Ciyar da Najeriya Gaba a Fannin Kimiyya da Kere-Kere (4)

Wannan shi ne kashi na hudu a jerin kasidunmu kan hanyoyin ci gaba a fannin kimiyya da kere-kere a Najeriya, kuma mun dubi dalilan da suka sa muka ci gaba ne, a mahangar tarihi. A sha karatu lafiya.

419

Tarihin Ci Gabanmu a Fannin Kere-kere

Hakika a bayyane yake cewa kowace al’umma na da hanyoyin da take bi wajen ciyar da kanta gaba a fannin kere-kere.  Hakan kuma na samuwa ne ta hanyar fasaha da hazakar da Allah Ya hore wa dan adam.  Kafin zuwan turawan mulkin mallaka kasar nan, al’ummar wannan kasa na amfani ne da hanyoyi daban-daban da suka kirkira a fannin kere-kere.  Muna kera kujerun da muke zama a kai daga bishiyoyin da Allah ya hore mana a dazuzzukanmu.  Muna kera akushi, da masakai, da takalma, da zobba, da injinan saka, da na barza hatsi, da dai sauransu.  Sannan muna da makera inda muke sana’anta abubuwan da muke bukata wajen noma da kiwo da zamantakewa.  Makeran namu ma kala biyu ne; akwai “Farar Makera”, inda ake “Farar Kira”.  A wannan makera ne ake kera tukwanen dalma, da farantan azurfa da zinare, da zabba, da dai sauran kayayyakin alatu da kyale-kyale.

A daya bangaren kuma, akwai “Bakar Makera”, inda ake “Bakar Kira” don samar da ruwan garma, da fartanya, da sakatono, da magirbi, da sauran makamantansu. Dukkan wadannan abubuwa muna kera su ne ta amfani da fasaharmu da kuma itatuwa ko bishiyoyi ko duwatsun da Allah ya samar mana a muhallin da muke rayuwa.  Wannan hanya ta ci gaban kere-kere, wacce turawa daga baya suke kira “Local Crafts”, ita ce hanyar da ta rike mu tun kaka da kakanni, kafin zuwan turawa.  Kuma a haka muka ta rayuwa, cikin kwanciyar hankali da lumana, da kuma wadatuwar zuci.

Da Turawan mulkin mallaka suka shigo kasashenmu, sai suka zo da wasu sababbin kayayyakin kere-kere da aka kero daga kasashensu, kuma cikin karfi da yaji suka yi iya yinsu wajen ganin sun dakushe ci gaban hanyoyin da muke bi a baya don kera kayayyakin da suka same mu da su kafin zuwansu.  Misali, a Arewacin kasar nan, Bature ya same mu da makera mai cike da tsari, da masaka mai cike da hikima da fasaha; ga kuma mutane masu hazaka da ke aiki a cikinsu.  Kasancewar dukkan kasashe masu mulkin mallaka suna yin haka ne don amfanin kansu da kasashen da suke wakilta, nan take suka fara kokarin ganin sun kashe wadanann wuraren kere-kere da ke kasashenmu ta hanyoyi daban-daban, kamar yadda mai karatu zai karanta nan ba da dadewa ba.

Bayan sun karbi madafun iko a hannunsu, sai suka fara bullo da dokoki, suka sauya akalar ci gaban tattalin arziki, suka zo da sababbin tsare-tsaren shugabanci a kokarinsu na ganin sun tabbatar da rikonsu a kanmu.  Daga nan suka gina tituna, da dogayen hanyar jirgin kasa don hade manyan biranen kasar da bakin bodar kasar.  Sun yi hakan ne kuwa don amfanin kansu, kuma saboda samun saukin kwashe kayayyakin masarufi ta manyan jiragen ruwan da suka jibge a bakin gabar tekun Atilantika.  A haka suka ci gaba da mulkin mallaka, suna dada fadada kasar, suna dada shuka tasirinsu, suna kuma dada debe abin da suke bukata na amfanin kasarmu don kaiwa kasashensu.  Galibin wadannan ayyuka sun yi su ne da kudaden da kasar ta samar daga albarkatun noma – irinsu gyada da auduga da koko da katakai da sauransu.  Bayan sun bamu ‘yancin kanmu (a siyasance), sai muka gano man fetur, daga nan sai kamfanonin hakon mai suka shigo, nan take sai kudaden shiga ya karu; musamman cikin shekarar 1973, sa’adda rikici yayi tsamari a tsakanin Falasdinawa da Kasar Isra’ila.  Cikin wannan shekara kasar nan ta samu kudade masu dimbin yawa daga cinikin danyen mai, saboda kasashen Larabawa sun sanya takunkumin sayar da mai ga kasashen Yamma, don haka suka koma sayen danyen mai daga Najeriya da sauran kasashen da ke Kudancin Amurka.

