Shahararrun Samame Kan Wasu ‘Yan Dandatsa

A yau za mu yi nazari ne kan wasu shahararrun ‘yan dandatsa, wato “Hackers” da hukumomi suka damke su, sanadiyyar ta’addancin da suke aikatawa.

314

Mabudin Kunnunwa

Kamar yadda muka yi alkawari a makon jiya, yau za mu kawo bayanai ne kan wasu shahararrun samamen da aka kai kan wasu ‘Yan Dandatsa a shekaru ko lokutan baya, da irin hukuncin da aka yanke musu.  Wannan ke nuna cewa duk kwarewarka wajen iya shege, wani lokaci na nan zuwa da dabarun ka zasu kare.  Don haka, ba tare da bata lokaci ba, sai mu dukufa:

Shahararrun Samame

Mun ce shahararrun samame ne, don ba za mu iya kawo dukkan wadanda aka kama sanadiyyar wannan sana’a mummuna ba, ko don rashin bayanai kan dukkan su ko kuma don kauce ma tsawaita bayanai.  Don a yau za mu ji bayani ne kan wasu cikin wadanda aka kama, da yadda aka kama su, da kuma irin barnan da suka yi kafin a kai gare su.  A karshe kuma muji me kuliya ya yanke  musu na tara ko zama a gidan kaso.

“Akill”, Hamilton, New Zealand

Cikin watan Nuwanba na shekarar 2007 ne jaridar Guardian Unlimited (http://www.guardianunlimited.co.uk) da ke kasar Ingila ta labarto cewa an gurfanar da wani saurayi dan shekara 18 mai lakabin “Akill” (ba asalin sunan sa ba kenan), wanda kuma ake tuhuma da aikin dandatsa (Hacking) da ya haddasa salwantar kwamfutoci sama da miliyan daya da dubu dari uku, tare da satan bayanan sirri da suka shafi lambobin katin adashin bankin jama’a da wasu bayanai muhimmai.  Wannan  saurayi dai na cikin kungiyar wasu ‘Yan Dandatsa (Hacking Group) ne da ke amfani da manhajar satan bayanai da leken asiri na SpyBot (wanda bayanin sa ya gabata a makon jiya), kuma aika-aikan sa ya haddasa hasaran kudade da aka kiyasta yawan su a dalar Amurka miliyan ashirin ($20m).  A cewan mai gabatar da kara, wannan saurayi “Akill”, wanda dan asalin jihar Hamilton ce da ke kasar New Zealand, tare da wani abokin sa mai suna Ryan Goldstein dan kasar Amurka, sun taba shiga cikin kwamfutar jami’ar Pennsylvania na kasar Amurka, suka aiwatar da barna mai yawa cikin watan Fabrairun 2006. Ana sa ran za a yanke musu hukunci na karshe nan ba da dadewa ba.

Chad Davis, Winsconsin

Shi Chad Davis dan jihar Winsconsin ne da ke kasar Amurka, kuma gwamnatin Amurka na tuhumar sa ne da laifin shiga kwamfutocin Hukumar Tsaro na Amurka wato Pentagon, tare da caccanza bayanan da ke cikin wasu jakunkunan bayanan da ya samu isa gare a lokacin shigan sa, cikin shekarar 1999.  A cewar gidan yanar sadarwa ta CNET (http://www.cnetnews.com), Chad Davis saurayi ne dan shekara 19, kuma shi ne shugaban kungiyar dandatsa mai suna “Global Hell”, kuma idan aka same shi da laifi, hukuncinsa shi ne zaman yari na tsawon shekaru goma. Lakabin Chad Davis na ta’addanci shi ne “MindPhasr”.

David Sternberg, Jerusalem

Jaridar Jerusalem Post ta ruwaito hukuncin da aka yanke ma wani saurayi dan shekara 24 mai suna David Sternberg, mazunin birnin Haifa da ke kasar Isra’ila, cikin watan Afrailun shekarar 2005.  Shi dai David tare da wasu abokan sa su shida, an kama su ne da laifin shiga kwamfutocin babban bankin Post Bank da ke birnin Haifa, tare da aiwatar da satan bayanai, ciki har da shigar da kudade masu dimbin yawa cikin taskan su da ke bankin.  Jaridar tace asali David na zaune ne a kasar Amurka, amma ya gudo sanadiyyar wani ta’addanci da suka aiwatar cikin babban kwamfutar kamfanin E-Bay, daya cikin manyan kantinan saye da sayarwa da ke giza-gizan sadarwa ta duniya.  Bayan dawowan sa kasar Isra’ila, sai ya kai hari cikin reshen bankin da ke Haifa, cikin dare, inda ya fasa wata kofa ya shiga, amma har ya fice ba a kama shi ba.  Da gari ya waye, hukumomin bankin suka aiwatar da bincike, ba a samu wani bayani ba kan wanda yayi, sannan kuma babu abin da aka dauka ko sauya masa zama.  Sai aka rufe kundin bincike. Ashe mugun ya san abin da yayi.  Sai kawai ya kama shago nan kusa da bankin, cikin dan tazarar da bai wuce mita talatin ba (30 meters), ya ajiye ‘yar kwamfutar sa guda daya, da kujera da teburin sa. Wai shi ma wani ma’aikacin kan sa ne.

