Sakonnin Masu Karatu (2016) (10)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

115

Assalamu alaikum, barka dai.  A gaskiya na ji dadin albishir da kayi mana na gina mana shafin da za mu rika lekawa domin mu karu.  Sai ban sani ba, za a ajiye mana bayanan a yanayin “pdf” ne ko wani yanayin daban?  Allah taimaka.  Daga: Haiman Khan Ra’ees, Kaduna: 08185819176

Wa alaikumus salam, barka da warhaka Malam Haiman.  Kasidun zasu kasance ne a shafuka, ba wai a yanayin jakunkunan bayanai ba (Files).  Illa dai, akwai dogayen kasidu masu shafuka daga 10 zuwa 100, wadannan za su kasance ne a yanayin “pdf”, duk mai bukata sai ya saukar dasu.  Kasidu irin wadannan za su kasance ne a bangaren “Dunkulallun Kasidu.”  Ko kuma “Kasidu Na Musamman.”  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya.  Tambayata ita ce: yaya ake saukar da bidiyo ta shafin “Youtube”?  daga: Muhammad Chiroma, Birnin Malam-madori. – 08024381651

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Muhammad.  Baka yi bayanin a kan waya ce ko a kwamfuta ba.  Idan a kan waya ce kuma nau’in Android, kana iya zuwa “Play Store” wato cibiyar manhajoji, sai ka nemi manhajar dake wannan aiki, ka rubuta: “Youtube Video Donwloader,” nan take za a nemo maka manhajar, sai ka saukar da ita kaci gaba da amfani da ita.  Idan kuma a kwamfuta ne, sai ka nemi manhajar lilo (Browser) na kamfanin Mozilla mai suna: FireFox.  Idan ka saukar ka loda wa kwamfutarka, sai ka shiga Google ka nemi irin wancan manhaja, wato: “Youtube Video Downloader” amma a gaba ka kara: “extension”, za a nemo maka kai tsaye, sai ka saukar.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu Alaikum. Mallam inaso ai mini bayani akan tsarin gina shafukan yanar sadarwa nau’in “HTML,” ina son sanin bayan na tsara ko na rubuta shafukan, na yi gwaji na ga ya yi yadda nake so, to, yaya zanyi na dora shi a intanet har in bashi adireshi (URL)?  Na gode: Aliyu Adamu Kondis, dalibi a Jigawa State Polytechnic, Dutse: aliyu0025@gmail.com

Wa alaikumus salam, Malam Aliyu barka ka dai.  Da farko dai ina neman afwa sanadiyyar lokaci mai tsawo da na dauka ba tare da na amsa maka tambayarka ba.  Abu na biyu, da zarar ka gama gina shafukan gidan yanar sadarwarka (Web Pages), sai ka yi rajistar adireshin gidana yanar sadarwar, tare da kamfanin da zai adana maka gidana yanar sadarwar, ta yadda a duk sadda aka tashi shiga za a samu ba tare da yankewa ba.  Samun rajistar adireshi ba shi da wahala, muddin kana da taskar banki (Bank Account) tare da katin ATM.  Kana iya yin rajistar adireshin gidana yanar tare da hidimar adana maka shafukan.  Wannan shi ake kira: “Web Hosting.”  Duk za ka iya samun wadannan hidindimu daga shafin: “Go Daddy” (www.godaddy.com), ko kamfanin “HostGator” (www.hostgator.com).  Bayan wadannan akwai kamfanoni da yawa masu tallata wannan hidima cikin farashi mai rahusa.

