Bitar Maƙalolin Da Suka Gabata a Shekarar 2022 (1)

Bayan shekaru 16 da fara rubutu a wannan shafi mai take: “Kimiyya da Ƙere-Ƙere” na jaridar AMINIYA mai albarka, mun gabatar da maƙaloli guda 730; an samu ƙarin 52 kenan daga adadin 680 da na sanar a shekarar da ta gabata. – Jaridar AMINIYA, ranar Jumma’a, 6 ga watan Janairu, 2023.

124

Bayan Makonni 52!

Ga al’ada, bayan tsawon lokaci da muka ɗauka muna kwararo darussa a wannan shafi mai albarka, mukan yi zama na musamman a ƙarshen shekara ko farkon sabuwar shekara, don yin waiwaye, abin da Malam Bahaushe kan kira “Adon tafiya.”  Haka abin yake tun faro wannan shafi mai albarka a shekarar 2006.  Zama na ƙarshe da muka yi shi ne wanda ya gudana a shekarar 2022; tsakanin 14 da 21 ga watan Janairu.

A halin yanzu, bayan shekaru 16 da fara rubutu a wannan shafi mai take: “Kimiyya da Ƙere-Ƙere” na jaridar AMINIYA mai albarka, mun gabatar da maƙaloli guda 730; an samu ƙarin 52 kenan daga adadin 680 da na sanar a shekarar da ta gabata.  Kuma kamar yadda na sanar a wancan karo, muna taskance waɗannan maƙaloli ne a shafin TASKAR BABAN SADIƘ dake: https://babansadik.com, kuma suna tsare a fanni-fanni.

Akwai fannin Kimiyya, wanda ya ƙunshi kimiyyar ƙere-ƙere, da kimiyyar makamashi, da kimiyyar sararin samaniya, da kimiyyar sinadarai, da kimiyyar ɗabi’u da halayya, da kimiyyar lantarki, da kimiyyar Ƙur’ani, da kuma kimiyyar teku.  Sannan akwai kuma ɓangaren Fasaha, wanda ya ƙunshi fasahar sadarwa, da fasahar Intanet, da fasahar wayar salula, da fasahar kariyar bayanai, da fasahar AI, da fasahar gina manhaja, da fasahar kwamfuta, da dai sauransu.  Sai kuma ɓangaren da suka shafi tambayoyin masu karatu.  Cikin maƙaloli 730 da na ayyana a sama, maƙaloli 215 duk amsar tambayoyin masu karatu ne.

A yau za mu yi bitar maƙalolin da muka amfana dasu ne daga farko zuwa ƙarshen shekarar 2022 da ta gabata.  Wannan shi ne bita na 10!

Saƙonnin Masu Karatu

- Adv -

Kamar yadda aka saba, masu karatu kan rubuto saƙonnin tambaya ko neman maƙalolin da suka gabata, ko neman ƙarin bayani, ko sharhi kan abin da suka karanta, ko kuma, a wasu lokuta, su min gyara kan kura-kuran da na tafka a ɗaya daga cikin abin da na gabatar na rubutu.  A shekarar da ta gabata masu karatu sun aiko saƙonni da dama.  Na kuma buga sakonnin masu karatu, ɗauke da sharhin amsoshin tambayoyinsu, a tsawon makonni 15.

Saƙonnin sun shafi kusan dukkan ɓangarorin da nake rubutu akai ne galibi.  Duk saƙon da ba shi da alaƙa da fanninmu, nakan shawarci mai saƙon da ya aika zuwa ɓangaren da zai iya samun jawabi mai gamsarwa.  Ba dukkan saƙonnin nake bugawa a jarida ba.  Wasu kan ce in aika musu jawabi ne kai tsaye ta hanyar Imel.  Wasu kuma su nemi in basu damar kira don neman ƙarin bayani.  Nakan yi hakan iya gwargwadon lokaci da damar da nake dashi.  Na amsa tambayoyin ne tare da sharhi ga masu buƙatar neman ƙarin bayani kan wani abu da na rubuta a baya.  Daga kashi na ɗaya zuwa na uku an buga su ne a watan Afrailu.  Kashi na huɗu zuwa na 15 ɗin kuma an buga su ne tsakanin watan Satumba zuwa Nuwamba.  Wato tsawon watanni uku kenan muka ɗauka wajen amsa tambayoyin kashi na ƙarshe.

Waɗannan saƙonni dai, kamar yadda na sha faɗa a baya, kan ƙara mini ƙwarin gwiwa, da ƙaruwar ilmi da fahimta, da kuma wayewa kan tsarin ma’amala da jama’a, da kuma koyon sababbin hanyoyin karantarwa.

Nazari Kan Abubuwan Ci Gaba a Shekarar 2021

Mun shigo shekarar 2022 ne da ƙarashen fassarar wata doguwar maƙala mai amfani kan ci gaban kimiyya a ƙasashen musulmi, wanda ɗan uwa Malam Mudassir Abdullahi ya faro mana a ƙarshen shekarar 2021.  Mun buga kashi na 9, kuma na ƙarshe a ranar jumma’a, 7 ga watan Janairu, 2021.  Wato maƙalar ta ɗaukemu tsawon makonni 9 kenan ana bugawa.  Daga nan muka yi Waiwaye Adon Tafiya kashi na 9, wanda ya ɗauke mu tsawon makonni biyu.

Bayan haka ne sai muka sake komawa ɗakin bincike, inda muka yi wani nazari mai cike da fa’ida.  Taken maƙalar shi ne: “Mahimman Fasahohin da Suka Sauya Duniya Cikin Shekaru 175” ta biyu baya.  Wannan maƙala dai, wanda sharhi ne kan nau’ukan hanyoyi da na’urorin kimiyya da fasahar sadarwa da suka yi tasiri wajen sauya rayuwar duniya da manhangarta, ta zo ne cikin makonni biyu ita ma.  Muna gamawa ne muka shiga sharhi kan ci gaban da aka samu a shekarar 2021, cikin maƙala mai take: “Mahimman Abubuwan Ci Gaba a Fannin Kimiyya da Fasahar Sadarwa a Shekarar 2021”.   A wannan karo, ta la’akari da fa’idar dake tattare da wannan sharhi, mun ɗauki makonni uku ne muna nazari.  Wannan ya kai mu har zuwa ƙarshen watan Fabrairu, inda muka dakata don amsa tambaoyi da sharhin masu karatu.  Hakan shi ma ya ɗauke mu tsawon makonni uku.

Daga nan ne muka sake garzayawa zuwa ɗakin bincike don ci gaba da nazarin wasu fannoni na ilmin kimiyya da fasahar sadarwa da ƙere-ƙere, kamar yadda bayani zai zo a makon dake tafe.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.