Facebook Gidan Rudu: Mata-Maza ‘Yan Damfara (1)

Na fara rubuta wadannan makaloli ne a shafina na Facebook, a shekarar 2015.

273

Mata-Maza ‘Yan Damfara (1)

Daga cikin manyan rudu dake makare a dandalin sada zumunta na zamanin yau akwai rashin hakikanin manufofin wadanda muke tare dasu a matsayin abokanai.  Tabbas, idan abokananka galibi wadanda ka sani ne a zahiri, wannan matsalarka ragaggiya ce.  Amma idan kashi 70 cikin 100 na abokananka a nan ka hadu dasu, to, dole ne kayi taka-tsantsan.

A nan ba cewa nake ka rika tuhumar duk wadanda baka sansu a zahirin rayuwa ba, ko kuma munana musu zato, a a.  Amma dai ka tsaya a iya haddin alakar da kake tunanin shi ne asalin mahadinku.  Wannan ba wai ga abokananka maza kadai ba, hatta mata – duk daya ne, wai makaho ya yi dare a kasuwa.  Yadda ake samun mazambata cikin maza haka ake samun mazambata cikin mata, sosai ma kuwa.  Wasu kuma mata-maza ne, ma’ana mata ne amma a siffar maza, ko maza ne amma a siffar mata; kuma ‘yan damfara.

Akwai wadanda ke bude shafi da sunan mata, kuma mata ne, amma manufarsu kawai ita ce nemo wa wasu mazajen wadanda za su yi maashaa’a dasu.  Wadannan kawalai mata kenan.  Akwai kuma kawalai maza, da sunan maza sosai.  Sannan akwai wadanda maza ne su, amma sai su bude shafi da sunan mace, su rika tallar kansu a matsayin wani namijin ne daban, ga mata.  Idan mace ta nuna tana so, sai su bata lambar wayarsu.  Da zarar ta kira sai ya dauka, daman an gaya mata cewa namiji ne, ba matsala kenan.  Galibi wadannan sun fi yawa a zaurukan Facebook, saboda nan ne aka fi haduwa kuma kana iya ganin “Profile” din mutum warewake, inji Zage-zagi.

- Adv -

Akwai wanda ya bude shafi da sunan mace, yana hira da mata.  Kashi 90 cikin 100 na abokanansa mata ne.  Hira yake dasu, a matsayin mace ce shi.  Yace musu sha’awa na damunsa amma ya samu wani gaye dake debe masa kewa wajen “sex chat” (hirar batsa don kawar da sha’awa), idan suna so zai iya hada su dashi.  Da zarar sun amince sai ya tura musu lambar wayarsa, daman yana da lambobi kusan 5 daban-daban, kuma yana da wani shafi daban mai sunan namiji.  Haka ya rika yi wa ‘yan mata da yawa da na sani, har a karshe Allah ya kawo karshen wannan shashanci nasa.  Akwai kuma wanda ya bude shafi da sunan mace, yana neman abokai mata zalla.  Da zarar an karbi abotarsa, sai ya turo sako tun fari, yace:

“Hajiya ki gafarceni, ni namiji ne, wanda ke debe wa manyan mata sha’awa da zawarawa, ta hanyar sex chat in suna so.  Idan kina so to, amma in baki so, don Allah kiyi blocking dina kawai.  Ba zagi.  Na gode.”

Wata ‘yar uwa ta nuna mini irin wannan sako, da na bibiyi wannan tantiri, sai naga namijin ne kamar yadda ya fada.  Da yawa cikin mata sun rudu dashi, yana ta shashanci dasu.  Kuma bayan wannan shafi ma, yana da wani shafi da wata lambar wayar daban.  Allah kiyashe mu shashanci irin wannan.  Wannan bangaren masu boye fuskokinsu kenan da niyyar maashaa’a.

BABAN SADIK

22.03.2016 – 5:15pm

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.