- Adv -

Shi adireshin gidan yanar sadarwa ana masa rajista ne na tsawon shekara guda.  Idan shekara ta zagayo sai ka sake biyan kudin hidimar rajista.  A nasa bangare, hidimar adana maka shafukan yanar kuma, wato: “Web Hosting,” a duk wata ake biyan kudin hidimarsa, amma za ka iya biyan na shekara daya ko sama da haka ma.  Idan kayi kokarin yin hakan, za su maka rahusa matuka.  Idan kuma adireshi da ma’adanar kyauta kake bukata duk akwai.  Kana iya amfani da dandanlin “Wordpress,” wanda ke bayar da damar samun adireshin shafi na kyauta (mai dauke da tallace-tallace), da kuma hidimar adana shafuka (Web Hosting) shi ma kyauta.  Sai dai, kamar yadda ka sani ne, araha ba ta ado.  A yayin da suke baka wannan dama don amfana da dandalinsu wajen yada shafuka da ra’ayoyinka, su kuma za su rika sanya tallace-tallace a shafinka lokaci zuwa lokaci, don su ma su amfana da kai.

A matsayinka na dalilin fannin ilimin kwamfuta, ina kyautata zaton yin hakan bazai zama maka da wahala ba.  Ina maka fatan alheri, Allah taimaka ya kuma sa albarka cikin karatunka, amin.  Da fatan ka gamsu.


Asslamu alaikum, yallabai da fatan kana lafia.  Ina binka a jarida duk mako.  Ina so ka sakani a groups naka.  Ga adireshin Imel di na: iiajingi@gmail.com Waya: 07034395506. Na gode. Imran Ibrahim Ubale

Wa alaikumus salam, bark aka dai Malam Imran.  Muna farin cikin jin kana tare damu a duk mako, kuma da fatan za ka ci gaba da kasancewa tare damu a kullum.  Dangane da “Group”, ban tanadi wani mahalli na musamman don yin hakan ba, idan ka kebe shafin Facebook da na mallaka.  Da yawa cikin masu karatu ‘yan uwanka sun tuntube ni kan wannan lamari, musamman ta bangaren manhajar “Whatsapp,” amma nace babu.  Dalilin rashin samuwa kuwa shi ne don yanayin lokacina bazai ba ni damar tafiyar da zauren yadda ya kamata ba.  Wani bawan Allah ya bukaci in bashi dama ya bude da sunan wannan shafi, sai dai kuma, tunda ba shi da ahalin abin (na yaba sha’awarsa kan yin hakan), sai ya zama a kullum zauren babu wani motsi.  A karshe ma ya zama sai dai a ta aiko wasu sakonni da ba su da alaka da wannan fanni.

Irin haka ne na guje masa.  Domin duk wanda nace ga zaure na bude a “Whatsapp” ko a dandalin Facebook ko wani dandali, zai yi tsammanin ganina da jin motsina a zauren a kullum; safiya da maraice, dare da rana.  Idan ya shigo yaji shiru, ko ya ga sakonnin da ake aikowa ma ba su da alaka da abin da ko sunan zauren, ka ga bai amfana da komai ba kenan ta wannan bangare.  Don haka ayi hakuri.  A halin yanzu ina kan gina gidan yanar sadarwa ne don adana dukkan kasidun wannan shafi.  Idan na gama kuma na gayatta shafin, daga nan zan tanadi mahalli na musamman don haka in sha Allah.  Da fatan ka gamsu.


Amincin allah ya tabbata gareka. Hakika muna matukar amfana da wannan shafi mai albarka na fasaha da kere-kere.  Allahu ya kara basira.  Don allah Baban Sadik ina so ka turo min DUKKAN Kasidunka game da dabarun samun ingantattun bayanai a Internet.  Daga na farko har zuwa karshe.  Na gode. Daga Ja’afar Ahmad Saleh: kingjafar6@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Ja’afar.  Idan na fahimci bukatarka, kana ishara ne ga kasidun da na rubuta don karantar da hanyoyin neman bayanai da dabarun yin hakan, cikin sauki.  Sai dai, sabanin yadda kake zato (kamar yadda kayi amfani da kalmar “daga farko zuwa karshe”) kasidun guda uku ne kacal.  Allahumma sai in kana nufin dukkan kasidun da na taba rubutawa ne a wannan shafi, hakan kuwa zai yi wahala ta Imel dinka lokaci guda.  Sai dai kayi hakuri idan shafinmu ya gyattu sai ka shiga ka saukar kai tsaye.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.