Da galibin kudaden da aka samu a wannan shekara ne aka gina tsofaffin Jami’o’in da ke kasar nan, da manyan gadojin da ke birnin Legas, da Kwalejin Fasaha da wasu daga cikin Cibiyoyin Binciken Kimiyya da dai sauransu.  Sauran kudaden kuma aka yi gagarumin bikin al’adun nan mai taken Festac ’77, lokacin mulkin shugaba Obasanjo karo na farko.  Daga wannan lokaci ne shugabannin Najeriya suka fara rasa alkibla a fannin ci gaban kasar nan, har a karshe muka samu kanmu cikin wannan halin da muke ciki.  A halin yanzu ga wasu daga cikin dalilan da suka jefa kasarmu cikin ci baya ko ince rashin ci gaba a wannan fanni:

Mummunan Tasirin Mulkin Mallaka

Kamar yadda kowa ya sani daga baya, duk kasashen da suka shahara wajen mulkin mallaka a duniya sun yi hakan ne don amfanin kansu.  Domin bayan kokarin da suka yi wajen kwashe kayayyakin masarufin da suka yi, sun kuma taimaka wa kamfanonin da ke kasashensu wajen tallata hajojin da suke kerawa.  Hakan kuma bai yiwu musu ta dadi ba, sai da suka kirkiri dokokin da suka dakushe hanyoyin kere-keren da ke kasashen da suke mallaka.  Hukumar Burtaniya ta taimaka wajen shigowa da bindigogi, da kayayyakin alatun daki, da kekunan hawa, da takalma, kai hatta ababen shaye-shaye na barasa ta taimaka wajen shigowa da su.

A wasu bangarorin Najeriya – musamman kudanci – hukumar mulkin mallaka ta haramta sayarwa ko shan giyar “gwaggwaro” wacce ake tsimawa a kauyuka.  Ba don komai ta yi haka ba sai don taimaka wa kasuwar barasar turai ta samu fadada.  Wannan tsari na dakushe kokarin ‘yan kasa da kashe wa hajarsu kasuwa don ciyar da kasuwar hajojin kasashen turai gaba, ta yi mummunar tasiri wajen dakushe ci gaban kimiyya da kere-kere a kasar nan. A cikin littafinsa mai suna How Europe Underdeveloped Africa, Professor Walter Rodney, wani shahararren malamin tarihi da siyasar tattalin arzikin kasa na kasar Gayana, ya yi bayani filla-filla kan yadda turawan mulkin mallaka suka tsiyata al’ummar da suka mulkesu.  Duk mai bukatar Karin bayani, to ya nemi wannan littafi.

Rarraunan Tsarin Karantarwa

A tabbace yake cewa hanya mafi tasiri wajen samar da ingantaccen ilmin kimiyya da kere-kere na zamani, ita ce ta hanyar ilmin zamani.  Sanin haka, tare da fahimtar hazakar da Allah ya yi wa mutumin Najeriya, ta hana turawa samar da ingantacciyar tsarin ilmin zamani a kasar nan.  Domin sun san cewa muddin muka cafki wannan ilmi ta hanyar da ta dace, to ikonsu ya kare a kanmu.  Duk wanda yayi la’akari da manhajar karatun da muka gada daga turawan mulkin mallaka zai fahimci haka cikin sauki.  Bayan kashe tsarin karatun ajami da suka yi a shekarar 1913, sun tabbatar da cewa babu wani dan kasa da darajar karatunsa ta wuce sakandare ko elamentare.  Amfanin hakan ma, kamar yadda shugabannin mulkin mallakar suka tabbatar da bakinsu, shi ne don samar da kananan ma’aikata masu musu hidima a ofisoshi, da kotuna, da kuma wadanda za su rika yi musu tafinta.  Ga abin da Lord Lugard yake cewa cikin shekarar 1921:

“Babban manufar gwamnatin (mulkin mallaka) wajen kafa makarantun firamare da sakandare a tsakanin ‘yan kasa shi ne don ilmantar da yara masu hazaka daga cikinsu don su zama malamai a wadannan makarantu, ko akawu a kananan kotuna da kuma samar da masu tafinta a tsakaninsu.”  (Lord Lugard 1921). 