Bayan wasu ‘yan kwanaki, sai aka lura, daga hedikwatan bankin, cewa ana shigar da wasu kudade daga reshen bankin, ta amfani da tsarin shigar da kudade ta kwamfuta (Electronic Fund Transfer), wanda hakan ba ya cikin ka’idar bankin.  Daga nan aka fara bincike, sai masana kan harkan kwamfuta da tsaron lafiyan bayanai suka gano wata na’ura ‘yar karama da aka ajiye ta cikin wata ‘yar karamar akwatin sadarwa (Communication Box), wacce ke zuko bayanai daga gajeren zangon kwamfutar da ke cikin bankin, zuwa wajen bankin, mai cin gajeren zango. Ko da aka bi wannan na’ura, sai aka samu ta tike ne a shagon wannan saurayi.  Ashe daga nan ya hada sadarwa tsakanin na’urar da ya shuka cikin bankin, da kuma kwamfutar sa. Dukkan kwamfutocin bankin, da kuma bayanan da ke cikin su, yana iya shiga ciki, yayi duk abin da ya ga dama.  Kuma daman shi da wasu abokanan sa sun bude taskar ajiya (account) a bankin, sai kawai ya rika shigar musu da kudade, kai tsaye.  Bayan samun sa da laifi, alkali ya yanke masa hukuncin zaman wakafi na watanni goma sha shida, tare da kwace wasu daga cikin kudaden da aka samu a hannunsa.

Gary McKinnon, London

- Adv -

Cikin shekarar 2002 ne kasar Amurka tai hasarar bayanan da bata taba yin irinsa ba, wanda har daga karshe take cewa ‘yan Al-Qa’ida ne suka ruso cikin rumbum kwamfutocin ta suka aiwatar da abin da take kira ta’addanci, don abin ya wuce iya tunanin ta.  Ko da Hukumar Binciken Laifukan cikin Gida, wato FBI ta tsananta bincike, sai aka gano ashe wani dan kasar Ingila ne mai suna Gary McKinnon, mai shekaru 39, ya aikata wannan aiki.  McKinnon dai dan kasar Ingila ne, kuma kwararre ne kan kimiyya da injiniyancin kwamfuta (Computer Engineer), wanda aka fi sani a duniyar dandatsanci da lakabin “Solo”, yana kuma aiwatar da aikace-aikacen sa ne daga kwamfutar sa, cikin dakin sa da ke Unguwar Green Wood a birnin Landan.  Kasar Amurka na tuhumar sa ne da laifuka wajen guda takwas, kuma tana bukatar a mika mata shi don ta yanke masa hukunci a kasar ta. Amma lauyansa yace haka bazai yiwu ba.  Idan har aka samu kai shi kasar Amurka, McKinnon zai fuskanci hukunci a jihohi dai-dai har takwas.  Don shi ne ya samu shiga kwamfutocin Hukumar Tsaro ta kasar Amurka wato Pentagon, da kuma kwamfutocin Hukumar Soji na kasar, wajen casa’in da biyu. Ana kuma tuhumar sa da lalata wasu kwamfutocin har wa yau na wasu kamfanonin Amurka guda shida. McKinnon dai na fuskantar barazanar dauri a gidan kaso na tsawon shekaru saba’in, tare da tara na zunzurun kudi da suka kai fam na Ingila dubu dari tara da hamshin (£950,000.00).  Baya ga nan, kasar Amurka tace zai biya wasu fam dari biyar da saba’in (£570,000.00) da ta kashe wajen neman sa.  Lallai aiki ya samu lauyan McKinnon.

