dai-dai ko fiye da gudun haske. Ni da kaina ina son nayi tunanin ta hanyar da za’aje can domin ko shi Einstein ya yi hasashen za’a iya zuwa.  Nasan babu wanda zai iya tafiya da gudu fiye da gudun haske, amma idan har injiniyoyinmu za su ci gaba da yin aiki tukuru har su samar mana da abin hawa na kwarai, lallai za mu iya yin gudu a sararin samaniya da sauri fiye da gudun haske, sai dai na iyakance cewa hakan bazai faru ba ina raye, a hasashena ko da hakan zai faru sai nan da shekaru dari biyar masu zuwa, ina ganin a wannan lokacin duk abin da aka gaza yinsa a wannan duniyar a yanzu, to a wannan lokacin za’a iya aiwatar da shi.   Saboda haka, nan da shekaru dari biyar  masu zuwa (shekara ta 2461), za’a samu wadanda za su iya zuwa Gungun taurarin (Galaxy) “Andromeda”,  ba ma Tauraruwa “Proxima” ba.

Sai dai Wani misalin kuma da nake so a duba; yanzu ace na yi tafiya fiye da gudun haskeN sararin samaniya, me kuke tunani ku masu kallo daga nan duniyar za ku gani?  Za ku rika kallo na ne na nufi “Andromeda” da tsananin gudu wanda yafi gudun haske, yadda zan dauki lokaci dan kankane wajen zuwa.   Shekarun tafiyar haske zuwa can yana daukarsa shekaru miliyan biyu ne da ‘yan kadan, idan za mu yi lissafi, lokaci (T) ya zamo shekaru miliyan biyu kenan.  Sai kuma nisan dake tsakaninmu da “Andromeda” (R) a daya bangaren,  wanda zai zamo nisan tafiyar haske a shekaru miliyan biyu kenan.   Sai kuma nisan da haske zai iya ci a irin wannan lokacin (shekaru miliyan biyu) (ct) wanda shi ma zai zamo nisan haske shekaru miliyan biyu da dori.   Idan aka yi amfani da wadannan abubuwan wajen lissafa bambancin lokacin da za’a ci a sararin samaniya da yadda zai koma a duniyarmu, za’a ga lokacin  ya koma dan kadan.  Ga ka’idar nan a kimiyyance:  (ct)2 – R2 = Q (Q shi ne sabon lokacin da za’a dauka).   Wannan ne abin da ku dake nan duniyar za ku gani.   Amma ni kuma da na tafi fa?

A wuri na da na hau na’urar  Rocket zan zamo kamar wanda ya hau jirgin sama ne daga wata jiha zuwa wata jiha; kamar yadda kuka lissafa kuka ga lokacin ya kankance muku, haka ni ma zan ga lokacin ya kankance.   Hasalima ku lokacin a gurinku shekaru miliyan biyu ne amma ni a gurina da na tafi zai iya zamowa shekaru ashirin.   To shikenan ma, a ce shekaru ashirin zan je “Andromeda,” sai dai idan naje zan iya fuskantar matsaloli da dama; daga ciki su ne: abin da yake a gungun taurarinmu (Galaxy) mai kyaune ne, a wani gungun taurari (Galaxy) fa zai iya kasancewa abu mai matukar hadari.   Domin babu mamaki abincin da na tafi dashi daga nan idan naje can ya zamo guba mai hatsari.

Saboda haka ma ace naje “Andromeda” lafiya, na zauna a can tsawon shekaru goma ina zagayawa ina bincike duk lafiya, sannan na ninko na dawo gida a wasu shekaru ashirin din duk ace na dawo lafiya.   Kunga za ku iya ganin idan na dawo New York gari na, na rabu da ita ne shekaru hamsin a sararin sama, amma shekarun da duniya tayi zai zamo kwatankwacin shekaru miliyan hudu.  Kun ga duniya ta tsufa kenan da yawa; duk abokaina sun mutu, babu wanda zai iya yin Magana da yaren Turanci ne ko Hungarian.   Malaman wannan lokacin za su rika kallona ne da wani irin yanayi; ga shi ba za su iya karanta bayani na ba tunda kun sani da turanci zan rubuta.   Su kuma basu san turancin ba.   Ga shi ko a yanzu ina da shekaru Hamsin, idan na kara wasu Hamsin din a wannan yanayin ya kuke ganin zan koma? Na san daga karshe ma gidan ajiye namun daji (Zoo) za su kaini; na zama abin kallo a gare su!

Edward Tellar ya yi wannan jawabi ne da shekaru takwas, mutum na farko ya dira a duniyar wata. Abu na gaba bai wuce masu karatu su ji halin kimiyya a yanzu ba.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.