- Adv -

A nashi bangaren kuma, Rev. J. C. Taylor, daya daga cikin manyan shugabannin addini karkashin gwamnatin mulkin mallaka, ya kara da cewa sun karantar da yara a wadannan makarantu ne don taimaka musu wajen kira zuwa ga addini.  Don haka suka dage wajen karantar da su “A B C D.”  Ya fadi hakan ne a shekarar 1857.  Wannan tasa a duk tsawon zaman gwamnatin mulkin mallaka a Najeriya, in ban da Kwalejin Fasaha ta Yaba da ke Legas da aka gina don samar da kwararru “masu matsakaicin ilmi” kan fasahar kere-kere, duk sauran makarantun sakandare ne da firamare da aka kirkiro don samar da ma’aikatan ofis da masu tafinta ko kananan ma’aikatan kotu.  Ko kadan gwamnatin mulkin mallaka bata damu da inganta tsarin ilmi ba balle har a samu wasu kwararru da za su motsa ci gaban kimiyya da kere-kere a kasar nan.

Tsarin Habbaka Kamfanonin Kere-kere

Bayan samun ‘yancin siyasa gwamnatin Najeriya ta yi kokarin ciyar da kasar gaba a fannin kere-kere ta hanyar samar da kamfanonin kere-kere (na motoci, da mashina, da sauran kayayyakin aikace-aikace) a gida, tare da shigowa da kayan aikin don kera abubuwan da ake bukata ba tare da dogaro kan wasu kasashe ba.  Wannan tsari na ci gaban tattalin arziki mai suna Import Substitution Industrialization Policy, ya fara aiki, inda har gwamnati ta kafa masana’antun kere-kere na motoci da bangarorinsu – kamar Fiat, da Leyland da Stear – da kuma kamfanonin sarrafa karafa – irin su Kamfanin Sarrafa Karafa na Delta, da Kamfanin Sarrafa Karafa na Ajaokuta – da aka samar don kera bangarorin mota (Automobile Spare Parts).  Karkashin wannan tsari har wa yau, gwamnati ta tanadi masana’antar kera manyan bangarorin injina da mashinan masana’antu.

To amma saboda rashin damuwa da ci gaban kasar, haka gwamnati ta bar wadannan kamfanoni ko masana’antu da ta fara kafawa don wannan gagarumin aiki mai muhimmanci, galala, har abin ya daidaice.  Domin daga baya an daina shigowa da kayayyakin da wadannan masana’antu ke bukata don ci gaba da aiki, kuma a haka suka durkushe, aka sallami ma’aikatan da ke ciki; tsarin ya mutu.  A daya bangaren, kasashe irinsu Brazil da Malesiya sun ci gaba nesa ba kusa ba a wannan fanni, alhali kuma cikin lokaci daya muka faro da su.

Rashin Dabbaka Sakamakon Binciken Ilmi

Duk da tabarbarewan ilmi a kasar nan, akwai cibiyoyin bincike masu kokarin kirkiro hanyoyin samar da sababbin kayayyakin kere-kere a kasar nan.  To amma saboda shi bincike wani abu ne da ake fara shi a takarda, amma a kare shi da aiki, babu abin da ya damu hukuma da ire-iren sakamakon binciken ilmi da ke fitowa daga wadannan manyan cibiyoyin binciken kimiyya. A wasu kasashe, da ire-iren wadannan sakamakon bincike ake takama, su ake dabbakawa a aikace, har a karshe a samar da sababbin hanyoyin ciyar da rayuwa gaba.  Bayan wadannan cibiyoyin bincike har wa yau, akwai sakamakon binciken ilmin kere-kere da ke fitowa daga manyan malamai masu hazaka a jami’o’inmu da kuma kwalejin fasaha da kere-kere, su ma ko kadan hukuma bata damu da su balle ta yi wani abu a kai.  Ni kaina sheda na kan haka.  Lokacin da nake sakandare, akwai malamin fannin Fiziya da ya kera jirgin saman mai saukar ungulu, wato Helicopter babba.  Duk sa’adda muka shiga dakin bincikensa don daukan darasi, wannan abu da ya kera ya kan bamu sha’awa tare da kayatar da mu sosai.  Sau tari mukan yi kwadayin ina ma ace gwamnati ko wani kamfanin kera jiragen sama ya dauke shi aiki, don karasa kera wannan jirgi.  To amma kaico!  Haka wannan hikima tasa ta kare tsakanin aji da dakin bincikensa, har ya bar makarantar.