Andrew Harvey da Jordan Bradley, County Durham

Wadannan samari biyu dai yan kasar Ingila ne, mazauna garin County Durham, kuma ana tuhumar su ne da kirkiran wani manhaja na satan bayanai da leken asiri mai suna TK Worm, wanda suka gina ta amfani da burbushin GTBot da bayanan sa suka gabata a makon shekaranjiya.  Andrew dan shekara 24 ne, shi kuma Jordan dan shekara 22; yara ne masu matukar hazaka wajen gina manhajar kwamfuta (Programming), kuma sun amsa laifin su a gaban kuliya, cewa lallai su suka kirkiri wannan manhaja da ya haddasa salwantar kudi wajen fam na Ingila miliyan biyar da digo biyar (£5.5m).  Wannan mummunan manhaja na su na TK Worm dai na amfani ne da wani rauni ko kafa da ke cikin masarrafan lilo da tsallake-tsallake (Web Browser) na kamfanin Microsoft, wato Internet Explorer, kuma ya haddasa ma kwamfutoci wajen dubu goma sha takwas zazzabi mai tsanani tare da hasaran kudade da lokacin aiki.  Kafin su shiga hannu, Andrew Harvey da Jordan Bradley na cikin shahararriyar kungiyar nan ta ‘yan dandatsa ta duniya mai suna “THr34tKrew”.

Farid Essebar, Morocco

Shi Farid dan kasar Maroko ne, kuma an kama shi ne cikin shekarar 2006, lokacin da ya kirkiri wani manhajar kwayar cutar kwamfuta (Virus Program) mai suna Zotob, wanda kuma ya yada shi cikin kasashen duniya, ya haddasa matsalaloli da dama ga kwamfutocin mutane, musamman kwamfutocin Babban Bankin Duniya (World Bank) da wasu shahararrun kamfanonin yada labarai na duniya.  A yanzu kasar Amurka ta mika wannan saurayi mai shekaru 18, ga hukumar kasar Maroko inda yake jiran a yanke masa hukunci.

Axel Gembe, Germany

Na san masu karatu basu mance manhajar satan bayanai da leken asiri mai suna AgoBot ba, wanda bayaninsa ya gabata makonni biyu da suka shude. To Malam Axel Gembe, shi ne makirkirin wannan manhaja na ta’addanci.  Axel, wanda duk bai wuce shekaru 21 ba a duniya, an kama shi ne cikin shekarar 2004, da laifin kirkiran wannan manhaja na AgoBot, mai bangarorin ta’addanci wajen uku.  Tare da wasu abokan sa su biyar, an kuma yanke musu hukunci ne cikin shekarar 2004, a kasar Jamus.

Christopher Maxwell, California

An kama Christopher Maxwell ne cikin watan Janairun 2005 a jihar Kalfoniya da ke kasar Amurka.  Kamar Gary McKinnon, laifin Maxwell ya shallake kasar Amurka har zuwa kasar Jamus.  Maxwell, dan shekara 20, mai lakabin “donttrip”, ya aika manhajojin ta’addancin sa ne “yawo” don neman kwamfutar da zasu kai mata hari, sai azal ta afka dashi suka far ma kwamfutocin wata asibiti da ke Jihar Seattle na kasar Amurka.  Wadannan kwamfutoci da jami’an Maxwell suka darkake lokaci guda, su ne masu tafiyar da galibin harkokin asibin gaba daya. Don haka, suna harbuwa, sai duk kofofin asibitin suka kasa buduwa ko rufewa.  Hatta na’urorin Pager da ma’aikatan asibitin ke amfani dasu suka dauke, suka daina aiki.  Ba nan kadai abin ya tsaya ba, marasa lafiya da ke cikin halin kaka-nika-yi (Intensive Care Section), sun shiga halin la haula, domin kwamfutocin da ke taimaka musu numfashi ko kuma sawwake musu halin da suke ciki, duk sun daina aiki.

Maxwell dai yayi amfani ne da jami’ai (bots) wajen miliyan daya, wadanda kuma suka darkake wadannan kwamfutoci.  Har wa yau, ana tuhumar sa da laifin kwantar da wasu kwamfutoci guda dari hudu dake Hukumar Tsaro na kasar Jamus, duk a lokaci guda.  A halin yanzu Maxwell zai biya tara na zunzurutun kudi na dalan Amurka dubu dari biyu da hamsin da biyu ($252,000.00), ga hukumar wannan asibiti, sannan yaje gidan yari na tsawon watanni talatin da bakwai.

Kammalawa

Wannan shi ne kadan cikin labaran wadanda aka samu kai samame akan su, har aka gurfanar da su a gaban alkali don yanke musu hukunci. A ci gaba da kasancewa tare da mu. Ina mika sakon gaisuwata ga dukkan masu karatu, musamman masu bugo waya  ko aiko da sakon tes ko na Imel.  Allah Ya kara zumunci, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.