Rashin Damuwa a Bangaren Gwamnati

Dabi’un gwamnatin tarayya da na jihohi wajen rashin damuwa da habbaka fannin kimiyya da kere-kere a Najeriya ya dada taimakawa wajen durkeshewar wannan fanni.  Ba abin mamaki bane a yanzu ka samu kowace irin mota ce a kasar nan.  Duk irin wanda kake so akwai, an shigo da ita.  A wasu lokuta ma, mako biyu ko uku da kera wata sabuwar mota, ka sa idonka a kan titunan kasar nan, za ka ganta tana tafiya.  Wasu masu alfarmar ma aka ce kamfanin kera motocin suke zuwa don zaban irin wacce suke so a kera musu.

Amma har yanzu babu wanda ya damu – daga gwamnatin tarayya har zuwa jihohi – don ganin an farfado da tsarin samar da kamfanoni da masana’antun kere-kere a kasar nan.  An wayi gari galibin tsare-tsaren gwamnati wadanda suka shafi fannin kimiyya da kere-kere, da ka ake shirya su, ba tare da shawartar kwararru a wannan fanni ba.  A inda aka shawarce su wajen shirya tsare-tsaren kuwa, za ka samu ba a nemansu idan aka tashi aiwatar da shirin.  Wannan ke sa ka ga an kashe kudade makudai a fannin, amma sai ka nemi aikin da aka yi ka rasa.  Siyasanci, da tumasanci, da ‘yangaranci, da cin hanci, da rashawa sun bata tsare-tsarenmu baki daya.  Wannan ba zai haifar mana da mai ido ba ko kadan.

Kangon Makarantu

A kasa irin Najeriya ne kadai za ka samu jami’o’i a kowace jiha, da kwalejin fasaha bila-adadin, amma ka nemi tasirin ilmin ka rasa.  Hakan ya samo asali ne daga irin tsarin da ake tafiyar da karatun.  Domin kowace jami’a tana bukatar tallafin kudi da zai tamaka mata wajen aiwatar da bincike mai inganci, ya samar da yanayin karatu mai kyau, ya kuma taimaka wajen tabbatar da kimar ilmi.  Idan ka dubi kasarmu za ka ga kusan dukkan wadannan abubuwa guda uku babu su.  Bayan haka, galibin makarantunmu suna fama da matsalar wutar lantarki, da hanyoyi marasa inganci, da rashin kayayyakin aiki masu taimakawa wajen samar da ilmi mai inganci; duk babu wadannan abubuwa.  In kuwa haka ne, mai karatu ya gaya min yadda za a samu dalibai masu inganci da za su yi wani abin kirki!  Wani malamin jami’a a kudancin kasar nan ya taba cewa, ba abin mamaki bane ka samu dalibi mai karatun fannin fasahar kere-kere (Mechanical Engineering) a jami’armu ya kasa bambance maka tsakanin sandar noti, wato bolt, da kuma noti, wato nut. 

A duniya karankaf, kasar Indiya ce ta uku a fannin ci gaban kere-kere da kimiyyar lantarki, inda take biye da kasar Amurka da Rasha.  A kididdigar shekarar 2003, kasar Indiya ta mallaki kwararru kan harkar kimiyyar kere-kere da lantarki sama da miliyan hudu.  A shekarar 1985 kadai ta yi rajistan Injiniyoyi 750,000.  Tana da manyan cibiyoyin koyar da ilmin kimiyya da fasahar kere-kere guda biyar da take kira India Institutes of Technology, wadanda take basu tallafi mai tsoka, don karantar da ingantaccen ilmi ga ‘yan kasarta da masu shigowa daga wasu kasashe.  Kasar Indiya na fitar da galibin hajojinta ne zuwa kasar Amurka da sauran kasashen Turai.  A shekarar 2008 kasar Indiya ta samu dalar Amurka dala na gugar dala har sama da biliyan goma sha daya wajen sayar da manhajojin kwamfuta da ‘yan asalin kasarta suka gina kadai.  Duk wannan bai samu ba sai don sadaukar da kanta da tayi wajen ganin ta inganta ilmin kimiyya da kere-kere. Wannan ne kuma yasa jami’o’in kasarta da na kasashe irinsu Malesiya da Singafo ke samun dalibai daga dukkan sasannin duniya, ciki har da ‘yan Najeriya!

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. abubakar muhammad aljigwalee says

    Allah ya taimaka Yakuma buda kwakwalan masu shirin far fado da nijeriya daga dogon sumanda tayi zuwa ga hanyar kimiyya da fasaha,

Leave A Reply

Your email address will not be published.